[24/7/2:30pm]
💖BEEBAH LUV 💖
&
🎋SADEEY S ADAM 🎋
WITH
🌲RASH KARDAM 🌲
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
MA'YAUDARAH
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
52~54
Yau saura sati biyu bikin Futha Yau ne aka kawo lefe na gani na fada don kuwa Marwan yayi rawar gani, a lefen kowa ya yaba sai san barka.
Teemah kam ba karamin mamaki tayi ba don kuwa gani take Marwan mugun talaka ne bashi da komai,, a tunanin ta Futha kawai wahala zata je tasha a gidan shi, saboda baida kudi, ita nata tunanin indai ba mai kudi ta aura ba to wahala kawai zata je tasha a gidan mijin.
kee Futha amman fa Marwan yayi rawar gani whl ashe daman yana da kudi kuke nunawa bashi da kudi ke da shi ko?
Hhhhh daria Futha tayi tace a a ni mijina baida kudi yana da rufin asiri dai, da kuma zuciyar yi, hmmm Allah yasa dai a dore a hakan, amin inji Futha don tasan halin kawarta sarai yanzu sai su fara kace nace.
Kwanci tashi ta karfin wasa a gurin Allah, komai aka sa rana zaizo karshe, Yau Thursday yaune aka fara bikin Futha Yau za ai kamu da walima gobe Friday kuma za ai luncheon ranar Saturday kuma ayi daurin aure ayi dinner ran Sunday kuma akai amarya.
Su teemah kawayen amarya, a gaskia yayi rawar gani a bikin tayi barin nera, tayi kuma fa jikin ta, don kuwa tun ana sauran sati daya ta dawo gidan don yin hidimar biki.
Biki yayi biki an rakashe sosai an kuma zubar da nera, don kuwa ango ma basaja yayi ma amarya ashe ba talaka bane me kudi ne yana son dai ya sami me son shi tsakani fa Allah ne, ba don kudin shi ba, kuma ya samu sai dai fatan zaman lfy.
Ankai amarya gidan ta dake unguwar nasarawa G.R.A. ai teemah bata gama tsinkewa ba sai da taje gidan amarya ta gani sannan.
Harda dan bakin cikinta a gefe, wai daman ita ce. Hhhhh yar dunia kyaji dashi.
Rufaidah an zama yan makaranta, an nemo mata B.U.K level 1 inda su hidaya ke level 2 hundred, sun fita da aji daya.
Komai nata na tafia neat a gidan ta kara kiba ta kara fari da kyau kamar ba ita ba.
Mamyn su farouk ce zaune tana shan fruits, ta wani bangaren kuma tana hango dacewar farouk ya auri Rufaidah, sai dai bata son ta gaya masa ko ta sanya shi yayi Dole tafi son ya furta da kanshi.
Zata ci gaba dayi masu addua in Akwai alkhairi Allah yasa masu son junan su, in hakan ta kasance sai tafi kowa farin ciki.
Areef kam abu kamar wasa wai karamar magana ta zama babba tun ranar da umman su tayi mashi maganar hameedah ya kasa sukuni, karshe dai har sai da ya kwanta a asibiti, umma kuwa cewa tayi whl Areef ko zaka mutu ka dawo sai anyi auran nan,, ka yarda ko kar ka yarda babu fashi indai nina haife ka bakai ka haife ni ba.
Bayan sati biyu ne da fitowar shi daga asibiti, yaje har gida ya samu farouk yake gaya masa ya taya shi addua ga abinda umma tace,, farouk ne ya taso yazo dab dashi yace abokina don Allah ka saurare ni da kunnen basira, umma fa uwa ce a gareka kuma nayi imani baza ta cutar dakai ba, kayi hkr ka faranta mata, kaga ita kadai kake da ita baba ya rasu, kayi kokarin faranta mata har ranar da zaku rabu, kayi mata biyayya don Allah, whl baza ka tabe ba,
Amman rashin yi mata biyayya akan auran nan da take son hada ku babban kuskure ne kayi hakuri kaci gaba da addua Allah ya sanya albarka a cikin auran.
Whl ka ganni nan ni har so nike ace mamy ta hada ni da watan ma don kuwa yan matan yanzu sai a hankali har gwara ma ka auri ta gida, wadda kasan halin ta, akan ta wajen duk mayaudara ne akasarin su.
Nan dai Areef yayi ajiyar zuciyar yace a gaskia farouk ko da zan auri hameedah to whl ba dan ina so ba zan yarda da auran amman fa ba zata samu soyayya taba, don teemah kawai nike so kuma ita zan so, babu wata mace da zata samu soyayya ta bacin ita.
Kayi hakuri Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, yace amin.
Yana komawa gida direct dakin umma ya wuce yake gaya mata ya amince da auran hameedah, umman taji dadi sosai ta ringa sanya mashi albarka, yanzu yaushe kake ganin za saka ranar? Yace ai komai yana wajen ta duk yanda tayi, sai in suna bukatar kudi suyi magana zai basu tun daga hada lefe da sauran abubuwa, tace Allah ya kai mu lokacin, ai wata daya za a saka yace yayi ummina tace yau babana Allah ya maka albarka.
Nan dai ya tashi ya dakyar don baijin kwari a jikin shi ya nufi dakin shi.
Umma kam komai yayi daidai harta fara shirin biki, ankai kudin aure gidan su hameedah,, ranar Friday ma zasu tafi Dubai ita kawarta don zuwa hada lefe da abinda ya kamata.
Hameedah kam sai murna take Allah ya amsa adduar don tana kaunar yaya Areef sosai shine dai baya sonta, kuma ta dau alwashin sai ta bi duk wata hanya da zata bi,, don ta shawo kansa ya sota fiye da kowacce mace.
Toh masu karatu muje zuwa dai don jin yanda zata kasance ku biyo .....
🎋S💖B🌲R
[truncated by WhatsApp]
0 comments:
Post a Comment