New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA PAGE 3

HANNUNKA MAI SANDA.......

Rash Kardam

Sanah S Matazu.

(3)

Malam Auwal haifaffan garin Kano ne,cikin kwaryar Kano wato Yakasai.Yana da matan aure biyu Mama Aishat ita ce uwar gida tana da yara hu?u duk mata.Hadiza ita ce babba tana aure a unguwar Dabai da yaranta biyu duk maza.Karimatu ita ce ta biyu tana aure a unguwar na'ibawa yaranta ?aya Ammar.Sai Sa'adatu da Maryam wanda suke matakin karatu a babbar makaranta ta yan mata ta Ummu~Samhat islamic secondary school dake titin nasarrawa.Maryam nada shekaru sha biyar tana matakin aji hu?u,Sa'adatu mai shekaru sha takwas tana matakin karshe.Dukansu sun sami kyakkyawar tarbiya yadda ta dace,auransu auran zumuncine suna kyautattawa juna dai-dai gwargwado.Malam Auwal ?an kasuwa ne,a kasuwar sabon gari aikinsa shi ne saida takalma.Mutum mai neman na kansa tare da kyautattawa iyalansa iyakar karfinsa.
Aunty Halima wadda suke kira Aunty Amarya,ita ce matarsa ta biyu yaronta biyar babbar ita ce sa ar Maryam wato Murjanatu sai Mussadik Mubashar da Mus'abu sai auta tagwaye Sanah da Sahiem mace da namiji.
Malam Auwal mutum ne mai ?kyautattawa iyalansa dai-dai gwargwado iyakar iyawarsa,da wuya su nemi abu basu samu ba daga gareshi.Kwatsam rumfarsa ta rufta cikin rumfunan da suka sami jarrabawar gobara a garin Kano.Hakan ya durkusar da duk wata walwala tashi da iyalansa.Mama kayin iyakar kokarinta wajan tallafawa yaranta harma dana abokiyar zamanta kasancewar tana kanannun sana'o'i danginsu kayan miya da omo da sairansu ga kuma kitso da Maryam take yi da kunshi ita kuma Sa'adatu ?inki take.Hakan yasa hidimarsu basu damu su tursassa mahaifinsu kan bukatun rayuwa ba.

A hankali matsi ya soma riskarsu,a tsarinsa duk sallah yana yankawa iyalansa manyan raguna biyu da sa ?aya,sa dashi yake rabon mabukata raguna ?kuwa kowace ?ai-?ai ita da yaranta sai wanda zata bawa.A duk lokacin da sallah tazo sukan haura shida Aunty Amarya kasancewarta mace mai son abin duniya gashi bata san zafin nemaba ita dai kawai bani-bani shi ne aikinta.Shekarar farko da ya gaza yin layya a gidansu tayi tafiyarta da sunan yaji,mahaifanta suka yi mata tas tare da korota.A shekara ta biyune ta tsiri rarraba masa yara zuwa gidan makota da dangi da sunan taya aiki.

?Hakan ba karamin tayar masa da hankali ya yi ba,Murjanatu ita ake turawa gidan makotansu Aunty Naja mace mai kirki da kawaici saikuma Lubabatu da itama Murjanatun ke tayata aiki kasancewar sai uku ga sallah suke yankansu.Sauran mazan kuwa gidan danginta take aikasu kota aikasu suyo fincine mahaifinsu na mugun takaicin hallayarta amma ko ajikinta an tsikari kakkausa inji yan magana.Tofa bana ko'ina rashi ya kur?a abincima wuya yakewa al'ummah masu ci uku safe da dare da kuma rana sun dawo ?ayanma na neman gaggara ciki kuwa hadasu Auntyn Muruanatu Naja wannan yasa tun kafin sallah ta soma kudurtar gujewa ?hallatar gidan a wannan karon.

*************************

Kamar kodayaushe cikin fara'a ta shiga gidan amma tun daga tsakar gida fuskarta ta sauya yanayi tamkar kashin shanu.
"A'a Murjanatu yar gatan Aunty, shigo mana kika toge anan sak'ek'e a tsaye tamkar sandar bafulatanin jeji".
Gimtse fuska ta yi tana duban

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts