MOTAR KWADAY
By
Rash Kardam
10-15
Safiya rayuwa ta mata dad'i,ayarta take shekewa, yanzu har gun party, take zuwa ko 'karfe nawa ne, zata kai ba tare da ta damu ba. In ta dawo gida innarta bata damu da taji inda ta tsaya ba, tun sau d'aya da ta tambaye safiya, ina rake kwana?. Safiya tace"sunje bikin kawarsu ne dare ya musu, shine suka dawo gdnsu 'kawar suka kwana, tun daga lokacin inna bata k'ara tambayarta ba. Malam da yayi magana sai tace"dun yaga yarta tana samun naira shine yake jin haushi, kuma tasan zuga sa akeyi, ana musu bak'in ciki. Yayi fad'an ya gaji don Inna masife shi takeyi, shiyasa ya zuba musu ido, yaga gudun ruwansu. Duk wani gun hutawa, na garin kaduna ta san da zamansa, amma ko dawasa duk son kud'inta bata yarda ta bada mutuncin ta ba, yawancin samarin da suke nimanta, jikinta suke farauta, ba son gsky bane. Duk soyayyan da zakuyi da ita, sai dai ya tsaya a kiss, hug, da makaantan su, ko a gaban waye kuwa bata kunyan namiji ya tabata, ta saba da hakan, bata kunyan kowa, kana kalonta kuwa idonta a tsatsaye suke, na rashin kunya, ba komai ke rud'n ta ba face farin da take dashi da kyanta da ya bayyana.
Ayshat kuwa, karatun ta take, ba wasa aciki, yanzu haka tana SSS3, gata da 'ko'kari, in debate ko competition, ita ake d'auka, ga yawan kyautar, da take samu daga makaranta. Hakan ya kara bata kwarin gwiwa, da zage damtse, taka tasamu result mai kyau. Umma ta kuwa, kulum fatan alkairi rake ma d'iyarta.
Safiya ce ke shiri, don yau suna da party 'kawarta, kuma till down zasuyi, kud'i ta d'auko ta saka a jakarta, ta nufi kasuwa, wasu matsatun kaya tasayo riga da wando, daga kasuwa kuwa, shagon saloon ta nufa, aka gyara mata gashinta mai kyau, da kyali. Bata dawo gida ba sai bayan magriba. Wanka tashiga, sai da ta d'au 15 minutes tana wanka, kafin ta fito ta tsane jikinta, ta d'auko kayan make-up d'inta tasoma kwalliya, ni Rash nace"wanan irin gayu ne haka, kamar mai shirin ganawa da shugaban kasa, hmm. Sai da ta kusa 1hrs tana make-up, kayanta, da tasayo ta sanya, duk wata hallita na jikinta ya bayyana, sun matseta kamar zasu yage, ta kalli kanta, a katon madubin da ke d'akin, tun daga nesa na hango S.A Azeez, da Zee hrt sun saki baki, suba kalonta, nima Rash na tab'a Khadija Candy, nace"wai mai su Zee suke kallo ne?. Juyawa mukayi, tare da bin gurin da suka zuba ido da kalo, dan muga mai suke ma, irin wannan kalon, bamu san, lokacin da muka had'a baki tare da cewa"Ohohoho mai karatu kunganta kuwa, ai ko Falmi bazata gwada mata kyau ba...lol.. Allah yayi halita a gurin. After dress, ta d'auko ta d'aura akan kayan data sa, in ka ganta bazaka ce tayi banzan shiga ba. Tuurarukanta masu sanyin 'kamshi ta d'auko ta fessa, take gurin ya d'au kamshi. Labulen d'akin Innan ta, ta d'aga tare da ce mata"na tafi gun party Seema, to sai kin dawo, labulen ta sake ta fita. Napep ta shiga, sai gidan su Seema. Duk k'awayen su, sun had'u ita ake jira tana shiga, cikin gidan aka fara mata kirari, Mai kyau da kasai ta, hayakin taba, yar duniya, Sai ke Safiya lashe money, wani fari da ido tayi tare da juya jikinta ta ko ina.
.......Na......
Rash Kardam
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 10-15
MOTAR KWADAYI PAGE 10-15
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment