New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA PAGE 1

HANNUNKA MAI SANDA...........

Rash Kardam

Sanah S Matazu

TSOKACI
Assalamu alaikum, wannan labari kirkirane daga ?hannun wa?anan bayin Allah guda biyu.Rubutunsa baya nufin cin fuska ko kaskanci ga wani ko wata,fa?akarwace muke fatan yi ta wannan hanya fatan wanda ya yi kwatankwaci da rayuwarsa ya yi mana afuwa ?an adam ajizine.

(1)
Cikin matsanancin gudu yaron ya shigo, tamkar sabuwar motar data sami sabis ya yi tirjiya yana numfarfashi. Sai ya saki dariya irin ta nuna zallar yarinta yana sauke idanunsa a kanta. Itama dariyar tayi zuciyarta
"Ummata San gidansu Abdoul muka je muka gani, ?ato dashi ya fi na gidansu Mukashif, Ummata mu yaushe za a siyo mana namu?".
Duk lokaci ?aya yake maganar ba tare da ya sauraraba, ta dubeshi tare da sakin murmushi. Ta ce,

"Najjash karka damu da sannu Ubangiji zai bu?a mana, kaima zaka ci naman sallah ka ji".
Kai ya ka?a ya juya, ya yi alamu da hannunsa,

"To Ummata babu abinda zan siyo miki....?".
Maganar ta katse sakammakon shigowar Dadynsa, kallo ?aya zakai masa ka suffantashi da cikakken namiji tun daga yanayin tafiyarsa.
Cikin murmushin da ya zamo ?abi'arta ta kodayaushe, ta mi?e ta kar?i ledar hannunsa ta na yi masa sannu da zuwa. Ransa fes yake amsawa, da saurin yaron ya ?aneshi yana fa?in,

"Daddyna sannu da zuwa".

"Yauwa yaron Daddynsa, _(hope)_ fatan kaje _(school)_makaranta?", Ya fa?a yana dafa kansa.
"Daddy na je, an yi karatu sosai da aka taso kuma naje kallon San gidansu abokina, Daddy mu yaushe zaka siyo mana namu?" Ya yi tsaye yana dogon tunani.
"Najjash!".
Muryar mahaifiyarsa ta kara?e kunnuwansa, da sauri ya guntse bakinsa. Mahaifinsa ya yi murmushi yana dubansa.

"Karka damu yarona zaka ci naman sallah".
Da murna ya fita yana tsale-tsalensa, mahaifinsa ya rakashi da ido ya dawo da hankalinsa kan matarsa su kai murmushi a lokaci ?aya.

                              **************

"Gaskiya Malam Mustapha bana sai godiyar ubangiji, saboda lamuran kara tsauri suke koda yaushe. Ni fa bana Lubabbatu ta ce na ha?ura da yin layya saboda matsin da muke ciki, sai dai tausayin Najjash nake bana so yaje kwa?ayi gidan makota".

Wanda aka kira da Malam Mustapha ya yi zambarwa yana dubansa ya ce,

"Taf! Wallahi Malam Ahmad bana koda ku?in bashi sai nayi layya, haka kawai aita hantarar yaranka musamman gidanmu da ya kasance gidan yawa".
Ya kalleshi cike da takaicin kalamansa, ji yake da zai iya daya kai masa duka ya huta.

Ya sassauta murya ya ce "Haba Malam Mamman bashi fa ka ce, ya zakai layya da bashi?".
Cikin kumfar baki ya ce "Bai hallata bane?".

Kai ya jinjina ya dubeshi ya ce "Haba Malam Mustapha ko a musulunci, layyah sunna ce maikarfi ga wanda ya sami iko mace ko namiji, ba wajibi bace saidai idan mutum ne ya ?orawa kansa, kamar ya yi alwashi cewa In ya samu wannan aikin ko

in ya ci jarabawannan ko in me?akin shi ta sauka lafiya sai ya yi layya, to da zarar abinda ya anbata ya auku layya ta zama wajibi akanshi saboda bakance ya yi. Amma batun kai layya bashi ma bai taso ba. Bance kar kayi layya bashi ba amma akwai matakan da ake bi wajan aikata hakan wanda na tabbatar baka ciki".
Cikin masifa ya tari hanzarinsa,

"bangane ba, kana nufin bana cikin matakan? Akan wane dalili?".
"Saboda yana hallata ga mutumin da yake da tabbas na ku?i ya ci bashi domin ya sayi dabbar da zai yi layya da ita, mu lura munce wanda yake da tabbas, kamar ma'aikacin da ya ke jiran albashi, ko

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts