New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA PAGE 9

: HANNUNKA MAI SANDA........
Sanah

Rash�
9
Kwanci tashi ya rage saura kwana uku sallah, fannoni da dama kowa ka duba hada-hadarsa yake musulmi sun cika da farin ciki koda rashin da ake yi dayawa basu sare da lamarinba domin sunyi imanin ubangijine mai yi kuma bakin da ubangiji ya tsaga baya hanashi abinci. Haka lamarin yake mudun zaka dogara ga ubangiji to kuwa zai tallafa maka cikin yardarsa.
Suna zaune Malam Auwal ya shigo hannunsa rike da babbar leda mai ru?in baki da ruwan ?orawa Sa'adatu nata hidimar ?inki gefe Maryam na fama da masu kunshi sunata hada-hada da sauri Murjantu ta taso ta kar?eshi suna yi masa sannu da zuwa ya sauke idonsa a kansu yana murmushi.
"Yauwa Murja an Baba a gyara akai marka?e saboda yin bu?a baki an jima".
"To Baba bari in gyara"

Tana bu?ewa idonta ya sauka kan kayan miya da nama, ta yi murmushi tana jin da?i nan da nan ta gyara ta bada Mus'abu ya kai marka?e kafin la'asar ta hattama komai.
Kafin akira sallah sun salami kowa sun kamawa Murjanatu aikin nan da nan suka ha?a bu?a baki ana kiran sallah kowa ya ci dabino suka kuskure baki mahaifinsu ya jasu jam'i.Bayan sun idar anci ansha sai nisha?i suke ana yaba da?in girkin mahaifinsu ya yi gyaran murya yana dubansu ya ce,
"Hakika wa?annan ranaku ne ma su falala. Domin hadisi ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abb?s (ra) ya ce: Manzon Allah (saw) ya ce: ?Babu wasu ranaku da ayyukan alkhairi su ka fi soyuwa a wurin ubangiji (swt) kamar wadannan ranaku (goma na farkon Zul-Hijja).? Sai su ka ce: ya ma'aikin Allah (saw) ?ko da jihadi fisabilillahi ne?? Sai manzon Allah (saw) ya ce: ?Ko da jihadi fisabilillahi ne, sai dai mutumin da ya fita jihadi da ransa da dukiyarsa, bai koma gida da wani abu ba (ma'ana: ya yi shahada a fagen fama har da dukiya baki daya).? - Sah?hul Bukh?r?: 969.
Haka kuma, an kar?o daga J?bir Ibn Abdullah (ra) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: ?Mafifitan ranakun duniya su ne ranaku goma (na farkon Zul-Hijja).? Sai aka ce da shi: ?babu kwatankwacinsu ko a jihadi fi sabilillahi?? Sai ya ce: ?babu kamarsu sai dai mutumin da aka turmuza fuskarsa a cikin turbaya (Ma?ana: an kashe shi, ya yi shahada a fagen fama). - Sah?h al-Targ?b, juz?i 2, shafi na 32, hadisi na 1150, Sha?kh Alb?n? ya ce: hadisi ne sah?h? liga?rih? (ingantacce ga waninsa).
Don haka Sa??d Ibn Juba?r ya kasance yayin da ranaku goma na farkon Zul-Hijja su ka shiga, yana yawaita ibada a cikinsu. Yana da kyau ga dukkan mai qaunar manzon Allah (saw), ya kasance yana kyautata ayyukansa a cikin wadannan ranaku.

�Mafi soyuwar aiki a wa?annan kwanaki shi ne, azumin ranar Arfa, ko da ta dace da ranar Asabar.Don wasu Malaman kamar Sha?kh Nasiruddinil Alb?n?, da almajirinsa Aliyu Ibn Hasan al-Athar?, su na ganin ba za a yi azumin ranar Arfa ba, in ya dace da ranar Asabar, saboda sun inganta hadisin da yake haramta yin azumin nafila ranar Asabar. Sai dai mafiya yawan malaman hadisi, sun raunana wannan hadisin da hujjoji ma su qarfin da lokaci ba zai ba mu dama mu kawo su a nan ba.
Amma dalilan da su ke nuna za a iya yin azumin Arfa koda ya dace da ranar Asabar sun hada da hadisin da aka karbo daga Ab? Hura?rah (RA) ya ce: na ji manzon Allah (saw) yana cewa: ?Kada dayanku ya yi azumi ranar Jumu?a, sai dai idan ya yi azumi kafinta; ko zai yi azumin bayanta (ana nufin: azumin nafila). - Sah?hul Bukh?r?: 1985, Sah?h Muslim: 1144.
Abin nufi da azumi kafinta; azumin ranar Alhamis; bayanta kuma shi ne ranar Asabar. Wannan ya nuna ana yin azumin nafila ranar Assabar.�
Haka kuma, an karbo daga Ab? Hura?rah (RA) daga manzon Allah (saw) ya ce: ?Kada ku kebance daren Jumu?a da yin (qiyamul laili) a tsakanin darare. Kada kuma ku kebance ranar Jumu?a da azumi a tsakanin ranaku, sai dai idan ya kasance azumi ne da dayanku ya saba yins

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts