New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI... PAGE 6

°•°•° *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(JULY 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*6*
_Malam ya d'an muskuta ya gyara zama ya ci gaba da ce wa"yatsun hannu mu ba dai-dai suke ba wani yafi wani kinga *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI*  tanan ma ya isheki misali da tunani abunda nake nufi shine kada ki hangi na sama da ke ko kiga k'awayen ki suna da abu kaza ko an sai musu kaza, kice zaki saka rai ko lalle nima sai na samo abu irin na wacce hakan ba dai-dai bane yana sanya mutum kaucewa hanya ya kai ka ga halaka wanda bama fatan hakan Allah ya kare mana ke da sauran *'YA'YA* al'umman Annabi ameen dan Allah ki k'ara kula ki kama kanki ki kula da tarbiyan da muka baki"_. _('Yan uwa wannan irin nasiha yana da kyau mu rink'a tasa Yaran mu gaba muna musu, muna tunasar dasu jin tsoron Allah ko da bama tare da su ki kuma yawaita yi ma *'YA'YANKI* addu'a alkairi don zai na binsu, sannan banda kiran Yaro shege d'an abu kazan uba, tsinane, sai naci ubanka, la'ananne tsinane yaro wawa fitinane, banza, dabban yaro d.s.s, hakan yana k'ara kan garar da Yaro kuma yazo ya fiti neki da al'umma wanda ke Uwa kuma kece ummul-aba'isin hakan sabida jifansa da munanan kalamai masu had'ari kuma mafi yawanci matan hauwa ko ince iyaye suna yawan aikata hakan kuma kisani bakin uwa kan d'anta yana da matuk'ar tasiri, wani lokaci  lafin da yaro zai miki ba yawan duka shine zai sa ya shiryu ba a'a addu'a ko inya b'ata miki rai kice wane Allah ya shiryeka/Allah ya maka Albarka kinga hakan zai bisa dan Allah iyaye mukula mu kiyaye)_.
_Jikinta a sanyaye ta amsa da"Ameen Abba nagode Allah ya k'ara kare mu ya ja min kwanaku". duka suka amsa da ameen kiran sallah magriba shi ya fitar da Malam yaje yayi sallah suma mik'ewa sukayi tare da d'auro alwala suka gabatar da sallah._

                *DEDICATED TO*
     *_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam💕_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts