???? *ZAMAN MAKOKI*????
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*41to50*
Candy jikinta na rawa ta ja hannu Munay suka nufi k'ofar gidan rasuwan suna zuwa suka gaida mazan da ke *```ZAMAN MAKOKI```* a k'ofar gidan. Kayan drinks ake shiga da shi ga manyan jeep suke tsayawa suna ta'aziya suna shiga zauren suka mammatsa idonsu suka fara hawaye kafin suka shiga da kuka.
Ga wasu suna zaune sai brush suke da naman saniya manyan tsoka ga wata rantsatsen abinci kai ka d'auka gidan biki ne.
Wata Hajiya ce ta shigo ta sha less ta sha gayu kai ka d'auka zab'en kyawawa zata sai wani takun k'asaita take in ka ganta bazaka dauka a gidan mutuwa ta ke ba.
Ga wanni lafiyayyen kamshin da ke tashi tamkar tayi b'arin turare. A hankali ta taka zuwa d'akin da ake karb'an tana gai dasu tukun ta dan zauna. Candy da ta sake baki sai kallon matar take yi don ta gama burgeta, Munay ce ta zun gure ?ke zo muje muyi abunda ya kawo mu tukun". Gurin da suka ga ana d'iban abinci nan suka nufa ba kunya su Candy suka saka hannu suka d'au plate suka zuba abinci naman kai d'in kuwa kamar da gayya suka saka tsaban had'ama goran Fanta bibbiyu suka dauka. Gefe suka koma suka fara jan abinci wata Mata ne ta shigo ita ma cikin shiga ta alfarma sai da ta shigo ta hangi wannan Hajiyar nan fa suka fara aika ma junansu da kallon-kallo. Kowacce a tuanninta ta gama kure adaka amma kashh!! Sai gashi sun ga juna kuma duka cikin shigan ba rai ni dalilin da yasaka suka fara kalon-kalo ma junansu.
Munay ta kalli Candy ta ce?kiga wa'yannan matan kallon da suke majuna kamar ba gidan rasuwa ba kuma inaga hakan baya rasa nasaba da sun dauwanka mai kyau shiyasa suke kallon-kallo ma junansu".
"Mtss abun da bai dameka ba dad'in ji gareka ina ruwan mu. Kowa yayi abunda ya ficce sa mu ba gashi cin shefe(shinkafa) shi ya kawo mu, kawai muyi mu tafi".
Mai sayar da pure wata ya bi su Candy bai gansu ba nan ya tafi yana kuka don ya san sai an dakesa a gida amma duk randa yaga Candy sai ya tara mata jama'a ta bashi kud'insa.
Sai da suka kai gejin k'oshi kafin suka sud'ad'e suka bar gidan .
Candy na dawowa gida ta canza fiska da sallama ta shiga sai da ta gai da Umma kafin ta ce"kai Umma gsky Munay tana jin jiki amma da sauki har an mata allura ma".
Umma ta ce"ayya Allah ya bata lfy gobe zanje na dubata in Allah ya kai mu".
Idon Candy yayi tsuru-tsuru jin gobe Umma zataje duba Munay take wata dabara ta fad'o mata cikin sauri ta ce"la! Umma ai basai kinje ba ma naji kamar Mamanta ta ce gobe da safe zasu je Gashuwa".
Umma ta ce"ayya! Allah ya sauwake ya kai su lafiya".
Bayan kwana biyo komai na tafiya wa Candy lafiya suna zaune a k'ofar gidan su Autan Hajiya nan suka ga wasu Christian sun wuce da motar gawa acikin akwati da alama daga asibiti suka d'auko za'aje bikin birne shi. Da sauri da lakato Munay ta ce"kaa kalli mu hanzarta mubi bayansu don kar su mana nisa da alama ba daga unguwan nan suke ba".
Munay ta mike da sauri ta ce"aikam don yunwa nake ji sosai".
Candy ta jata suka fara sauri suna bin motar kasancewar bata gudu sosi motar a slow take tafiya.
Candy ta kalli Munay ta ce"nifa kinsan duk randa banci shinkafan gidan Mutuwa ba bana jin dad'i ji nake kamar ba abinci naci ba shiyasa nake ala-ala ayi mutuwa.
Ganin motar ta fara gudu yasa suma suka saka gudu.
Motar gawan ta nufi Abuja Road Magajin garin dai-dai Wushishi road ta tsaya, nan suka ga ta faka a k'ofar wani gida aka fito da gwan aka shiga gida basu dad'e ba sai ga motoci aka tafi gun da za'ayi biki.
Mutane sun fito sai ihu suke yi suna kira jejous name Candy ta ce"kai nifa yau naka sa kuka fa". Munay ta ce"ni ma idona kyamas yau".
Candy kamar wacce ta tuna wani abu ta waro hannu zaninta sai ga *ROB* ta ce" mud'an shafa wannan abakin idon mu zai yi hawaye na Umma nane da ta aiken". Nan fa suka goga kan kace me sai ga hawaye suk
0 comments:
Post a Comment