New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 6-10

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧

_Ummieeluff😘_
        &
_Rash Kardam_

Page~6/10

Bayan ta gama ciye'ciyenta ta zame ta kama hanyan gida tana mai ciki da farin ciki, dan ta koshi sosai ta jima bataci abu mai dad'i irin wannan ba. Tana tafia tana wake'wakenta harta iso anguwansu dake tudun wada hausawa road..jikin wani gida ta tsaya,wanda bangon gidan kadan ya rage ya fad'i karamin gidane maidaici..sallama tayi tun daga kofan gidan,sannan ta shiga, d'aki kwaya d'aya ne ah tsakar gidan sai wani ginin daya rushe daga gefe..da kuma d'an wani akurkin kajinsu,sai kuma wani kichen d'in langa'langa dake jikin akurkin d'akin.

Hango mahaifiyarta tayi nata faman hura wuta yaki kamawa duk idanunta sunyi jajaye abun tausayi,duk iskancin khadija tana mugun son mamarta bata son taga tana shan wahala..dan ita kad'ai take da ita aduniya. Da sauri ta isu inda take "sannu mama kawo na hura miki" ta kar'bi hura wutan,dataga baida niyyan kamawa ta fita waje tsintan ledodi da ruba sabida ta samu saukin hura wutan. Tana shigowa ta had'a wutan ya kamaci kamar wanda aka xuba masa petrol, " ummah me xa'a d'aura"? Nuna mata wani tsohon tukunyan tower tayi "d'auki ki dumama mana tuwun jiyane da  bakiciba ya rage"..nan take khadija  ta 'bata rai dan ah duniyanta ta tsani d'umame ballema tuwun dawa..da miyan kuka shar daga gishiri saidan magi dabai wuce kwaya 2 ba. Ah xuciyanta tace "ohh Allah ya taimakeni danaje gidan ```MAKOKIN NAN``` naci abu mai dad'i son raina,da yanxu saidai na kwana da yunwa" .

"Candy" maman ta kira sunan ta,d'agowa tayi tana kallonta,"toh ki daura abincin mana kikabar wuta naci bayan kinsa babu itacen"da sauri ta d'aura tuwun akan wuta tareda xama daga gefenta. " waini ina kika shigane tun safe kina yawo ah anguwannan"? Mamah gidansu Haneefa naje ..shine su nana suke fad'a mana anyi rasuwa anan layin yan kosai,shine mukaje gaidasu".  "a'a kikaje dai dan bayanda xa'ayi rasuwa ah anguwannan ace ba'a sameki ah wajenba" wai me kike samu ah xuwa gidan makoki ne? Candy tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta. "koh bada ke nake magana ba,ki fad'a min dalilinki na yawan zuwa gidan makoki da kikeyi? " eyy amm muna zuwa gaishe da sune fa' bayan kin gaishesu toh zaman me kikeyi? Ta zungoro baki "muna cin shinkafa..ga kuma drinks kala2".  Innalillahi wa'inna elaihi'raju'un" mamah ta fad'a tareda rike baki." yanzu abunda kuke zuwa yi kenan ah gidan makokin? Kai duniya abin tsoro yanxu rasuwan ma baya bawa mutane tsoro saidai aje ayita hira anacin abinci kamar gidan biki" toh khadija Allah ya shiryeki..ki kumayi hankali da xuwa gidan makoki..dan talauci ba hauka bane."toh toh mama basu bane suke bamu.."oho nidai na fad'amiki kiyi hankali da biyebiyen gidan makoki.

```Shin wacece khadija (Candy?)```

_khadija Abubakar Alkali_ shine cikakken sunanta..mahaifinta malam Abubakar Allah yamasa rasuwa tun tana qarama..bata wani saba dashiba..dama sana'ansa shine facin tayoyin mota da keke..bayan rasuwansa Maryama  watoh mahaifiyar ta kenan taci gaba da d'aukan dawainiyar yarta tilo guda d'aya khadaji wacce akafi sani da candy..candy nason mamanta sosai sabida ta wahala akanta ainun..kullum magananta mamana,banida kowa aduniya sai mamana. Koh Aure batason amata maganan sa sabida bata son rabuwa da mamanta. Matsalanta d'aya masifan son xuwa *Gidan Makoki* da Allah ya d'aura mata,koh muce ta d'aurawa kanta.duk nisan inda taji rasuwa toh insha Allahu xakuga candy acan..burinta kawai abinci da drinks..kowanne cikin kawayenta taji anyi rasuwa toh xai sanar da dan uwansa..su d'ebi juna xuwa gaisuwa kodako basusan suba..su zarah B B ah gaba..na kalli rasheeda,itama ni take kallo atare muka had'a baki wurin fad'in,```ikon Allah!```


*TA GWAYEN MARUBUTA*😘

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts