New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI 56-60

MOTAR KWADAYI??????

56-60

Cikin ikon Allah anyi aiki lafiya lau, acire ciki murna agun Sofy ba'a magana, Alhaji ya had'o mata magunguna, da kayan ci masu kyau. Kula ta musamman yake bata, sai da ta warke sosai, tukun suka sake komawa ruwa don bata bar Abuja ba sai da tayi samaru biyi, kuma duk halin d'aya ne,Ta samu kud'i ba kad'an ba suka dawo Kaduna.

Kwanaki sun tafi, yanzu Ayshat ta kamala jaraba wanta, biki yarage saura sati d'aya duk dangi sun had'u sai shirye-shirye akeyi.

Sofy kuwa waya tayi ta sanar da Alhaji, dubai ya aika aka sayomata, wasu ready mate d'in kaya, Kala 6 da takalama su, wanda zatayi fitan biki kawai. Inna ta kuwa wani mai shago ta wanka ya bata Swiss less masu kyau, tabayar aja d'inka mata.

Ayshat bata shirya yin wani event ba, kasancewan mijinta bayida k'arfi, d'aurin aurene da yini kawai. Haka akayi ta su cin-cin, ranar jimma'a ta zago aka d'aura aure, da daddare mota uku sukazo d'aukan amarya, aka kaita gidanta, washegari yini karkuso kuga inna da d'iyarta don sunyi wanka kece raini, wankan nuna masa'a. Ko ina a gidan biki su ake nunawa, baran Sofy duk kayanda tasaka abinsone. Wasu kuma gulmasu suke a ina take samun kud'i haka?.�

Yayinda wasu dangin uban yan neman k'ora, sun makale musu, yini kam a gidan amarya Alhamdulilah! Biki ne na rufin asiri bana k'arya ba.

Da dadare yan'uwan Umma, suka saka Ayshat tayi wanka ta canza kaya, nasiha sosai suka mata, da gwada mata irin gidan ta suke, tarike bakinta banda gulma, kuma duk kashin abunda mijinta ya kawo, tamasa godiya, ta amsa da mutunci. Kuka tayi sosai dakyar ta barsu suka tafi. Ni ko Rash na zo gulma don inga yanda d'akin Amarya ya tsaru. 'Daki d'aya ne, sai gadonta da kujeru guda biyar, sai d'an fridge karami, da tv karami. 'Daki dai sai son barka a talakance yayi, abokan ango ne sukayi sallama, bayan sun zauna, nasiha sosai sukayi Ayshat, sannan suka musu fatan alkairi, suka tafi abunsu.

Bayan tafiyansu ne, Khaleel ya umurceta da tayi alwala suyi Sallaha, ba musu ta d'auro alwala, suka gatar da sallah, yan tambayoyi ya mata gameda addini, ta bashi amsa. Kayan da yazo dashi ya d'auko musu, tana yar kunya ya ringa bata abaki, saida ya tabbatar ta qoshi tukun shima yaci. Daga nan yasoma janta da hira, ganin ango da amarya suna buk'atar hutu, yasa na fito a d'akin, don ba hurumina a gun, nidai Rash na musu fatan alkairi, naja musu qofa aci Amarci lafiya.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts