°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*10*
_Jiddah ta had'iyi miyau ta ci gaba da ce wa"Ki bar k'awar da take yawan jan ki zuwa gidan k'awayen ta wa 'yan da bakisan su ba kuma basu da Mazaje koma Suna da Mazajen , amma wa 'yan da Kki ka ga suna yawan kulewa cikin uwar d'aka ko Suke Yawan Tafawa suna rungumar juna , ko kwanciya kkan cinyar juna ko suke yawan cire tufafinsu agaban juna ko wanka tare. Ki kyamaci k'awar da bata da hira sai hirar Mace yar uwar ta. Ki guji k'awar da ba ta son yawan mu'amala da Maza amatsayin Samari ko Masoya , amma ta fi mu'amala da Mace 'Yar uwarta matuka ainun. Ki kauracewa k'awar da take da sha'awar kallon fina-finan batsa musamman irin na Mace da Mace (Lesbian). Ki fita sha'anin k'awar da ake yad'a jita-jitan tana Madigo (Lesbian). Ki rabu da k'awar da take mu'amala da k'awaye masu Madigo (Lesbian) koda ita ba ta yi domin kallon Mai yi ake yi mata kema haka za'a yi miki kallo.Ki ya kice k'awar da take zaman kanta agidan da ta kama take haya kuma Mata ke raruwa a gidanta. Ki fita sha'anin k'aawar da va ta jin kunyar cewa aga-aga , naa k'irji ko baya ko kasan marar juna. Ki hakura da k'awar da 'Yan Madigo ke burgeta koda ita ba ta yi. Ki kyamaci k'awar da take yawan yabon surorin jikinki irin k'irjinki da mararki da bayanki. Kiyi tir ki kuma guji tare da kyamatar k'awar da kuna gaduwa mai-makon tamiko miki hannu kuyi musabaha Slsai dai takai hannu ta daki bayanki (Mazaunanki) Ko ta d'an shafa k'irjinki. Idan siffar k'awarki ya burgeki sai kice "Masha Allahu", kinji sufofin masu Mad'igo sai ki zauna ki nutsu ki du ba". Kdeey ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"nagode Jiddah shi yasa kulum nake jin dad'in tarayyana da ke".(Iyaye yana da kyau musa ma Yaran mu ido musan da suwa suke kwance da tarayya don gudun jefa Yara cikin halaka ko mumunan hanya dan Allah mu kula), Kdeey ta ci gaba da cewa" Jiddah don ina matuk'ar k'aruwa da ke gashi Ya Al'ameen zai d'auke mana ke sai dai mu muku fatan Alkairi da zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba". Jiddah cike da jin dad'i ta amsa da "amin" da haka suka iso makarata suka shiga aji tare da sallama, zama sukayi suka fara bitan karatu kafin azo a musu k'arin karatu._
TUSHEN LABARI.....
*DEDICATED TO*
*_KDEET 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment