°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*13*
_Jikin Malam yayi sanyi hannuta ya kamo ya janyota jikinsa ya soma share mata hawaye ya ce"Fatima ba ki min komai ba kuma bawai ina fushi da ke bane yau ban zauna bane komai ya wuce". Ya karasa maganan yana murmushi da kansa ya mik'e ya d'auko abinci ya shimfid'a musu dadduman cin abinci ya kamo hannuta ya zaunarta akan dadduman ya zauna shima shi ya rink'a bata abaki sai da ya tabbatar da ta k'oshi kafin ya fara ci ta rik'e hannusa da kanta ita rink'a basa shima sai da ya k'oshi, daga nan suka wanke hannu ya k'ara mata karatu kafin sukaje bayi tare sukayi wanka suna soyewansu abun gwanin burgewa._
_Bayan kwana hud'u Aunty Aisha ta tashi da nak'uda hankalin Fatima ya tashi ganin yanda Aisha keyi yasa tafara hawaye tana mata addu'a a haka Malam Jibrin yazo da mota aka kai ta Asibiti cikin ikon Allah bata dad'e sosai ba ta haifo d'iyarta mace kyakyawa da ita tubarkalla mashaa Allah ma'aikatan asibiti suka gyara 'Yar suka mik'ota ma ubanta ya ganta ya tofeta da addu'a kafin ya mik'ata ma Fatima hannuta har na rawa ta amsa tsananin farin ciki ne a bayyane a fuskanta har cikin zuciyanta take jin k'aumar 'yar itama addu'a ta mata ta k'ara rungumeta a zuciyanta itama ta na fatan"Allah ka babu 'ya'ya muma". Sai da ta rufe baki ta tuna da irin addu'a da tayi wandawasu masu niman haihuwa haka sukeyi basa niman mai albarka, da sauri ta sake ce wa"Ya Allah ka azurta mu da 'ya'ya na gari masu albarka amin"._
_Aisha aka fito da ita da sauri Fatima taje ta rik'o ta tana murna daga nan suka nufi gida duk wani aiki hidiman haihuwa Fatima keyi bata nuna gajiyawarta har ranan suna yarinya taci sunan Hauwa'u suna kiranta da Jiddah sunyi bikin suna lafiya Aisha ta ci gaba da kula da d'iyarta._
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment