MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
16-20
Kirari suke mata, nan take taji kanta ya kara girma.Babbale botilan After Dress d'in tayi, take, sura jikinta suka bayyana, kayan jikinta sun mata kyau, shewa suka saki,tare da fad'i yar duniya cikin ki, mrar kyai wajenki mai kyau. Wani lallausan murmushi ta saki, Seema ce ta d'aga waya, ta kira KB ta sanar masa sun shirya. Ba'a dad'e ba sai ga motoci uku sunzo, duk wacce bata da motarta, sai ta shiga wanda aka kawo, sai karfe 11:30 suka bar 'kofar gidan Seema, sun yi tafiya mai nisa, kafin suka isa Silver Sand Hotel, dake cikin garin kaduna, an kawata gurin gwanin burgewa, sun isa 12:7 don har sun makara, wanda suke da mota har sun hallara, manyan guys masu ji da kansu ne a gurin, suna isa bayan sun sauka, wayar Safiya ce Goinee M3 tayi 'kara, tana d'agawa sunan Mubson ta gani a scream d'in wayan, cikin shagwaba ta d'aga, tace" nayi fishi tun da ka bar k'asan baka k'irana kamanta dani. Cikin tattasausan murya yace"kiyi hak'uri, aiki ne yamin yawa, amma yanzu na shigo 9ja yau sai kin gaji da ganina. Cike da murna tace"haba mumushi ya mata, tace"ina wani abu zamiyi waya d'an anjima, ok! Ya kashe wayarsa. Ko da ta duba, su Seema sun shiga, tun tana waya ta mudu alamar su fara shiga. A hankali ta fara takawa, zuwa cikin hall d'in, duk wani matashi mai ji da naira, da kuma tashen rashin kunya, to ya hallara a gurin, yawancin su ya'ayan manya ne. A hankali take tafiya harta zo 'kofar hall d'in ta saka 'kafarta, a han kali take tafiya har tanufi kujeran da take kusa dana Seema. Tunda Safiya ta saka k'afarta, Mai dalla ya hangota, ido ya zuba mata ko kyaftawa bayayi, gsky beb d'in ta tafi dashi, daman duk yan matan gurin ba wacce ta masa. Melan ne ya tab'asa, tare da cewa"Bad Boy mai kake kalo hak?. Safeya ya nuna masa, cikin murmushi yace"wannan ae Sofy ce, yarinyan tana da kyau,amma sam bata bada h'ad'in kai wa samari, duk yanda akayi da ita. Bad boy ya sauke wata ajiyar zuciya, tare da cewa" ni kuma yau sai na d'an-dana ta, don yawuna ya tsinke, kuma sai na maidashi. Ya sake kallon Melan yace"ko kasan abinda tafi so?. Melan ya d'aga kansa yana tunani zuwa wani d'an lokaci yace"abu biyu na sani shine, yarinya manyar kud'i ne, don har sun mata la'kani da lashe money, kuma tana son namiji kyakyawa, kaga ka had'a duka, sai dabara ya rage naka, kasan hanyar da zaka bi ka ja hankalinta. Ajiyar zuciya tare da cewa"bari ka gani yau ko party baza'a karasa damu ba, gidana zan tafi da ita. Melan yace"in ka tafi da ita ka sanar ni, nima sai na... Wani harara ya aika masa, ya mike, cikin takun 'kasaita yake tafiya, Seema ne tafara kus-kus ma Safiya, tace"kinga wannan Don ne, ba k'aramin kud'i, yake kashe ma budurwa ba. A hankali yake taku har ya iso gunsu, gaisawa sukayi da Seema, yace"ya kwana biyu? Seema tace" lfylau, hira yarinka jan su dashi. Safiya kuwa ta share, can ya nisa yace" nikam Seema k'awarkin nan bata magana ne?. Seema tace" tanayi kai Safiya sunanta, nan dai sukayita hira, har yasamu yaja Safiya waje, cikin motarsa suka shiga, da gan-gan ya bud'e, lokar da ke jikin motar, kud'ine ya bayyana, karaf ko sai a kan idon Safiya, sai da ta lashe wasu miyau. Rufewa yayi kamar mai niman abu, can sai ya d'ago ya kalleta, hira suka fara yana d'an tattabata, bata hana sa ba can ya fara shafata, ganin kar tace zata ki, yasa yaja motar sa, don zuwa inda yake son cimma burinsa.
Shin Bad Boy yana samun abunda yake so a gun Sofy?.
Ya Sofy in taga abun da take so, zata iya sayar da daranta?.
Ya rayuwanta zai kaya?.
Ayshat tana dauwa ma a cikin kunci, da rashin saurayi?.
Don samun wayan nan amsan, kubiyo,
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 16-20
MOTAR KWADAYI PAGE 16-20
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment