🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
DAI-DAI RUWA
DAI-DAI GARI
(DON'T EXPECT TOO MUCH
IN
LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
NA
©RASHIDA .A. KARDAM
Pg-21~25
Hakan yasanya Hameeda ta d'au k'arya, ta d'aura ma kanta. Ta manta da cewa yatsun hannun mu ba dai-dai suke ba, kuma komai zakayi sai ka dubi kanka, karka hango na sama da kai, *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI*. Wannan shine taqaitacen tarihin Hameedah, bari mu dawo labarin.
Ummin Yusrah ce ke ta shiri ta fito daga wanka, simple make-up tayi, sabida Ramadan ne bata bata fuskanta da wani gayu ba. Abunka da k'yak'yawar mace, duk da simple make-up tayi, bak'aramin kyau tayi ba. Atamfarta tasaka mai kalan green da yellow da ratsin baki aciki, tayi kyau sosai, ta kalmi ta d'auko flat shoe yello sai hijab yello, ta saka takalmi da hijab yellow ne, sabida adon atamfar yellow ba yawa sosai aciki, kuma matuk'ar amsan jikinta. Falo ta fito ta samu Mum d'inta ta gaidata da gida, kafin tace"Mum zan danje un guwa gidan kawata Munay don tun jiya nace mata zanje ban samu zuwa ba. Hajiya saida ta kalleta tsaf tace"Yanzu Baban Yusra yasan zaki fita?.
"Kanta ta sunkuyar k'asa tace"eh ya sani sai da mukayi waya na fad'amasa ae.
"To shikenan adawo lafiya Allah ya kare.
Ta amsa ma Mum da "Ameen".
Tana fitowa harabar gidansu Bala driver ta kira tace"kazo ka kaini Nasarawa Jahun.
Ya taso da sauri ya amsa mata da"to Hajiya". Kasancewar motocin duk a wanke suke a goge, daukowa yayi suka nufi Nasarawa Jahun.
Sai da sukayi tafiya mai d'an nisa kafin suka isa Nasara jahun, yana ajiyeta tace"ka koma gida don ba yanzu zan dawo ba.
"Kuma ina tashi dawowa ko Napep zan shiga in dawo. Bala driver yayi corner ya juya, ita kuma da sallamarta ta shiga gidan Munay.
Munay da ke yan fere dankalinta da murna ta amsa mata, ajiye firan tayi suka shiga d'aki don su gaisa. Sai da suka zauna dukansu, sanan suka gaisa nan suka fara hira kenan saiga mijin Munay da yar ledansa na kayan sallah. Ko da ya shigo saida suka gaisa da Ummin Yusrah, kafin yashiga daki, Munay ta bishi daki ta masa sannu da zuwa, yace"ga kayan sallah ki nan sai kiyi hak'uri bana ba kudi ba lalle bane asamu mai tsada kamar kulum. Wani lallausar murmushi tasaki tace"haba maigidana na kaina, abin sona abun alfaharina, sanyin idaniyata, farin cikina abin tin kahona.
"Wallahi tun kan inga kayan naji sun burgeni kuma sun fimin na kowani shekara kyau da kayatarwa.
"Din haka dole un shirya maka kwaliyan burgewa a sallah nan.
Har cikin ransa yaji dadin kalamanta, albarka ya sanya mata.
kayan kafin ya fita waje yayi sallama ma Ummin Yusrah, Munay kuma ta rakosa ya zare N500 yace"gashi ki bata tayi kud'in Napep. Munay tace"ta gode Allah ya kara bud'i.
"Sai kadawo Allah ya kare.
Cike da farin ciki ta dawo cikin gida tace"afuwan Ummin Yusrah na barki ke kadai ko?.
Ummin Yusrah tace"ba komai.
Munay tashiga d'aki ta dauko ledan tace"k'awa ga kayan Sallah na fa yanzu ya kawo min. Cike da d'oki Ummin Yusrah ta fara zarowa tana d'agoea ta ga zani gana England yan N4500 da takalmi yan N1500 sai gyale d'aya. Tace"Munay akan yan wannan kayan kike murna cab.
Munay cikin rashin fahimta tace"ban gane mai kike nufi ba?.
" ae naga kayan sunyi kyau sosai, miye aibun su?.
"Uhmmm lalle kam yanzu da wannan kayan zakiyi photo kisaka a group akan wankan sallah. Kinaso a raina mu na ko?.
Munay tace"ban gane a raina mu ba?.
Nan Ummin Yusrah ta bata labarin yanda sukayi da Abban Yusrah.
Munay tace"Ummin Yusrah kina da hankali kuwa
Munay tace"Haba Ummin Yusrah akan kayan Sallah har kiyi mijinki ya sakeki, amma wallahi kin ban mamaki k'warai da gaske.
Ummin Yusrah tace"mamaki fa kika ce ae hakan shine dai-dai.
Munay tayita nusar da ita amma fir taki ta gane daga k'arshe ma suka rabu baram-baram.
A b'an garen su Khairat kuwa an kawo kayan aurenta, nagani na fad'a duk inda kazaga a unguwan maganan lefenta akeyi a ko ina na unguwansu. Babanta yasaka auren ana sallah da sati d'aya.
Hameeda kuwa Haisam ya kawo mata kayan Sallah sa na dai-dai talaka, a gun ta watsa masa ba irin kalan wulakanci da bata masa ba. Da har zata tafi ta barkayan gani zata bar banza kuma dole aurensu ba fashi, yasa ta dawo ta d'auka tace"gwamma in rabaka da shi ko kyauta nayi, tayi tsaki ta tafi abunta.
Duk wasu masu shiri sunyi shiri yau take jaji beri, masu kitso nayi masu lalle nayi, abun gwanin burgewa, nima Rash ina layin kitso da lalle don gayun sallah.
*DEDICATED TO*
*MY FANZ*
*AS HAPPY SALLAH*
0 comments:
Post a Comment