New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE- 71-75

🌲RASH KARDAM🌲🌲
               &
🎋SADEEY S ADAM🎋
            WITH
💖💖BEEBAH LUV💖💖

  🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
   *MA'YAUDARAH*
     🌺🌺🌺🌺🌺🌺

             _71-75_

Areef wulak'anci kala-kala yake ma Hameeda tana hakuri da shi in ya kuntata mata sai ta shiga d'aki tayi kukanta ta share hawaye, addu'ar ta kulun Allah ya karkato mata da hankalin mijinta gareta.

Bikin farouk ya kan-kama yau saura sati guda duk wani abunda ya dace sunyi Hajiyar Farouk da kanta ta ke gyara Rufaida.

   *6 DAYS LATER*

Yau juma'a dubban mutane suka shaida d'aurin auren Umar Farouk da Rufaida abun sai fatan Allah ya basu zaman lfya , abin sai son barka, basuyi wani shagalin k'arya ba Hajiya ce ta shirya musu walima da yamma aka gabatar.

Da dadare aka kai Amarya d'akinta, zuwa tara na dare abokai suka rako ango  suka musu nasiha gami da barkwanci daga nan suka musu sallama, muma kuma muka mik'e tare da basu guri don wannan lokacin sirrinsune...

                Aunty Farha kuwa tayi nadama sosai kuka taxo tana yiwa Rufaida kan ta yafe mata abinda tayi mata dan kuwa batayi mata rik'on kirki ba...
'yar Tata da take tak'ama da ita ta kwaso musu cikin shege ga mijin aunty Farha ya saketa ya kora su yace baxai iya zama dasu ba...
Ga yarinyar kullun laulayi take tana kwance ba lfya...
Tana kuka tana bawa Rufaida hkri kan ta taimakesu da ko dubu biyu ce suci abinci...
          Kuka sosai Rufaida take ta Shiga bedroom d'inta ta d'akko dubu goma ta bawa Aunty Farha...
Sannan tace zata xo ta dubasu idan yaya Farouq ya dawo...
Haka Aunty Farha ta tafi tana kuka tana regretting abinda ta aikata ma Rufaida,yanxu gata cikin daula su suna cikin tsumma...(Duniya budurwar wawa).

         ***********
Areef ne zaune a office wayarsa tayi k'ara yana dagawa yaga abokinsa Dr Saif ne ya ke kiransa. Ya d'aga tare da fadin" Allah ya kare mana likitan zamani". Dr Saif ya ce"kana inane Areef maza kazo yanzu kaga wani abun mamaki ina cikin asibiti". Kashe wayar yayi ba tare da ya ji abunda Areef zai ce ba.

Cikin fargaba Areef ya dauko key din motarsa ya nufi asibiti.

Office din Dr Saif ya nufa yana zuwa ya basa hannu suka gaisa.
  dr Saif  ya d'akko wani file ya turo gaban Areef ya ce "duba ka gani"

Cikin fargaba ya ce"na menene wannan file din?" Dr Saif ya ce" in ka duba zaka gani".

Da sauri Areef ya bude, rass!! K'irjinsa ya buga, ba komai ya gani ba illa takardan gwajin Teemah da cutar da take fama da ita har yayi worse sosai.

Hawaye ne ya ke zuba daga idonsa "tabbas Teema kinci amana ta ni inanan ina fama da soyayyarki ko matana naki kusantarta sabida sonki". Dr Saif ya ce"zo ka gani"

haka Areef ya rink'a binsa sukaje gun da ake taron k'anjamau nan yaga Teema ido-da-ido ana raba mudu gani kyauta. Take yaji kansa ya sara godiya yayi ma Dr Saif ya shiga mota kasa komawa office yayi ya nufi gida.

Yana zuwa ya samu Hameeda tana kuka ta kifa kanta akan kujera bata san da zuwan Areef ba. Jikinsa yayi sanyi sai yanzu ya tuna da ita marainiyace gashi Hajiyarsa ta basa amanarta. Jikinsa yayi sanyi a hankali ya taka yaje gun da ta kwanta ya sanya fuskarta akan nata shima sai yaji hawaye na sauka masa. Kamshin turarensa ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take yi sai tajishi a jikinta kaman a mafarki. a hankali ta daga fuskarta ganin hawaye a idonsa abun ya bata mamaki, Areef na ganin ta dago ya durkusa akan gwiwansa ya had'a hannayensa yana rokonta gafara nan tasaki kuka tafad'a jikinsa...
         tun daga lokacin suka shirya don bata da wasu gatan da ya wuce su. Rayuwa mai dadi su ka gina cike da ban sha'awa har yana mamakin irin kaunar da yakeyi ma Hameeda ba yaso yayi nisa da ita.

Teema a irin taron masu ciwon kanjamau da take zuwa wani zuwan da tayi suka had'u da Khaleed nan yaba ta hakuri nan suka dai-dai ta kansu akan zatayi Istibura'i sai ya aureta tun daga lokacin ta bar gari ta tafi gun yan uwan Ummata....

         ***********
FIVE YEARS LATER...

Hameeda na hango da yan 'ya'yanta sun fito cikin super market Areef na rike da key din motansa, Teema da Khaleed suma sun zo, nan suka gaisa Teema taga matar Areef ta hadu iya haduwa amma ina yanzu ya mata nisa gata matar wani fatan alkairi sukayi majuna su Areef suka shiga mota suka tafi.

*ALHAMDULILAH!*
ala kulli halin..
_komai yayi farko zaiyi k'arshe_

_Anan muka kawo k'arshen wannan littafin mai suna *MA'YAUDARA* kuskuren  ciki da mukayi Allah ya yafe mana_ Ameen👏

   *SADAUKARWA*

Mun sadaukar da wannan littafin ga 'Yan Mata  da Samarin Zamani...

  *WANNAN LITTAFIN TUKWICI NE GA*
_'Danmu Abin Alfaharin mu our luvly *AREEF* Allah ya raya mana Kai cikin tafarkin gskya tare da sunnahr manxon Allah (S.A.W)_

*Godiya ta musamman ga*
_dukkan group din *Online Hausa Writers* Allah ya barmu tare.

          *TSOKACI*

Yan Mata da Matasan zamani kun mai da yaudara ya dawo abin ado a gare ku kunga kadan daga illan masu yaudara da kwadayin abun hannu saurayi ya kai Teema ga fad'awa halaka da nadama mai tarin yawa Allah ya kyauta yasa mu gane gsky Ameen.

Urs 🎋S 💖B 🌲R..
               
Munai muku fatan alkhairi....
Luv u alot swi[truncated by WhatsApp]

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts