New Post

Monday, 27 February 2017

BZATA PAGE 2

BAZATA
 
                By

©Rash Kardam

               2
    
Nan take taji wasu zafafan hawayen bakin ciki sun zomata, da sauri tayi maotar ta, ko kan marsal bata bi ba, motar ta shiga ta tada, da gudu ta bar gun, feenat da taga duk abunda ya faru sani halin kan warta yasa bata ce mata komai ba, amma gani irin gudun da take, yasa feenat tace Jiddah mai kk yi hakane, don wani ya bata miki rai kike son yin wasa da rayuwanki, me yasa kike da saurin daukan zafi akan al’amari, jiddah ko bata ce komai ba kuma bata rage gudun ba, ganin haka yasa ran feenat ya baci, tace tsaya jiddah ma tsawan baza ki rage gudun motar, to ki tsaya in fita miki a mota, ganin ran sis dinta ya baci yasa ta rage gudun, shiru sukayi, a haka suke tafiya, sannu a hankali, har suka iso Zamani Area, ko da suka shigo Area wani katon gida naga sun nufa ba laifi gidan na da kyau dai dai gargwado, horn tayi mai gadi ya bude, zuwa parking spaces tayi ta ajiye morta ta, gi fen na feenat, tana kashe motar ta fito da sauri tayi dakinta, kayan ta cire kafin ta shiga wanka, feenat ko tana shigowa sukayi karo da hajiyarsu, cikin girmama wa ta mata sannu da gida, ta’amsa cikin fara’ah, ya mai jikin ta amsa da sauki, tace Allah ya bata lfy ta amsa da Ameen, nan tace ina Jiddah kuma? tace ta shiga dakinta, tace ok, tayi kitchen, feenat ta wuce nata dakin, kwanciya tayi kan gado don hutawa.
Dr M Ghali kuwa ya bude jiddah da kura, ya nufi cikin T.H, ko da yashiga gurin ajiye motoci ya ajiye ta sa kafin ya dauko briefcase finsa ya fito, kallo daya zaka masa kasan yana cikin farin ciki, badan komai ba, sai don yasan ko ba komai ya tusa ma jiddah bakin ciki yau kuma ya tsokaneta gashi a bainar jama’ah, shima ya rama abunda ta masa, cikin kamala yake tafiya har ya isa office dinsa, mutane sai gaidasa sukeyi ya na amsa musu cikin sakin fuska, ko da ya shiga office din sa, ko ina a gyare tsab do Dr Ghali gwanin tsabta ne, gashi ma aboci son sanyi da kashi, kallo daya zaka masa ka gane cikaken dan boko ne da ya amsa sunansa, ya hadu iya haduwa, ko da ya zauna, nima na dan leko ta window office dinsa don in kara kalon wan nan guye din, ko.da na leka na zuba masa ido sosai, zan iya ce muku dogo ne, yana da dan kauri ba kuma wai zamuce mai kiba ba aa, dan da dai de, yana da dogon hanci wanda ya kai daf da karamin bakinsa, ko da yayi murmushi nan na hango fararen hakuransa, fari ne, fuskansa na dauke da annuri sosai, gaskiy Dr Ghali bana wasa bane, don irin saurayinda yan mata  suke rubunsa ne:mrgreen:. Wasu file ya jawo ya fara aikin gabansa, ganin haka yasa nima na kara wuta.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts