New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI.... PAGE 28-29

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(AUGUST 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*28*

_Dambe sukayi sosai har ta yaga ma Kdeey Samy tafi k'arfin Kdeey ganin zata iya nasara akan ta tarasa wani irin abu zata mata can ta hango wani abu karami kaman k'arfe kafa tasa ta jayo ta shammace ta kwad'a mata a gwiwan k'afa take Samy ta fad'i tana nishi._
_Cikin hakki Kdeey ta ce"tabbas nayi kuskure yarda dake a rayuwata Alhamdulilah! Allah ta tsareni daga kaidin ki da sharri ki kisani kullum iyayena suna min addu'a kuma nayi imani addu'a su bai tafi banza ba don gashi Allah ya kare ni daga sharri ki nagode ma Allah". Zaninta ta gyara d'aurawa ta d'auki d'ankwalinta ta d'aura ta ce“Allah ne kad'ai yasan yawan mutane da kuka b'atar shin wai baki tsoron Allah ne ko kinsan irin masifan dake cikin mad'igo(lesbian) to in baki sani ba kisani yanzu don na sauke nauyin da ke kai na". Tsayiarta ta gyara don tasan tayi illa ma Samy a kafa bazata iya mata komai ba._
_Taci gaba da cewa"Madigo haramun ne a cikin addinin musulunci. Malamai sun sanya shi daga cikin manya-manyan zunubai._ _(Duba Almausu’atul Fikihiyyatul Kuwaitiyya da Almugniy na Ibnu kudama)._ _Musulunci na yin nuni da azabar da aka yiwa al'ummar Annabi Lud kamar yadda ya zo a Al-qur'ani haka ma kiristoci na nuni da zabar da aka yiwa al'ummar Sodom da Gomara(al'ummar Lud)_ _kamar yadda yake a littafi mai tsarki ko bible dangane da amincewarsu da dokar hana luadi da madigo._ _ki sani mad'igo fita ne daga dabi’ar da Allah Ya halicci mace a kanta, ta jin dadi da da namiji ba mace ’yar uwarta ba._ _Cikin Mad'igo akwai rashin kunya da fitsara, alhali Manzon Allah (S.A.W)yana cewa:_ _“Kunya alheri ce gaba dayanta.”_ _A wata riwaya:_ _“Kunya ba ta kawo komai sai alheri.”_```Buhari ne ya
rawaito.``` _In budurwa ce tana iya rasa budurcinta ta hanyar mad'igo, wanda hakan ba karamin tozarta ba ne ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure._

                 *DEDICATED TO*
     *KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN*

```Rash Kardam💕```

°•°•° *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(AUGUST 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*29*

_Kdeey ta ci gaba da cewa“kuma karki manta duk mai mad'igo takan rayu a cikin kuncin zuciya da k'unarta sabida Allah zai d'ebe mata natsuwa a tare da ita, ya kuma maye gurbin da kunci da damuwa. Sannan mad'igo yakan hana 'Ya mace zaman aure domin dukwacce ta saba da shi, to zai wuya ta dai na yikuma hakan shi zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta sai ta rik'a fita tana yi. Har lokacin da Allah zai toni asirinta mijinta yasake sakin wulakanci ko kuma ta nimi saki da kanta taje taci gaba da mad'igonta. Kisani mad'igo dabbaci ne ko ince dabba ma tafi 'Yar mad'igo. Kinan kina cin *Amanar* ```Allah``` don cikin mad'igo akwai cin Amanar *Allah* sabida an aikata abinda ya hana kuma hakan cin *Amanar* iyaye ne"._
_Kdeey ta share hawayen da ya zubo mata ta ci gaba da cewa“Shawaran da zan baki don ki gyara ki koma ga Allah ki sani shi Allah ```GAFURUN ne kuma RAHEEMUN``` hanya d'aya da zaki bi ki tsira daga wannan halaka shine kiyi kyakkyawar ikilasi da niyyar tuba ba tuban muzuru ba._ _Ki dage da yin karatun Qur'ani da tsarkin zuciya. Idan shaiɗan ya kwaɗaita maki yin lez, ki kawo Allah a ranki ki kuma  ji tsoronsa a baki da zuci da kuma a aikace. Ki dai na kallon fina-finan batsa, don kallonshi ma yana sanya ki k'ara faɗawa hatsarin yin mad'igo. Domin kamfanin shirya fina-finan batsa sun fi kowanne kamfani samun kud'i". Allah ne yasan iya bibiyata da kike yi Allah ne ya kare ni daga sharri ki yabani nasara akanki Alhamdulilah!.  Ke kuma Dan Allah ina rok'onki badan ni ba kiji tsoron Allah ki dai na don bansan yawan mutanen da kika b'atar ba ndai ina k'ara kiranki da kiji tsoron Allah. Kuma k'awance ni da ke daga yau ta k'are don tabbas wataran zaki iya jana nikuma ina tsoron sab'a wa Allah sai anjima"._

                *DEDICATED TO*
       *KDEEY ‘N' MRS AL'AMEEN*

```Rash Kardam💕```

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts