New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI... PAGE 24

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(AUGUST 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*24*

_Sai da suka gama lalacewarsu suka tashi sukayi wanka tun daga wannan ranan Salima ta shiga cikin su Samy. Sannu a hankali kwana nesa gobe take d'aurin aure Samy duk wani shagali ayi su kamu kauyawa day. Yau Alhamis ta gabatar da walima duk wasu k'awayenta 'yan bariki sun hallarci gurin washe gari jumma'a bayan Sallah Azahar aka d'aura auresu. Da daddare aka kai marya gidanta washe gari akayi yini cikin lafiya da kwanciyar hankali._
_bayan an watse abokai suka rako Ango sai da sukayi 'yan barkwancin su kafin suka tafi. Bayan tafiyansu ango ya umarci amarya da tayi alwala suka gabatar da sallah tare da rok'on Allah ya basu zuri'a ta gari. Bayan sun gama ya baje musu kayan motsa baki suka motsa baki daga nan kowa ya nufi d'akinsa wanka tayi ta feshe jikinta da turare tasaka rigan bacci. Ango shima wankan yayi ya sa kayan bacci tare da fesa ma jikinsa turare ya nufo d'akin Amaryansa tun danaga Ango ya shigo na tattara 'yan matan k'afana nafita._
_kasancewar Mummy Samy ta zumata hakan bai sa ya gane tana aikata mungun aiki ba sabida Samy duk iskanci da zakuyi da ita bata yarda tayi amfani da abunda zai iya kamo ma budurcinta matsala sai dai a kare arungume-rungume da shafe-shafe d.s.s._ washe gari da safe ta narke masa nan ya ringa tarairayata kamar kwai. Tun gada wannan lokaci suka ci gaba da rayuwan auresu in yazo ya mata kwana biyu yaje gidan Uwargida ya mata kwana biyu, haka harkanta bata daina ba, barin ma in randa baya gidanta nan take samun daman tsola tsiyanta sam shi kuma bai ganewa sabida bata sake ya gane mai take aikatawa shi anashi fad'an yana alfahari da ita a matsayin mace ta gari.

                 *DEDICATED TO*
     *_KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam💕_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts