�?�?�? *RUWA CIKIN COKALI*�?�?�
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*�Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*7*
_Bayan sun idar da Sallah abinci suka ci its da Umma suna gamawa suka wanke hannu littafan Tauhidi Hadisi da Fiqihu da Al-qur'ani suka d'auka nan Umma ta saka glashinta, Kdeey ne ta bita mata karatun da ta mata jiya sannan ta soma d'aura mata sabon k'arin karatun, bayan sun idar da littafan ne kowanne ya d'auki Al-qur'ani yana karantawa cikin murya mai dad'i sauraro tare da sanya wa mutum nutsuwa da imani a cikin zuciyarsa._
_Malam kuma yana waje yana k'arin karatu ma Dattawa a waje da Matasa da Yara sai k'arfe tara ya sallamesu ya shigo gida, sai da ya ci abinci kafin yazo ya zauna a tsakanin matansa da d'iyarsa nan kuma suka fara karatun Sira wanda Malam shike musu yana basu tarihin Manzon Allah da irin gwa-gwarmayan da yayi da kafirai (Allahu Akbar mazan fama kenan Allah ya k'ara ma Annabi daraja Ameen). Sai da suka idan kafin sukayi addu'a tashi daga majalisi wanda kulum sai sunyi shi gashi kamar haka(Subhanakallaumma wa bi handika ash hadu alla ila ha illa anta astagafirka wa atubu ilaika, yan uwa yana da kyau duk lokacin da muka zauna a wani majalisi ko gunda aka taru akayi magana duk lokacin da mukazo tashi yana da kyau mu karanta wannan addu'a don Annabi yana yinta a duk lokacin da ya zauna a majalisi in yazo tashi)._
_Oh! Ni Rash ina daga gefe na ce"wannan rayuwan bayin Allah ya burgeni gaskiya rayuwansu a kwai darasi sosai Allah yasa mu gane mu kuma d'auka Ameen"._
_Kdeey ta mik'e ta d'auki sallaya ta nike ta musu sai da safe ta nufi d'akinta sai da tayi addu'a kafin ta rufe k'ofa ta rage kayan jikinta tasaka na bacci, kan gado ta hau tayi addu'a ta shafa ta kwanta ta runtse ido, sai abunda ya faru d'azu tsakaninta da Aunty Samy ya dawo mata sam ita hankalinta bai gama kwanciya da matar ba sabida yanda take wasu d'abi'unta a kwai alaman tambaya aciki, da ire-iren wannan tunani taga bazai fucce taba nan ta fara yin tunanin akan abubuwan da tabaikata a yinin ranan ta auna mai kyau da marar kyau, sai da tayi istigifari ta tuba ma Allah(yana da kyau a kowani rana munayi ma kammu hisabi kafin ubangiki ya mana don ta hakan zaka iya gane ayyukan alkairin da ka aikata a kowani rana), kafin ta runtse ido bacci mai dad'i yayi awon gaba daba ita tana yinsa kuma cikin kwanciyan hankali._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam??_
0 comments:
Post a Comment