°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*17*
_Malam jikinsa yayi sanyi suna zaune a gun kowa da addu'a da yakeyi zuwa can likitoci suka fito d'auke da fara'a a fuskansu nan suka shaida musu a kammala komai lafiya a cire mata 'Ya mace nan Malam yayi hamdalah, ba su dad'e ba aka fito da Fatima a ka kaita d'akin hutu nan Malam ya kira 'yan uwa ya shaida musu kar kuso ku ga murna a gun su Malam._
_Satin Fatima d'aya aka sallameta washe gari akayi suna yarinya ta ci sunan Khadijatul~kubrah haka suka ci gaba da kula da d'iyarsu Aunty Aisha ma ba'a barta a baya ba gurin nuna ma Khadija k'auna komai zata saya musu iri d'aya ne da Jiddah haka rayuwa yayi ta tafiya har su akasa Khadija a makaranta cikin ikon Allah tana karatu gata da k'ok'ari Malam kuma yana koya mata karatu a gida kuma yasata a Islamiya hakan yasa ta taso da hazak'a ko da tayi wayo tana kiran Fatima da Ummina ko Umma._
_Umma bata barin Kdeey da kawaye sai Jiddah ta hana ta yawan kawaye don acewarta yawan kawaye yana kawo d'anka ya lalace amma in kawaye basu da yawa zaka dage gun sanin ina suke zuwa mai sukeyi.**********_
_6 years latter._
_Kdeey na hango sai murna takeyi yau ta kammala makaranta ta fito da sakamako mai kyau hakan yasa Malam yayi iya k'ok'arinsa ya sanya ta a private school sabida k'ok'arinta shi da kanshi yake kaita a mashin d'insa in lokacin tashi yayi yaje ya d'auko ta haka rayuwa taci gaba da guda na Kdeey na zuwa makaranta kuma bata da k'awar da ta wuce Jiddah ko ina tare su ke zuwa don in tayi sabuwar k'awa sai Ummata ta bi diddigi tasan 'yar waye don gudun had'uwa da munanan kawaye kuma kulum tana cikin yi mata addu'a da nasiha_. _Aunty Aisha ma in suna tare da ita da Jiddah nasihan take musu da gwada musu halin rayuwa da basu misalai kala-da-iri hakan yasa suka had'a kansu basa cika son haya nita ba._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment