🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍧🍹
Page➖51~60
Tun daga k'ofan gida take ihun kiran sunan Umma!! ta shigo aguje sukaci karo da Umma tana nufo inda take." kai Khadija harkin tsorata ni wlhy,wane irin kirane wannan sai kace makauniya, ke kullum ba kya sanin kin girma kenan" dariya Candy ta fashe dashi "kai haba Umma daga kiran sunanki saiki tsorata haka,toh yau kiran naki ba fad'a na janyo aka biyo niba". Hmm" Umma tayi ajiyan zuciya,"toh Allah dai yasa hakan ne". Tsalle tayi ta d'ane cinyanta yau u
Ummah na gama primary d'ina kuma naci makaranta ta jeka ka dawo dake kabala costain,kinga kenan mafarkina zai zamo gaskia,dama kullum burina kenan,Banason naje makarantan kwana sabida bazan iya rabuwa dakeba Ummana".
"Uhumm Khadija yaranta ke damunki,kina yawan mantawa da akwai aure da mutu...." Da sauri ta rufe mata baki "ballema bazaki mutuba muna tare har karshen rayuwanmu". Tana kai wa nan ta nufi d'aki aguje dan cire uniform d'inta.
BAYAN SHEKARA UKKU!!
Su Candy an zamo manyan mata komai na budurci yasoma bayyana ajikinta. Cikin sauri tafito sanye da uniform d'inta tayi kyau sosai abinta."umma nizan wuce dan na kusa yin latti,"toh yar umma da fatan kin cinye d'umamen dana baki, Candy tad'an bata fuska "eyy na cinye umma",Sannan tafara tafiya umma tace "zo Khadija gad'an guntun naira ashirin ko zaki sai wani abu amakaranta". Ta karba tareda godiya "toh Allah kiyaye hanya" Tace "amin". sannan ta kama hanyan tafiya abinta. Taku take cikeda nutsuwa ahankali kamar bata son taka kasa. Rasheeda ta kalleni, " Ummielurv ammah kina kallon abunda nake kallo kuwa"? Juyawa nayi na kalleta "wlhy kuwa kinga yanda Candy take tafiya a nitse kamar da gaske". "Nidai ban yarda Candy zata iya canza halinta ba" inji Rash. Da haka dai harta shiga makaranta ta nufi ajinsu wato JS3A tana zuwa aka fara mata ihu. Tana d'aga musu hannu harta zo wajen zamanta. Ta kalli Rabi'at SK "ke matsamin awajen zamana, ai kinsan nice da lungu amma kullum saiki zauna min awaje". Yanda kuka san bada mutum take magana ba haka Rabee'at ta manna mata.haushi yasa ta kai mata mari tasss!!, kake ji karan marin, sai da wutan idanun Rabee suka d'auke na wucin gadi. Nan take kokawa ta kaure, babu wanda yayi kokarin rabasu dan kowa na tsoron kada fad'an yadawo kansa. D'ane ruwan cikin Rabee'at tayi ta rinka kai mata naushi aciki kamar tasamu jaka. Tun tana kokarin kare kanta harta kasa karfinta yakare.
Cikin sauri malamin ya shigo ajin ya daka musu tsaya. Kowa yasamu nutsuwa nan take Candy ta nutsu dan babu wanda take tsoro aduniya irin Malam Muh'd tsawa yadaka mata "u again Khadija, come here ma frnd". Da sauri ta matso kusa dashi jikinta na rawa kamar mazari dan tasan yau ubanta zata ci. Yasa aka d'aga Rabee tare da zaunar da ita akan kujeranta. Tana mai da nunfashi. Malam Muh'd yasa Candy up n down tun tanayi tana dariya harta fara kuka da majina. Malam Muh'd najin kukan har tsakar kanshi ammah babu yanda zaiyi, yana son ya hukunta'ta tukun tayi hankali. Tun tana kukan ahankali harta wage baki,ta soma ihu. Tsawa yadaka mata "will u keep quit?". Kai ranan Candy taci kuka ta gode Allah. Sanda yagama darasin sa na lissafi sannan yace taje ta zauna. Da kyar take tafiya zuwa wajen zamanta. Tsayawa yayi yana kallonta cikeda tausayawa. azuciyansa yasan hukuncin da yayi mata yayi tsauri da yawa. Ba yanda ya iya ne Candy bata ji sosai.
Da aka tashi kawayenta irinsu Mamu da Kausar suka fara bata hakuri. Kausar tace "kai ammah Malamin nan dan rai nin wayone,in ba dan iska ba me yasa zai baki irin wannan punishment d'in". Mamu tace "rashin imani mana".wlhy idan ba kici uban Rabee ba baki burgeniba, Shigiyar yarinya anan da kike kukan fa dariya take miki". Kausar tayi karaf tace "wlhy malam Muh'd sai mun"..." Candy ta daka mata tsawa "dan Allah ya isa tun d'azu Malam Muh'd ina ruwanku, ni daya wahalar banji haushi ba balle ku, Kowa taji buzzir dake d'uwawunta,munafukan banza, ina kuma dad'i kukaji dayake punishing d'ina" "mustew!!". ta karya kwana zuwa bin layin gidansu tana di gisa kafa.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment