🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
DAI-DAI RUWA
DAI-DAI GARI
(DON'T EXPECT TOO MUCH
IN
LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
NA
©RASHIDA .A. KARDAM
Pg-6~10
Aiki sosai sukayi da Ummita, na kayan shan ruwa, bayan sungama k'arfe 5:49pm tashiga wanka tare. Bayan ta fito ta gyara jikinta, kamar yanda ta saba, ta saka riga da skirt. K'arfe shidda da minti arba'in da biyu, aka kira Sallah. Bayan sun sha ruwa ne, ta huta ana kiran Sallah isha'i, ta mik'e don gabatar da farillah.
K'arfe tar saura ta idar da sallah, tare da yin yan dogon addu'anta ta shafa. Wayarta da ke gefe naji tana fidda sautin wakan (Sauti Safiyul bul-buli) sai da yadad'e yana k'ara, kamar zata tsinke, kafin ta d'auka cikin murya mai sanyin dad'i tace"Assalamu'alaikum.
Daga d'aya b'an garen aka amsa da Wa'alaikumusalam, Meedah ya kk?. Ina fatan kin sha ruwa lafiya?.
Sai da ta wani yatsina fuska kafin tace"Alhamdulilah!.
Yace"Mashaa Allah!.
"Hameedah gani a k'ofar gida ina jiranki.
Jin yana k'ofar gida, yasa ta mik'e da sauri, man baki kawai ta shafa, ta fesa turare ta fito.
Cikin nutsuwa ya ta iso, ta ce masa "anyini lafiya?. Ya ibada?.
Cikin girmamawa ya amsa da"lafiya kalau.
"Ya mutanen gida?.
"Lafiyalau" ta bashi amsa a tak'aice.
Ko da ta zauna a gefe sai dan satan kalon gefensa takeyi, ko zataga laida, ganin ba wani alama take taji, ya fara bata haushi, hiran ma ta daina bashi amsa sam.
Haisam na ganin yanayi Hameeda ya canza yace"lafiya kuwa Hameeda?.
Cikin ya tsina tace" hmm nagaji gida zan shiga?
Cikin damuwa yace"lafiya dai ko?.
"Lafiyalau, na gaji ne kawai.
"Ok! Ba matsala ya kamata ki huta kam.
Kafin ya sake magana tace"sai da safe". Ta nufi gida zuciyarta a cun kuse, damuwa fal cikinta, a zuciyarta ko cewa take"wai me Haisam ke nufi bare kawo min kayan azumi ba ne?. Ga Sallah ya kusa.
Tsaki ta saki a fili tare da shigewa d'akinta.
Haisam ko baiji dadi ganinta a yanayin da tat afi ba, jiki ba k'wari ya nufi gida.
Washe gari da safe bayan Hameeda ta gama aikinta, gidansu Khairat ta shiga, ta samu Khairat da Saleema, suna zance kayan Sallah, zama tayi cikinsu. Saleema tace"Meedat ya kamata wannan Sallah asan munyi wanka sosai, don ni yanzu damuwata a Sallah, ita canza photo a DP na da group, suma asan nayi wankan Sallah. Kuma kinsan Sallah kowa zata ta d'aura photo. Yanzu abunda na yanke na kira Isma'il nace ya sai min Holland, sai Ahmad kuma nace masa Less nakeso mai kyau.
Khairat tace"nikam ko ban fad'a ba nasan Anas zai saimin kayan kece raini nagani na fad'a.
Hameeda uhumm tace, Khairat tace"haba Meedat kice wani abu mana.
"Hameeda tace"hmm banda ta cewa don kinsan Haisam sai a slow, kayan azumi ma bai kawo min ba bare na Sallah.
Saleema tace"ni haushin Haisam d'in nan nakeji duk da ya had'u amma sam daga ganinsa bai sake hannu.
Khairat tace"gashi su Malam sun dage saishi, amma da badun haka ba ae da Hameeda ba k'aramin samuwa zatayi ba, sabida tana da kyau matar manya ce.
Hameeda tace ni da zakuyi shiru da yafi, don zuciyata na saka min munana abubuwa. Haka sukayita hiransu kowa tana fad'an nata ra'ayin, gameda saurayinta.
Saeed ne zaune gaban mai saida atamfa, sai da ya duba sosai ya hango wani Sheraton mai kalan ruwan ganye da ratsin yellow da baki, zanin yayi matuk'ar yin kyau sosai. Yace" mai shago mik'omin wannan mai green d'in.
Da sauri mai shago ya mik'o masa, ya duba yaga yana da kyau sosai. Yace"mai shago nawa prize d'in wannan?.
Mai shago yace"N6500 kawai. Saeed yace"haba mai shago ni customer ne ae ya kamata kamin ragi. Mai shago yace"hakane amma kasan kaya sun k'ara kud'i ga dollars sun tashi yanzu.
Saeed yace"duk da haka amin ragi kasan yanayi garin mu wata 5 wasu ba salary, wasu 3 wasu 2.
Hakane kam sai Allah ya kyauta, yanzu kawo N5500 kawai ok to nagode.
Yace"ka yanka min yadin hijab yadi uku, ya k'irga 7k ya mika masa ya karbi kayan ya tafi.
*DEDICATED TO*
*MY FANS*
*AS HAPPY SALLAH*
0 comments:
Post a Comment