New Post

Monday, 20 February 2017

DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI PG 26-30

🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
             DAI-DAI RUWA
              DAI-DAI GARI
   (DON'T EXPECT TOO MUCH 
                         IN
                       LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓

                         NA

©RASHIDA .A. KARDAM

Pg-26~30

Yau takama sallah duk wani Musulmi yana shirin zuwa idi, wanka Hameeda da Khairat da Saleema sukayi don zasu sallah masallacin Malam Idris, a qofar gidan su Khairat suka tsaya photo. Hameeda tana bud'e data saiga message sun fara shigowa, cikin sauri ta hau WhatsApp group d'in *Rash Kardam  Hausa Novels* ta fara karo dashi, da sauri ta shiga group d'in sakon barka da Sallah ta gani, sai Futha da ta d'aura photo wankan idin ta. Futha tayi kyau sosai, ana haka saiga Jiddah Ja'o ta faso nata kan kace me aka fara comments, ana ya ba kyan su. Hameeda tace"Khairat kin gani ko sun fara saka photo a group. Khairat da sauri ta bud'e data, ae ko nan ta fara karo da photo kala da iri, abun gwanin burgewa. Tace"kai kutsaya mudawo daga masallaci sai in mana editing d'in pics dinmu kafin mu d'aura. Karfe tara suka dawo daga masallaci.
Nan Khairat ta d'au wayanta ta gyara musu photo, ta tura ma kowa nata, nan suka fara d'aurawa a group d'in *MAMU HOME OF NOVELS* aka fara ma Hameeda comments kamar me, ana yaba kyan da tayi. Sai kusan 11:00am Aisha S Mazoji ta fara sako photo ta, ni kaina rash sai dana razana da irin wankan da tayi. Kamar Futha tana jiran ta fara sawa sai ta kara sako nata pics din abun sai ya dawo kamar gasa.
Sai ga su Beeba Lurv da k'awarta Sadeey, sun d'auro nasu abun sai wanda yagani, su Fulany Cediya ba'a barta abaya ba. Can sai ga Rabi'at da  Amrah Lurv sun faso nasu. Ni dai Rash na koma gefe na dawo yar kalo don abun na masuyi dagaske ne.
Ummin Yusrah tana hawa online taga pics sai da ta ciza yatsa tukun, tace"ae dole nanemo aron kaya inyi photo don kar abarni abaya. Tana haka wayarta tayi qara tana d'agawa taga suna Writer Haneefa Usman cikin han zari ta d'aga suna gaisa bayan sunyi hira ta mata barka da sallah, tacw"Ummin Yusrah muna zuwa ranan asabar ni da Zee Hrt zamuzo miki yawon sallah.
Sai da ta hadiyi wami miyau tukun tace"dan Allah to Allah ya kaimu.
"Amma naji dadi sai kunzo. Hira sukayi kafin ta kashe wayar. Wani gumine ya feso mata yau ina zata samu kayan da zata saka mai kyai da tsada.
Washe gari duk wacce zaka duba dp ta a whatsapp ta sako pics din wankan sallah, kuma sai ta tabbatar da tayi kyau kafin ta saka abun dai sai wanda ya gani. Group ko in banda gasan saka pics ba abunda ake sai labarin munje gurin hutawa kaza da kaza mun sha ice cream a kaza, ta din dai kenan.
Ummin Yusrah ko gari tashiga ta aro kaya zafafa kala uku tayi pics da kala biyu tasakasu a online, gaskiya tayi kyau kayan kuma sun amsheta, dayan ta bari sai randa su Haneefa zasuzo tasaka. Ranar asabar Haneefa ta kirata a waya tace"sis kiyi hakuri yau bazamu samu zuwa ba sai gobe da yamma,.
Ummin Yusrah tace"ba komai Allah ya kaimu gobe.
Ban garen su Hameeda ma an bata aron kaya tayi pic masu kyau ta daura a online, yanzu suna ta shirye-shiryen bikin Khairat ne.
Haneefa sunyi shigansu mai kyau suka nufi gidansu Ummin Yusra, ko da suka isa ta tsara musu abunci mai kyau da burgewa, suna zuwa ta gwada musu guri suka zauna,  ta koma daki ta karasa gayunta tayi kyau ba kadan ba. Ko suma bakinta sun yaba da kyan da tayi. Sai da tayi saving dinsu ta shiga daki kenan, sai da Asma'u da sallamanta, tundaga qifar daki, tace'ina Ummim Yusrah haka akeyi kinje kin karbo min kaya na, yau kwanana kenan.
"Bakinki basu zo bane, da bazaki mayar min kayana ba.
"Sai shegen qarya gida ba danga, gashi kin bar gidan mijiki akan karyan kaya da gayu.
Duk wannan magana sai a kunnensu Haneefa tayi, Ummim Yusrah da kunya ya lullubeta kar ta nutse kasa ya fito sai ido take ma Asma'u, amma ina bata ma san tanayi ba sai kara fadan magama takeyi.
Ganim su Haneefa sun gane yasa tace"kiyi hakuri zanzo na same ki a gida.
Asma'u tace"ni ina ruwana ki daiyi fada ma kanki kima gidan mijiki ya fi miki alheri da karyan da kikeyi tajuya ta fita.
Haneefa tace"haba Ummin Yusrah kin bam mamaki da hankalinki, zaki bata wayonki. Nan suka mata nasiha sosai. Zee hrt tace"gaskiya ki kira mijinki ki basa hakuri ku dai-daita.
Godiya ta musu suka tafi.
Washe gari Abban ta ya dawo daga Umra, kowa sai murna akeyi, yana zuwa yaga Ummin Yusrah hakan yasaka ta tambayi Mum dinta mai ya dawo da ita gida?.  Batare da bata lokaciba ta sanar masa komai. Waya ya dauko ya kira Abban Yusra yace"kana inane yanzu yace ina gida.
"Ok to kazo ina son ganinka yanzu nan. Yace"to Abba. Key motarsa ya dauka ya nufi gidan, ya samu Abba a falo ya gaida su. Abba ya tambayesa dalilin zuwan Ummin Yusra gida, bai boye masa komai ya sanar masa, cikin qunar rai yace"Hajiya kira min ita yanzu nan. Ta mike ta nufi dakin da Ummin Yusrah take. Tace"kizo Abban ki na kiranki. Damm! Sai da taji gabanta ya fadi kafin ta sauko daga kan gado ta nufi falo.

               *DEDICATED TO*
                     *MY FANS*
             *AS HAPPY SALLAH*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts