°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*11*
_Malam Ahmad Ibrahim haifafen d'an garin kano ne nan ya taso cikin gata da kulawa a gun iyayensa nan yayi karatunsa na makarantar ga ba primary yana kammalawa ya taho garin bauchi karatunsa na N C E, bayan yayi N C E sa a haka har Allah ya tai maka ya samu aiki koyarwa a makarantar primary duk da yana aiki a jihar bauchi bai hana sa ziyar iyaye da 'yan uwansa a garin Kano ba. A haka wani zuwansa ya had'u da Fatima nan ya bita har gidan su sai da ya ni mi izin tsayuwa da ita a gun iyayenta kafin ya fara hira da ita. A haka har ya sake dawowa Kano nan fa maganan aure ya kan-kama iyayenta suka bashi wata biyu cikin ikon Allah ya soma had'a kaya kafin wata biyu duk wani abunda ya dace yayi anyi shi aka kai kayan aure a haka akayi biki aka kawo Amarya Bauchi, Fatima ta kasance mace mai hak'uri da rik'e sirrin mijinta sannan mace da duk a kowani hali mijinta yake bata gudanshi._
_Fatima ta iya kula da miji a duk lokacin da taga Ahmad d'inta yana cikin damuwa to tabbas bata da sukuni sai har taga ya dawo dai-dai yanda yake kulum, inko zai fita aiki sai ta raka shi har k'ofar gida ta yi masa addu'a tare da fatan nasara hakan yana k'ara ma Ahmad jin k'aunar Fatima shima yana iya k'ok'arinsa gurin faranta mata rai duk da aikin sa bawani kud'i yake samu ba sai dai rufin asirin Ubangiji. Duk randa basu da abinci Fatima zatayi hak'uri da abunda ya kawo musu ta dafa takuma gode ma Allah sam bata faye yawan k'awaye ba don gudun gulma da gutsiri-tsoma kulum tana gida tana bitar karatunta ko tana sak'a huluna da safan yara da rigunan sanyi na sayarwa. A haka suka kwashi shekara uku duk bayan shekara suna zuwa Sallah gida sannan su dawo gaskiya duk wanda yaga rayuwan Ahmad da matansa abun kwatance ne kuma duk wata mace mai hankali da hikima zata so ta koyi hali irin na Fatima don ita ba macece mai hayani ba ko Malam ne ya b'ata mata rai sam bata bari ya gane fishin ta ko kad'an har wani lokacin da kansa yake ce mata"Fatima nikam sam bana son irin b'oye fishinki don k'ar ina b'ata miki rai kina shiru duk da nasan rayuwa ta gaji haka duk mutumin da zaku zauna dole sai kun b'ata amma ba ma fatan b'atawan kuma hakan yana sa ina k'ara k'aunarki don kin zamo min kifi d'aya acikin rafi kin zamo madubin dubawa ta a duk lokacin dana kalleki ina me k'ara gode ma Allah da ya azurta ni da ke a matsayin mata._
MASUYI MIN COMMENTS, TEXT MESSAGE, TARE DA KIRAN WAYA AKAN WANNAN LABARI DUK NAGANI KUMA NAJI NAGODE ALLAH YA BAR ZUMUNCI ALLAH YASA MASU HALI IRIN NAN CIKIN LABARIN YASA ABUNDA ZASU KARANTA YAZAMA DARASI A GARESU WA'YANDA BASAYI KUMA ALLAH YA K'ARA KARE MU NAGODE DA COMMENTS 'DINKU KUMA HAKAN YANA K'ARA BANI KWARIN GWIWA ALLAH YA BAR K'AUNA AMEEN. TANKS YOU ONCE AGAIN YOU GUYS.
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment