°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*12*
_Yabo ya mata mai sanyaya duk zuciyan masoyi Malam ya na k'ok'arin gurin nuna mata soyayya dai-dai gwar-gwado duk randa ko bayida aiki to zaka samu yana taya matarsa aiki har su gama komai tare zasu yi rayuwansu gwanin burgewa ga duk wasu masoya._
_Fatima ba ta da k'awa a unguwan sai Aunty Aisha wanda ta girmeta shiyasa take kiranta da Aunty, Aisha ita ma tana girmama Fatima duk wani shawar-wari tare su keyi, in taga Fatima tayi abinda bai da ce ba a matsayinta na babba zata kirata ta bata shawar-wari ta kumacd mata wannan abunda kikayi ba dai-dai bane kazan nan shine dai-dai, Fatima tayi mata godiya haka rayuwansu ya kasance._
_Kwanaki sun tafi Fatima ko b'atan wata bata tab'ayi ba gashi yanzu shekaransu hud'u da aure, abun ya soma da munta ko tana ganin matsalan daga gareta ne nan ta fara matsa wa Malam ya nimi aure tunda sunje asibiti ga kuma na gida da take sha duk ba canji Allah bai kawo lokaci ba._
_Malam sai da ya gwada mata b'acin ransa ba ya ce"Fatima wai kina tunanin dun baki samu haihuwa sai na k'aro aure ko d'aya inayi niyar aurena zanyi amma ba ta dalilin haihuwarki zan yi ba". Kan ta a sunkuye idonta ya ciko da hawaye cikin sanyin jiki da sanyin murya ta ce"Yaya Ahmad ka fahince ni zan so ace nice macen da zata fara ajiye maka 'ya'ya amma Allah bai k'addara ba, ka sani zan so ace naga k'oyinka a duniya bai kamata mu zauna haka ba tunda Allah ya hallata maka auren mata har uku zaka k'ara dani mu zama na hud'u"._
_Cikin fishi ya mik'e ya fita abunsa nan Fatima tashare hawayenta cike da nadaman abunda ta fad'a masa, aikinta taci gaba da yi gaba d'aya niyin ranan sukuku tayishi don Malam ko gida bai dawo ba nan tashiga damuwa don ta saba kulum tare suke cin abinci. Malam bai dawo ba sai bayan sallah isha'i yazo ya sami Fatima ta had'a kai da gwiwa tana kuka a hankali ya tako ya zauna a kujera duk sai yaji ba dad'i tunda dalilin kukanta akansa ne, kafin yayi magana Fatima tazo ta tsuguna a gabansa ta ce"Malam dan Allah kayi hak'uri nayi lafi kuma ba zan k'ara ba"._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment