[18/7/07:08pm]
🎋SADEEY S ADAM🎋
&
💖BEEBAH LUV💖
WITH
🌲RASH KARDAM🌲
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
MAYAUDARA
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
51-52
Ya kasa cewa komai har Saida tace "ko baka jina ne"?
Yasa hannu ya dafe goshinsa sannan yace "hajia pls ki d'an k'ara bani lkci koda 1week ne"
Kallonsa tayi cike da mamakinsa tace "bazai yuwu ba,tunda baka da yadda xakayi dole ka auri hameedah shine mgna dan bazai yuwu ana ta jan lkci ba"
Kamar ta fad'a mai ranar mutuwar sa hka ya d'ago kai ya kalleta a firgice
Amma kuma Sai ya kasa cewa komai kawai sunkuyar da kai yayi bai san lkcin da hawaye ya gangaro a idonsa ba tsabar takaici.
"Areef kuka kake dan za'a had'aka Aure da 'yar uwarka jininka"?
nan ma bai bata amsa ba,, mamaki yake bata shin wace irin soyayya yake yiwa teemah?? Gskya yana matuk'ar sonta har cikin xuciyar sa
Kallonsa ta sakeyi,tausayinsa take yi sosai dan duk namijin da yayiwa Mace kuka lallai so na musamman yake mata.
"kaje kawai anjima Sai mu k'arasa maganar Naga ynxu u'ar nt in d mood"
Tashi yayi ya fita jikinsa babu k'wari
Duk mgnar da Akai Akan kunnen hameedah dan hka yana fita ta ruga bedrum da gudu
ta fad'a kan Bed Tana kuka,shin meyasa yayi Areef baya sonta?? Menene teemah ke dashi Wanda ita Allah bai halitta mata ba?ai itama Mace ce kuma Allah bai rageta da komai ba
Meye bata yiwa yaya Areef duk dan Tana k'aunarsa, amma ashe aikin banxa take yi baya sonta ko kad'an.
Kukanta tasha babu Wanda ya sani har ta gaji ta share hawayenta tayi alk'awarin insha Allahu xata yi istihara ta nemi xab'in Allah idan auren yaya Areef alkhairi ne Allah ya basu xaman lfya da hak'uri da juna
Idan kuma ba alkhairi bane Allah yasa a raba auren a barshi ya auri wadda yake so
Haka tayi ta tunani kala2 cike da damuwa a ranta
****************
Cikin Sallama ta shigo gidan, Futha na zaune a tsakar gida ta baje Kaya Akan tabarma gefenta kuma raw silk ne sky Blue shima gasunan da yawa
Fuskarta d'auke da murmushi ta amsa mata sallamar
Teemah ta k'araso ta zauna Tana dariya tace "Amarsu ta ango" hmmmm
"meye na cewa hmmm?"
"bbu komai Naji anayimin kirari tun kafin na zama amaryar"
"ba dole ba,neman fada muke tunda Naga ynxu an daina yi dani ko nemana ba'a yi, wai har a d'akko anko ban sani ba wlh besty kin k'aro wulak'anci"
Dariya sosai Futha tayi sannan tace "ke dai xa'a cewa kin k'aro wulak'anci,ba'a gaya miki naje ba? Kusan sau uku Ina zuwa Bakinan ynxu tunda kinxo Sai kiyi gaba da ankonki"
Hararta teemah tayi "wlh Baki Isa ba ki kaimin gidanmu nima"
"bani kaiwa nima ynxu busy nake,gashinan atamfa ta yini material shine na kamu dinner kuma babu anko amma xakiyi shigar Kaya peach Wit sky Blue Head tie shine gate pass,but na siyo raw silk ga Wanda keso,kuma saura ki kai inda baza ayi miki d'inki da wuri ba kinsan dai saura 1 mnth bikin"
Teemah tayi murmushi tace "kaji amare"
"dalla ki daina ce mini amarya ai ban xama ba"
"amma ai kin kusa ki barmu a kwantai"
😳"ni a suwa duk samarin naki,ga Areef ga Khalid ga bash duk gasunan da yawa amma ace kinyi kwantai"
Hmmm "wai Areef mtswww mubar mgnar nan plx"👏🏻
"Mun bari amma zaki xo ki bani lbri"
Nan dai suka d'an yi hira duk haushi ya eshi teemah dan hka kawai tashi tayi tayiwa Futha sallama ta tafi tare da kayan anko
Futha Kam dariya kawai take dan tasan ta k'ule teemah
ta Wani bangaren kuwa addua take yi mata Allah ya shiryeta ya ganar da ita gskya....!
Urs.....
🎋S💖B🌲R💘
T...........by Whtspp
0 comments:
Post a Comment