🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
DAI-DAI RUWA
DAI-DAI GARI
(DON'T EXPECT TOO MUCH
IN
LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
NA
©RASHIDA .A. KARDAM
Pg-11~15
Da murnansa ya nufi gida don yasan, Ummin Yusrah sa zatayi murna da kayan nan yanda ba salary, ga gari ba kud'i. Shiko nashi bai saya ba, ya had'a da yar laidan shinkafan da yasaya mudubiyar ya nufi gida da sallamansa ya shiga. Ummin Yusrah ganin Abban Yusrah da laida yau yasa ta mik'e da sauri ta tarbesa da fara'arta, bayan ya zauna ta masa sannu da dawowa. Ya masa cikin fara'a kamar kulum, zama yayi akan kujera tare da cewa "wash yau na gaji da yawa. Ummin Yusrah duk ta k'agu taga mai ke ledar, laidar katan Sallah ta ya mik'omata, da murna ta karb'a ta bud'e, zanin ta d'auko tare da karanta k'asan zanin taga an rubuta Sheraton. Cikin bal'acin rai tace"mai zangani anan badai Sheraton zansa a sallah ba?
Abban Yusrah yace"eh gashi kin gani.
"Kin san yanayin garin bana ba kud'i, ga shi ba albashi kuma d'an business d'in ma sai dai muce Alhamdulilah.
"Hahaha cab ae ko ban san wannan zancen ba ni kam bazan saka Sheraton ba.
"Ina laifin da Swiss ka sayo min ko Super Wax Exclusive ka sayo min ko cut less.
"Kasan irin shirin wankan da nayi niyan yi a sallah nan kuwa?.
"Inason yan group d'in mu susan na saka manyan sannuwa, kuma karsu rainani.
"Ga irin su Futha Lurv, Amrah ga Rabee'at, Munay, Duk nasan ba k'aramin wanka zasuyi ba.
"Ni gaskiya bazan iya saka Sheraton ba kuma har nad'aura a DP na ina.
Abban Yusrah cikin ta kaici yace"Haba Ummin Yusrah kinsan wahalan da nayi, kafin na samu kud'in kayan?.
Cikin tsiwa tace"ni duk ba damuwata bane, illa in ganni cikin kaya mai kyau.
"Cab ae ina d'inka wannan bazan so Aisha S Mazoji ta ganni da kayan ba, ita da take yawan canza DP ga saka kaya mai tsada.
"Kuma duk wanda na lissafo maka suna ji dani, suna min kalon matar manya, gaskiya sai kanimomin zani mao tsada shine zaman lafiyanka a gidan nan.
Wurga masa zanin tayi jikinsa, taja ta rik'e k'ugu. Abban Yusrah yana tsananin sonta sosai, bai son bacin ranta. Can tace"to meye kuma a d'ayan laidar?.
Da sauri yace mata"shinkafa ce a aciki na siyo mana.
Ido ta zaro tace"shin me?.
Yace"shinkafa mana.
Tace"ae ko sai kaci abunka don na gaji da cin shin kafa.
"Haba Ummin Yusrah kisani fa *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI*.
"Kuma ae ko yatsun hannumu ba dai-dai suke ba.
"Don me zamuna kallon na sama damu?.
"Kisani duk kashin abun da muka samu, yana da kyau mugode ma Allah sai ya k'ara mana.
"Ehehehe yau kadawo Malam ne?.
"In ka gama wa'azin sai kayi min bayani. Ledar ta jawo ta wurga masa tayi d'aki fuuu.
A fili yace"haba Ummin Yusrah kinsan yanayin garin nan wasu shin kafan ma suna nema basu samu ba, amma ke har kina ikirarin kin gaji daci.
Laidar ya d'auka yasaka a gefe, ya fita waje, duk abin duniya ya ishesa.
Sam Ummin Yusrah ta fita harkan Abban Yusrah akan in bai sai mata kayan Sallah mai tsada ba ita gidansu zata koma. Kwanaki sun tafi har yau Sallah saura Sati ganin har yanzu fushi yake da ita, itama tana fushi dashi. sai da ta tayar masa da hankali, ya kaiga sakinta.
Ta d'auki Yarta tayi hanyan gidansu, tana zuwa ko ta samu Dad d'inta yayi tafiya zuwa Umrah, sai Mum dan haka ta shera mata k'arya ta barta ta zauna, akan sai Dad ya dawo ya kira Abban Yusrah yaji mai ya had'asu.
Shiko tunda ya dawo yasamu bata nan ya d'au alwashin bazaije biko ba tunda yana da gaskiyansa.
Hameeda ce zaune abin duniya ya isheta, wai ace Haisam ya rasa mai zai kawo mata na kayan azumi sai kayan fruit, kuma acikin laida gari yayi zafi, wan nan ai abun kunya ne. Wa zan kira nanuna masa kayanda wai saurayina ya kawo?.
"Ina bazan iya ba, ga su Khairat yanzu sai anuna kayansu hala.
"Mtss gaskiya dole Haisam ya fita a hark'ata nima nasamu wanda zaina min wal-wala.
*DEDICATED TO*
*MY FANS*
*AS HAPPY SALLAH*.
0 comments:
Post a Comment