°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*27*
_Kdeey suka taso a islamiya ta dawo gida sai da taci abinci ta taya Umma aiki sannan ta kwanta ta huta. A haka Kdeey taci weekend ranan Monday ta nufi makaranta suna zaune a hall har Malami yazi ya musu karatu yau bata ga Samy ba sai zuwa can Zeena tazo ta ce“Kdeey kina da labari Samy bata da lafiya kuwa sosai". Ido Kdeey ta zaro ta ce“dan Allah mai ya sameta". Sobu ta ce“ban sani ba amma ance jikin yayi tsanani yau nima zanje duba ta"._
_Kdeey suka tashi ta dawo gida haka ta gudanar da aikin ta na kullum bayan kwana uku Samy bata zo makaranta ba kuma Zeena ma bata zo ba. Hakan yasa taji azuciyarta ta kamata ta sanar ma Umma don ra nimi izinin zuwa duba ta don yanda take musu mutunci. Ko da ta dawo gida ta sanar da Umma ta ce“ayya gashi bana jin dad'i ai da tare zamuje amma bari Malam ya dawo sai ya kaki gobe tunda baku da makaranta"._
_Da yamma da Malam ya dawo Umma ta sanar masa ya ce“Allah ya kai mu gobe". Haka Kdeey tayi karatunta washe gari da safe wajajen k'arfe goma Malam yazo ya d'auki Kdeey sai da suka biya kasuwa suka sai mata kayan marmari tukun suka nufi gidanta a k'ofar gida Malam ya sauk'i Kdeey nan ya ciro d'ari biyu ya bata ya ce“gashi in kin gai data ki koma gida bazan sami dawowa d'aukarki ba". Godiya tayi tashiga ciki sai da ta gaida mai gadi kafin ta tambayesa gun Aunty Samy shi ya nuna mata hanyan shiga gidan da sallama tashiga._
_A falo ta sameta Samy tayi murna da ganin Kdeey tashi tayi ta kama hannuta suka nufi uwar d'aki suna gaisawa Samy ta kawo mata drinks cikin ikon Allah Kdeey na azumi Samy tayi shiru a zuciyarta ko cewa take “yau sai na karya wannan azumin". Sun d'an dad'e suna hira Kdeey ta ce“Aunty zan tafi tunda naga jikin da sauki ga Umma ba lafiya zanje nayi aiki". Samy ta ce“to ina zuwa". Wani d'aki ta shiga ta had'a ma Kdeey kayan kwaliya harda turmin atamfa a laida ta kawo mata Kdeey taki karba amma Samy ta nuna b'acin rai da cewa “bata yarda da ni bane". Hakan yasa Kdeey ta karb'a tayi godiya ta zo zata fita a d'akin da sauri Samy tasha gabanta ta ce“Kdeey wai har yanzu baki gane mai nake nufi bane?". Cikin rashin fahimta Kdeey ta ce“kamar yaya". Samy ta tako zuwa gabanta ta fiske hijab d'in Kdeey ta ce“na dad'e ina sha'awarki na biki ta hanyoyi da dama kinki ganewa shiyasa na had'a wannan target na rashin lafiyata dan yau na samu abunda nake kwad'ayi". Matsowa tayi gun Kdeey tars da rungumota nan duka fara kokawa._
*DEDICATED TO*
*KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN*
```Rash Kardam💕```
0 comments:
Post a Comment