New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI PAGE 2

MOTAR KWADAYI

BY
Rash kardam

Page-2

Bayan sallar i'sha aysha na zaune tsakar gida ita da qawarta karima suna fira,

Safiya ta fito sanye da wani material riga da saker kayan sunyi mugun kama jikinta ga wani shegen Show ur back daya fitar mata da rabin waya waje sai wani munafikin gyale data dora a kafada ringing wayarta tayi da sauri ta dannan receive ta kara a kunne " gani zuwa yanzu "

Ido aysha da karima suka bita dasu tana kashe wayar ta watso musu harara " to kashedi dai wlh nan gani nan bari nafi karfin mutum tsaye da kyau zaune da kyau son kowa kin wadda ya rasa " ta karasa maganar tana ya mutsar fuskar

Ta nufi kofa tana wani yauki wai ita ala dole ga mai farin jini

Ajiyar zuciya aysha ta sauke karima ta kalle tace " tayi abunta banga laifinta ba tana da daraja dan shiyasa a samarukanta baba talaka " kallon tsoro aysha ta mata " haba karima ai darajar macce kyau tarbiyarta da kula da kare mutuncinta ba wai tara samari masu kudiba ko saka suturar banza ba dan kinsan duk namijin kirki bazai zo yace yana sonki ba kuma duk wadda ya ganki cikin wannan shigar bazai ga mutuncin kiba " karima tace " kuma fa hakane dan wani lokacin zakiga yan iskan ma matar kwarai suke nema in suka tashi aure Allah dai ya shirya mu " aysha tace amin wannan ai zubarda kimane ( hmmm ina ma yan matanmu zasu gane wannan ba wayeba bane )

Karima ta tashi tana fadin maganar kifa haka take amman fa gamai hankali nikan na tafi aysha saida safe to saida safe karima na gode sai mun hadi school,


............NA......
Rash Kardam

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts