New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI PAGE 5

MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
5
Haka suka dage masa gurin karatun addini, ahaka har yayi saukansa na Al'qur'ani mai girma, bayan shekara 8 da saukarsa Allah yayi ma babansa malam sabo rasuwa, bayan ya rasu haka zaije yayi aiki ya dan samo musu na abinci, ana cikin haka Allah ya hada shi da uwargidansa wato Amina soyayan su sukeyi sosai dakd irama iyayenta ba wasu masu kudi bane, cikin ikon Allah bai samu wahala gurin aurenta ba, akayi biki dai2na talaka a ka kai amarya.

Suna zaune cikin kwqnciyan hankali da soda kaunar junansu, haka rayuwansu yayi ta tafiya har suka kai 4 yrs da aure, amma shiru ba wani lbr ko batan wata bata taba yiba, ana haka mahaifiyar malam muhammadu ta tashi da matsanacin ciwon ciki tun kafin akaita asibiti Allah ya karbi abunsa sunyi yan koke, bayan rasuwarta da shekara 2 yan'uwan mahaifin shi suka daga masa hankali wai sai ya kara aure, don matarsa juya ce su kuma suna son ganin jikan dan'uwansu, duk suka tsan gwami amina bata isa tayi abuba su mata caaa a kai, wataran tayi kuka ta koshi harsai ta gode Allah, san'n kulum tanata rokon Allah ya bata yaya na gari masu Albarka.

Wasa-wasa yau anshafe shekara da yin maganar aure bako alamar haihuwa, nan suka hura ma muhammadu wuta dole ya sa ya fara neman shawaran Amina ganin ba sarki sai Allah yasa tace ya kara aure kawai, tasan Allah na tare da ita, ciki ba kwari ya fara binciken wace zai aura wanda bazata takura ma Aminarsa ba, ana haka har Allah ya hada sa da Hafsat tayi aure watan 9 da aure ya mutu, sabida tsaban fitinarta, ahaka dai aka lallaba akayi auren ta tare, tun da tazo tasoma tsiran iskanci dayake taji yana son haihuwa. Da gan2 zata fito tasoma sheka amai, ko in amina ce da abinci tace bazata ci ba wai bata son warin iskanci kala2, wai ita a dole cikine da ita, ana hakako bai dadeba Allah ya bata na gsky, karkuso kuga farin ciki agunta.

...........Na......

Rash Kardam

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts