°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*16*
_Da Sallamansa ya shigo gida ya samu su Inna da Fatima a falo k'asa gefen Fatima ya zauna ya gaida Inna sannan ya ce"Inna ga d'an wannan ba yawa ayi hak'uri da shi". Inna da fara'arta ta ce"Ah! Madallah mungode ai mai yawan kenan Allah yayi albarka ya k'ara bud'i yasa ka fi haka kai amma mungode sosai Allah yasaka". Cikin jin dad'i Malam Ahmad ya amsa da "ameen". Cikin zuciyarsa ya jin dad'i kalaman Inna sosai wata zuciya ta ce"gaskiya a zamanin nan kayi sa'ar surka ta gari yanzu sai ka zaga surkai goma da kyar kasamu mai hali irin na Inna gashi sun bama Fatima tarbiya mai kyau Alhamdulilah! Ya Allah nagode maka da ka azurtani da Fatima a matsayin mata kuma na san 'YA'YA na zasuyi alfahari da ita a matsayin Uwa ta gari tabbas nayi da ce da mace kwarai, shiyasa a ko da yaushe nake k'ara gode ma Allah don da kyautar da ya min"._
_Inna sai da tayi wata uku kafin ta koma lokacin cikin Fatima wata biyar haka rayuwansu ya ci gaba da gudana cikin jin dad'i da k'aunar juna tsakanin Aisha da Fatima ko ba abunda ya ragu sai wanda ya karu don suna mutumta juna sosai Malam Ahmad da Malam Jibrin ma sun k'ara ninkewa sun dawo d'aya.*******_
_4 months latter._
_Aunty Aisha na hango suna fita da Fatima daga gani nak'uda takeyi mota suka shiga da ita suka nufi Asibiti Malam Ahmad ko addu'a yakeyi ma Fatima Allah ya sauk'eta lafiya a haka har suka iso Asibiti nan aka shiga da ita labour room (d'akin haihuwa). Malam ya fara zarya a gun hannusa yana sak'ale a bayansa sai addu'a yake ma Fatimansa. Wasa-wasa Fatima sai da ta d'au kusan awa biyu da rabi bata haihu ba ga kan d'a yaso fitowa ganin haka wasu nurse suka fita da gudu suka kira likita basu dad'e ba suka dawo da likitan ta shiga ta duba Fatima ganin halin da take ciki tace sai an mata operation, nan suka fito da takarda suka ce“waye mijin Fatima Ahmad?". Da sauri Malam Ahmad ya ce“gani nan". Likita ta ce“muna so ka saka hannu a takardan nan zamu shiga da ita Tiyata". Jikin Malam ba kwari ya saka hannu basu dad'e ba suka fito da ita a kan gadon tura marasa lafiya Malam da sauri yazo gunta idonta cike da hawaye ta ce"Malam ina maka laifi a iya zaman mu da kai ka yafe min ina ji a jikina kamar bazan tashi ba kace ma iyayena su yafe min". Ta juya ta kalli Aisha ta ce“Aunty na ki kula min da Jiddah sosai kuma ki yafe ina tab'a b'ata miki rai". Malam hawaye yakeyi yayin da Aisha ma kuka takeyi Jiddah da take k'arama ganin mai mata wasa yau bata mata ba ta saki kuka tana mik'a ma Fatima hannu ta d'auketa amma ina ba halin d'aukarta nan aka wuce da ita cikin d'akin Tiyata._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment