°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*15*
_Likita ya kallesa ya ce"ina taya ka murna matarka tana d'auke da juna biyu har na tsawon wata biyu sannan munaso ta rage yawan aiki sabida cikin da ke jikinta in ta matsa da aiki zai iya salwanta". Malam Ahmad bai san lokacin da yayi ```k'abbara``` ba yayi ```sujudu shukur``` Aisha da Malam jibrin suma murnnan sukayi._
_Malam ya kira 'yan Kano ya shaida musu suma sunyi murna sosai washe gari Maman Fatima ta biyo mota tazo don kula da d'iyarta. Duk wani d'awainiya Aisha keyi ma Fatima bata nuna gajiyawart don ko zuwan Inna Fatima bata dai na ba, ba ta barinta tayi aiki kwanansu hud'u aka sallamesu._
_koda suka dawo gida haka Aisha take zuwa ta taya Inna aiki in tagama nata hakan yayi ma Inna dad'i wanda yau suna zaune da Fatima ta kalleta ta ce"Fatima gaskya kinyi sa'ar makwabciya irin wannan zaman da kuke yi shi akeso makwabta su ringa yi amma sam wasu basu gane ba daga gulma sai gaba da nuna kai kafi wane arziki wanda hakan ba abu bane mai kyau". Goronta ta gutsira ta ci gaba da ce wa“inaso ki rik'eta hannu bibbiyu kuyi zaman lafiya da ita har *'Ya'Yan ku* da jikoki ai kinga yanda nake zama da makwabta na ko gidan Malam Ilu da muke tare kinsani wa zai ce bamu da dan gantaka a tsakanin mu sai in mun fad'a amma kinga zaman tare da makwabtaka mun dawo 'yan uwa"._
_Ta muskuta ta ci gaba da ce wa“kinga zaman lafiya kenan da bada hakkin makwabtaka don haka ina shawarta ki da ki k'ara kai mi gun kyautata mata da zaman lafiya da ita ```Allah yayi muku albarka"``` Fatima ta amsa da “ameen"._
_Inna da Malam da Aisha suna bama Fatima kulawa ta musamman duk rana in Malam ya fita abunda ya samo komin kashinsa zai kayo ya basu hak'uri yau ma kamar kulum ya d'an sayo musu hanta na d'ari biyar ya nufo gida._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY ‘N’ MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment