°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*8*
_Da safe bayan tayi Sallah asuba ta shiga d'akin Umma ta gaishe ta sannan ta gaida Abba, falo ta fito da Al-qu'aninta ta fara karatu don hakan k'a'ida ne da safe sai sunyi izu d'aya in ranann aiki ne in kuma asabar da lahadi ne sunayin izubi biyu kafin suyi aikin abinci safe daga nan su karya. Ko da ta gama karatu kasancewan yau asabar makarantar hadda kad'ai zata tafi, kitchen (madafi) taje ta taya Umma soya kusai Umma kuma ta dama kunu suka gama aiki, falo suka dawo suka karya tukun Kdeey ta mik'e ta d'ibi ruwa mai zafi ta nufi bayi tayi wanka, ko da ta fito da zani d'aure a k'irjinta sai tawul da ta yafa a kanta. Tana shiga d'aki ta shafa mai ta ciro kayan Islamiyyanta ta saka tare da saka safa ta d'aura nikaf, bata tsaya fesa turare ba kasancewar sanin hukuncin fesa shi ga mace in zata fita, ita k'a'idanta ne duk randa tayi guga zata fesa ma kayanta turare d'an dai-dai shiyasa ko yaushe kayanta suke da k'amshi haka cikin akwatin tama._ _'Dakin Umma taje da sallamanta ta ce"Umma na gama shiryawa har nafito". Umma da take gyara wasu kaya d'aki ta ce"to sai kin dawo", duk sai taji wani iri falo ta fito taga Malam shima ta russuna ta ce"Abba na tafi makaranta", cikin sakin fuska tare da murmushi a fiskansa ya ce"Khadijatu a dawo lafiya 'Yar alkairi kuma uwar alkairi". Murmushi tayi taji dad'i kalamansa tayi godiya ta fita, kamar wacce tayi gagarun mantuwa ta juyo abun har yaba mani Rash mamaki._
_Abba ne ya ga tashigo ya ce"Khadija lafiya dai ko?", ta russuna ta ce"mantuwa nayi a gun Umma", ya ce"oho to tana ciki ai". Da sauri ta shiga d'akin ta nimi gu ta zauna ta marai-raice fiska alamar tausayi da damuwa mai tsanani Umma ta kalleta ta ce"lafiya naga kin dawo?", Kdeey ta fara hawaye ta ce"Umma na b'ata miki rai ko dan Allah kiyi hak'uri ki gafarceni dan Allah bazan k'ara ba". Cikin rashin fahimta Umma ta ce"lafin mai kuma kika min? Ni bakimin komai ba", Kdeey tayi rau-rau da ido ta ce"to Umma gani nayi kullum in zanfita sai kimin addu'a amma yau bakimin ba shine na d'auka ko laifi na miki". Ta k'arashe maganar hawaye na zuba, Umma ta taso tazo ta share ma Kdeey hawaye ta ce"d'iyar Albarka bakimin komai ba wallahi kuma kiyi hak'uri kinsan d'an Adam ajizine yau aiki ne yasa na manta da miki addu'a". Nan take Kdeey ta sauk'e ajiyar zuciya mai k'arfi nan Umma ta mik'ar da ita tsaye ta ce"diyar Albarka Allah ya kare minke daga sharrin mutu da aljan ya baki sa'a yasa ki rayu a addini ki haifi *'YA'YAN* acikun musulunci Allah ya miki Albarka sai kin dawo"_.
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment