MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
8
Haka rayuwan gidan ya kasance, yau dad'i gobe ba dad'i. Malam Muhammad yasa safiya da Aysha, a primary sun fara zuwa kamar a'bun kirki safiya tace"ita bazata iya zuwa ba. ta gaji da wani zuwa makaranta. Da ky'ar Malam Muhammad"ya lallaba safiya taci gaba da zuwa kama ranta, har suka gama primary.
Aysha kam ta kasance mai son karatu bata wasa ko a class ita ke zuwa musu na d'aya, hakan bak'aramin tayar ma safiya hankali yayi ba, wani sa'in kam cewa take "Aysha tana satar amsa ne take cin jara bawa.
Ko da suka tafi secondary Safiya na Jss2, Aysha ke Jss1,Malama'i sun santa sabida k'okarinta, jarabawar da tayi na na zango farko, ita tazo na d'aya. Ta samu ky'autu'tuka.****kwanaki sun ja, watan'ni sun shud'e, shekaru sun tafi. Safiya ta dawo cik'ak'iyar budurwa mai ji da kanta, makaranta ma sai ta ga dama take zuwa, ita ce gun party, da duk wani gurin hutawa ta san da zamansh'i.
Sam bata harka da yaran area su, sai ya'yan masu kud'i. Samaru kanta kuwa bazaki ce ga yawan su ba, don in dai zaka bata kud'i ko nawa ne zata sau'rareka, shiyasa ni da Candy "mun mata lak'ani da Lashe Money...lol... Bare kuma in kana da mota ae kaine abun so da k'auna.( kira gare ku Yan'mata, karki d'au son duniya da ky'ale'ky'alen cikinta su rud'e ki, kina biye ma Samarin Zamani, don zasu kaiki su bari ki, Samarin yanzu ya'wanci su yan'karya ne, kuyi hattara).
Aysha ko tana da ky'au sosai don duk wanda yasan sirri ky'au to ta fi Safiya, sai dai Aysha baka ce bakuma irin baka wuluk ba, tana da haske ga bakinta mai shining ne, k'irjinta sun cika gw'anin bur'gewa, ga maza'unata das-das da su.tana da diri mai ky'au, tamkar ita tayi kanta.
....... Na.....
Rash Kardam
0 comments:
Post a Comment