New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA LAST PAGE

: HANNUNKA MAI SANDA.........

BABIN KARSHE.........
"Gaskiya yau My Dear nasha wuyar azumin nan",

Cewar Lubabbatu kenan tana jujjuyawa tana rike da cikinta.
Murmushi ya su?uce masa ya ce,

"kinga da Najjash ya girma sai ya yi azumin nan".
"Saboda me Daddynsa?".

"Saboda falalarsa Mommynsa".
Ajiyar zuciya ta yi ta ce,

"Allah dai ya kaimu munsamu ikon ganin arfa kasan arfa akwai falala".
"Tabbas kuwa Mommynsa domin Manzon Allah Yace: "Mafi alkhairin addu'a ita ce Addu'ar ranar Arfa, kuma mafi alkhairin abunda na fad?a ni da Annabawa da suka gabace ni shi ne:

.

*??? ?????? ?????? ??????? ???????? ??? ??????? ????? ???? ????????? ?????? ????????? ?????? ????? ????? ?????? ???????*

.

"LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHAREEKA LAHU, LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'EEN QADEER ."

.

" Wato babu abunda yafi cancanta a bauta masa sai ALLAH, shi ka?ai, bayi da abokin tarayya agare shi, Mulki nasa ne (shi ka?ai) Yabo ma nasa ne, kuma shi mai iko ne akan komai."

.

[Sahihu Tirmizi 3/184, Ahdeeth Assaheeha 4/6]

.

??? ????? ???? ???? ??? ?????? (???? ????): "?? ???? ???? ??? ???? ???? ?? ?????". (?????)
Sheikh Muhammad Salih Bin Uthaymeen Yace: "Wanda ya yi sake Azumin Arfa ya ku6uce masa babu ramako."Wannan yana ?ara tabbatar maka da cewa idan kayi sake Azumin Arfa ya ku6uce maka baka yi ba, to ka sani cewa shi ba a rama shi sai dai idan wata shekarar ta sake zagayowa, kuma baka da tabbas akai domin watakila wannan shi ne shekararka ta karshe a rayuwarka".
Cikin murmushi ta ce,

"Allah yasa mu dace".

****************

RANAR SALLAH.....
Daukacin al'ummah kowa ka gani fuska cike da nisha?i da murmushi a tare dashi, hakan ce ta kasance ga kaffatanin iyalan Malam Auwal sunyi kwaliya shar dasu bayan an sauko masallaci ya yanka rago aka gyara aka rarrabawa makota rabi aka shiga gida da rabi. Aunty Halima ta hana Mama ko cangal ita da yanmatansu suka ha?u suka soya suka gyareshi tas yasha yajin tafarnuwa nan da nan ta mikawa Mama shi a soyensa kaf ko ?aya bata ta?aba sai na ?an?ane da suka ci ita da yara.
Bayan magarba, ko ina tsit sai kamshi ke tashi cikin unguwa Mama suka kawo masa nama suka dire gabansa.
"Wannan fa?".

Ya fa?a da sigar tambaya, suka kali juna sukai murmushi tare da ha?a baki wajan fa?ar,

"kawowa mukai ka raba".

Cikin murmushi ya dubesu,
"Aunty Amarya gaskiya wannan fagenki ne ke zaki raba".
Sune kai ta yi tana murmushi, cikin nutsuwa ta raba ta bawa kowa cike da farin ciki......
Masha Allahu! Alhamdullillah tammat bihamdulah.
Duka-duka anan muka kawo karshen wannan takaitacen rubutu mai taken HANNUNKA MAI SANDA......muna fatan wannan takaitacan rubutu ya zamo izna ga masu aikata hali irin na Aunty Halima mu rage kwa?ayi da buri ita duniya ba aljannah bace komai lokacine.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts