°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*26*
_Suna gamawa sai da tayi wanka ta ci kwalliya tukun Soby ta rakota gun motarta ta shiga ta taho gidanta._
_Hutu sosai suka sha tukun suka fara shirin komawa makaranta sai da sukaje suka biya kud'in makaranta suna layin biyan kud'i Kdeey tazo biya suna zaune cikin Kdeey ya soma ciwo ganin yanda take cije baki yasa Samy ta matsa kusa da ita ta ce“Kdeey lafiya dai?". Sai da ta cije baki ta ce“cikina ke ciwo". Samy ta ce“ayya sannu". Ana cikin haka Samy taga wani wanda ta sani sune masu aikin take Samy ta masa magana ya ce“kawo na muku". Batare da b'ata lokaci ba ta karbo nata dana Kdeey dana Zeena basu k'ara minti talatin agun ba aka gama musu komai Samy ita ta kama Kdeey ta ce“muje in sauke ki a gida Kdeey fir tak'i sai da Samy tayi ta lalalbin ta da kyar ta yarda suna shiga mota sai da tafiya da ita chemist ta musu bayani suka bata magani tabiya kud'i sannan ta shiga shagon drinks ta sai mata su multina da peak milk da kayan motsa baki ta had'a mata har k'ofar gidansu Kdeey ta kaita ta rufe motar ta kamata suka shiga cikin gidan._
_Samy ta yi sallama sai ga Umma tafito ganinsu ta ce“sibhanallah asha mai ya sameta?". Samy ta ce“bata jin dad'i ne cikinta ke ciwo sai da suka kaita d'aki Samy ta gaida Umma sannan ta koma mota ta shigo da kayan Umma tayi godiya sannan Samy ta musu sallama ta tafi. Tun daga wannan rana Samy tasamu saran zuwa gaida Umma tun bata sakewa da ita har suka fara sabawa sosai a makaranta ma ta ja Kdeey kusan tare suke zama sun saba sosai. In suna tare da Samy suna tare da Kdeey ta rinka yi mata wasa da hannu tare da tattab'ata Kdeey ta b'ata rai sosai ko ta matsa hakan ne ya faru randa ta rakota gida. A kwai randa har runguman Kdeey tayi ranan Kdeey ta tsorata hakan yasa da zasu tafi islamiya take ba ma k'warta kuma Aunty Jiddah 'yar gidan Aunty Aisha labari ._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment