New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 26-30

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍧🍹
                        ```NA```

```Ummieeluff```😘
               &
```Rash kardam```

Page
26~30

Murmushi tayi tace "Allah sarki ummana kina sona nima ina k'aunarki Allah yabani kud'i in gina miki k'aton gida kaman garin bauchi.

Bata wani bata lokaci ba ta kama hanyan gida ahanyanta na tafia ne ta gamu simbiat "yauwa yau wana kama?" simbie ta kama zazzare idanu dan tasan halin mugunta irinna candy. " ina tambayanki wana kama? Jiya ina rokanki alewan madara kika hanani kika gudu,toh yanzu kinga babu kowa dagani saike in lakad'i banza in more" simbie ta soma komawa da baya tana neman hanyan gudu. Candy na binta "aiyau sai kinci na jaki watarana idan na rokeki abu ki hanani" nan ta cabko wuyan riganta,tun kamin ta fara dukanta simbie ta suma kuka. "kai meya had'aku"  sukaji anfad'a daga bayansu. Ammah candy koh ah jikinta taki sakin wuyan riganta. Mutumin ya tsinko bulala yana zuwa,dataga yayi kusa sai ta saki wuyan simbie tareda faska mata wani zaz'zafan mari dayasa simbie sakin ihu ta tsuguna. Taruga ah goge gobema kimin rowa ki gani.

Tana shiga layin gidansu ta hango Anush ta mamanta sun nufo hanyan gidansu,da sauri ta buya jikin wani bishiya dan kada su ganta "kambu ammah idan Aneesa tasa ran mamah ya baci saina mata d'an karen duka"  suna wucewa tabi bayansu,basu gantaba ahankali take binsu har suka kawo kofan gidan. Ko sallama babu suka shiga cikin gidan.Allah sarki baiwar Allah tanata tsince'tsincen kara da zata had'a wuta.kawai taga mutane ah kanta kerere. " ah ah maman Aneesa ce sannu da zuwa ga wurin zama" tafad'a tana kokarin shin fid'a musu tabarma. "Kinga ba zama ya kawoni gidanki ba, nazone kijama yarki kunne kada ta sake dukan min d'iya" shiru tayi tana sauraron abinda take fad'a. Yama za'ayi yarinya da gidan ubanta ahanata sakewa, kinsan Aneesa bata iya fad'a ba tana zamanta tanacin abinci wannan kande d'in ta shigo ta cinye mata abinci hakan bai isheta ba ta kara mata da duka" ina mata magana zatamin rashin kunya ta gudu,ai talauci ba hauka bane".idan ran mama yayi dubu to yabaci. "Yanzu khadijan ce taje tayi miki rashin kunya har gida"? to dan Allah kiyi hakuri idan tazo zanmata fad'a" matsowa tayi wajen Aneesa "kiyi hakuri kinji mamana insha Allah bazata sake dukankiba".

"Inama zata sake ganinta, ki sakawa yarki ah kwa'kwalwarta idan nasake ganin kafanta ko wucewa tayi ta kofana to sainasa an karya mata kafa" janyo Aneesa tayi kamar zata cire mata hannu suka fice daga gidan. Candy dake labe tayi saurin buya dan karsu ganta. Suna wucewa ta fad'o cikin gidan da sauri. Yanda taga fuskan mamah tasan ranta yayi mugun baci. Da sauri ta isa wajenta "mam"...kamin ta karasa mama ta wanka mata mari. Cikeda tsoro candy ke kallonta dan mama bata dukanta, ta manta yaushe rabonda aka zegeta balle harya kaiga mari.

"khadija meyasa kike son sa kanki ah bakin mutanene?,bakisan harshe guba bane,kullum saikin nema min abun magana a anguwannan. Haba khadija saikin kasheni, da bakin ciki tukunna zakiji dad'i" da sauri ta dago kanta dan batason ana am'bata mata mutuwa musam'manma mamanta. haka mamata rinka mata fad'a shiru tayi ranta abace..ta kudurta aranta idonta idon Aneesa saita koya mata hankali tunda tasa mamanta bacin rai.



*TAGWAYEN MARUBUTA*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts