[10/08/08:41]
🎋 _SADEEY S ADAM_ 🎋
&
💖 _BEEBAH LUV_ 💖
WITH
🌲 _RASH KARDAM_ 🌲
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
*MA'YAUDARAH*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
*66-70*
Teemah ce zaune a falon gidansu tayi tagumi da hannunta duka biyun..
tsantsar nadama take, tayi nadamar abubuwan da ta aikata a rayuwarta...
Yanxu Ina samarin?Ina gayun?Ina ado da kwalliyar??,
Duk babu kowa ya gujeta k'awayenta duk sun gujeta idan ka d'auke Futha da take k'aunarta saboda Allah...
Umman ta ce ta shigo taga halin da take ciki,ga abincinta a gefe har ya fara hucewa..
Nasiha da rarrashi ta zauna tana yi mata wanda sai da ta zubda hawaye sosai..
Ina ma ace tun kafin wannan larurar ta sameta ta nutsi...
Kaii d'an adam yaji tsoran Allah dan kuwa ita darasi ce ga duk wata wadda take biyewa samari da wadda take cewa sai ta wanki gara..
Tabbas gara zai wanke ta ya barta a banza..
A yau Umma kam taji dad'i tunda har teemah tana kuka sbda nadama....
**********************
Ta gama shirya komai na lunch akan dining table..
Sannan ta Shiga d'aki tayi wanka ta cancad'a kwalliya cikin wani _Orange lace_ d'inkin _towel work_ ne yayi mata d'as a jiki tayi kyau sosai....
Ita kanta saida ta tsaya a gaban _mirror_ tana fad'in Anya nice kuwa..??
Falo ta sake dawo wa,taga har yanxu bai fito ba kusan awa uku da gama girkin har taje tayi wanka amma shiru kamar baya gidan??
Cikin fargaba ta nufi d'akinsa,
Da sallamarta ta Shiga
Yana zaune a k'asa Yana danna laptop,ba mamaki _chatting_ yake a _Facebook_ dan kuwa sai smiling yake yana ganin ta ya had'e rai kamar ba'a tab'a halittar annuri a fuskarsa ba..
A tsorace ta tsugunnan tace "Yaya an kammala abinci fa"
*Mtswww* yaja tsoki ya cigaba da abinda yake...
irin Mai mijin nan sai ta saka hannu ta rufe laptop d'in cikin tsokana tace "ka gama cin abinci kafin ka cigaba,kasan bana son ka zauna da yunwa"
Mari ya kifa mata har sau biyu "ke wace irin jahila ce da xaki rufe Abu ba tare da an kashe ba,uban wayace ki shigomin d'aki,to baxan ci abincin ba dole ne?stupid" ya fad'a cikin d'aga murya...
Rik'e kuncinta tayi sannan ta tashi ta fita tana kuka.
_By S🎋 B💖 R🌲_
[Truncated by Whatsapp]
0 comments:
Post a Comment