New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOMKI PAGE 131-140

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧

_Rash Kardam_
           _Ummieluff_

```Page➖131-140```

Jikin Umma kara tsanani yake yi, Candy duk ta rame kullum cikin kuka ta ke gashi ba yan kuɗi a hannunta. Ga shi yanzu Abdoul ya fita harkanta duk da yanzu bata kansa take ba, ta jinyan Umminta take. Wani sa'in da kyar ta ke samun aikatau tayi kafin ta samu kuɗin magani, rayuwansu ta dawo abar tausayi ga al'umma. Boko ta bar zuwa sai su Mamu da Kausar da ke ɗan leko ta. In sunzo suna bata ɗan kuɗaɗen da suka tara wani sa'in har kukan murna take yi don tabbas su Kausar kawaye ne  nagari masu halin kirki.

               ****

Malam Muh'd duniya ta masa kunci tun randa ya samu labarin Candy tayi saurayi ranan har kuka sai da yayi *MAFARKINSA*

tana soyayya da wani tasan mai ya kawo sa teaching makarantansu? Anya tasan ko shi waye? Idan kuɗi ta ke so yana da miloyin da zai sayi soyayyarta harma yayi yawa.

        “Candy sabi da na kasance *TARE DA KE* na bar gata na da yan uwana nazo gare ki. Bana iya bacci sai da photon ki a idona, zuciyata na cike da kaunarki,kaunarki tamkar makullin rayuwata ce".

Ya share wasu zafafan hawaye tare da furzar da iska mai zafi.

     “Ina sonki Candy naga kina tsananin son Abdoul-wahab bazan rabaki da abunda kike soba, ya zama dole na yi nesa da ke naje naga iyaye na ko zan sami sassaucin suyan da zuciyata ke min".

Mi kewa yayi ya fara har-haɗa kayansa ya bar wanda zai saka kaɗai a waje. Wanka ya shiga bai daɗe ba ya fito sauri-sauri ya gyara jikinsa ya sanya kaya tare da fesa turaruka masu sanyin kamshi. Cikin gidan ya shiga ya musu sallama, ɗakinsa ya dawo ya ɗauki jakarsa ya rataya ɗaya a kafaɗa, ɗaya hannun kuma wani katon photon Candy ne wanda aka zana masa ya zuge trolley ɗinsa ya saka a ciki. A hankali ya janyo trolley ɗin tare da manna bakar glass a fuskansa. Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidansu Candy ya ɗan ɓuya a lungu har yazo yaga wucewarta. A hankali ya rinka binta ba tare da ta sani ba yana ɗaukarta photo. Wayar sa ce ta soma ruri cikin hanzari ya ɗaga bayan sun gaisa daga ɗaya bangaren aka sanar masa saura minti talatin jirginsu ya tashi. Cikin sauri ya katse wayar yana wai-wayen Candy har ya tsari ɗan acaɓa sai Airport yana zuwa bai daɗe ba aka masa abunda ya dace jirginsu ya ɗaga zuwa Saudia. Ganin jirgin ya tashi na juyo da sauri na kalli Ummieluff.

       “Wai nikam waye ne wannan Malam Muh'd ɗin? Iyayensan suna inane da zama? Naji yace zai sai soyayarta  da miliyoyin kuɗaɗe?. Kai na ya kulle ina da tambayoyin da nake niman amsa".

Ummieluff ta sauke ajiyar zuciya tare da wani gwauron numfashi.

    “Yanzu kawai jirgin online network zamu hau mu bisa inaga hakan zai fi mana zaurin cimmasa don mu samu labarin da muke son ji".

Murmushi nayi mata wanda sai da kumatu na ya lotsa.

   “Yauwa kawalli haka za'ayi". Na faɗa mata.

Tsalle mai kyau mukayi sai cikin jirgi Online Network take ya lula da mu cikin gajimare gudu yake yi salansar jirgin tana bulbula hayaki...lol. tamkar murhum da aka garkama motar icce bata ci. Ba tare da ɓata lokaci ba muka hango jirginsu M Muh'd.

Munyi tafiya mai nisa kafin muka iso jiddah nan jirgin mu ya sauka.

Muh'd na sauka mota ya shiga zuwa cikin garin Makka nan mahaifinsa ke da zama. Tafiya mai nisa sosai sukayi wanda sai da suka kwana a hanya.

Notice kunsan jirgi bata sauka a Makka sai Jiddah. Kar wasu suga munsa hakan wa'yanda basu san da hakan ba.

Yana sauka ya sake hawa taxe zuwa wani katafaren unguwa. Dai-dai wani kofar gida mai kyau na gani na fada suka tsaya. Ya ciro kudi ya basa bai tsaya jiran sauran ba ya nufi gate ɗin ya kwan-kwasa mai gadi ya leko ganin Adnan ne ya washe bakin da sauri ya buɗe masa ya shigo.

   “Ranka shi daɗe kai ne haka ko labarin zuwanka banji ba a gun Hajiya".

     Murmushi Muh'd yayi mai bayyana kyansa.

  “Eh nine suma basu san da zuwana ba sai yanzu inna shiga ciki".

Mai gadi ya masa sannu da zuwa. Muh'd ya nufi cikin gida.

Hajiya Fatima da suke falo da Abban Muh'd da sauri suka mike cikin farin ciki suke tambayar lafiyansa.

“Abbah da Ummie  lafiyata lau haka mutanen 9ja ma duk kalau suke sunce a gaida ku". Cewar Muh'd.

“Mashaa Allah". Su Abba suka faɗa a tare.
Bayan ya huta ya ci abinci nan sukayi hiran yaushe gamo har kusan shaɗayan dare kafin yaje ɗakinsa ya kwanta.

Da safe Ummie da kanta ta haɗa masa breakfast mai lafiya bayan sun karya suka taɓa hira nan take tambayarsa Candy da ke yawan bata labarinta. Cikin dabara ya kawar da zancen suka ci gaba da wani hiran.

*WAYE MUH'D ADNAN(ADEEL)*

Muh'd Adnan haifafen Saudia ne amma Mahaifiyarsa yar Gombe ce sai Mahaifinsa Alhaji Aliyu yahya haihaffen ɗan Mai dugurine karatu ne ya kawosa kasa mai tsarki. Wanda a zuwan Fatima(Ummieluff) Ummurah suka haɗu har suka fara soyayya cikin ikon Allah akayi aure. Daga nan ta dawo Madina da zama. Sun daɗe da Aure kafin Allah ya azurtasu da ɗa guda ɗaya tilo wato Muh'd Adnan suna kiransa da *Adeel.* Adeel ya taso cikin gata har Allah yayi mahaifinsa ya kammala Masters ɗinsa ya fara ɗan aiki a Madina. Bayan wasu shekaru kasancewar ya rike gaskiya da Amana. Nan Allah ya haɗashi da wani balarabe mai suna Alhashim. Alhashim ya kasance mai kuɗi ne sosai yana da rijiyan man fetur. Ganin gaskiyan  Alh Aliyu yahya yasa ya ɗaukosa ya ɗaurasa a harkan ba da daɗewa ba shima ya bun kasa ya haɓaka. Ganin hakan yazo gida 9ja ya buɗe gidan mai da campany yin shinkafa da sugar. Bayan wasu shekaru lokacin Adeel ya girma suka zo 9ja ganin yan uwa. Nanne suka ga campany ba wani ci gaba hakan yasa Adeel yace zai zauna tunda ya kammala karatunsa. Wannan shine dalilin zuwansa 9ja da zama.

Bayan wasu watanni ya ga komai na campany ya zama dai-dai hakan yaji yana da sha'awar koyarwa hakan yasa yayi interview na teaching yaci bayan nan ya fara koyarwa yana kula da Campany su. Ananne ya ga Candy har ya fara sonta. Kuma wannan shine dalilin da yasa bai koma Saudi da wuri ba sai da Candy ta fara soyayya da Mr Smile. Dalilin da yasa yaji kasan Nigeria ta gun duresa ya shirya barin garin ba shiri. Har ya taho kasar da iyayensa suke wannan shine tarihinsa.

                *******

Jikin Ummin Candy kara tsanani yake yi wanda hakan yasaka suka je Asibiti. Gado a ka basu likitoti sunyi caa akan Ummi amma abu ya faskara nan suka sa mata drip ganin Candy tana cikin wani hali yasa basu sanar mata komai ba. Da kyar suka barta ta shiga gun Umminta. Ummi ta kama Hannun Candy ta rike cikin nishi da muryan marasa lafiya wanda jiki yayi tsanani ta soma cewa.

“Khadijatu ki buɗe kunnuwar ki kiji mai zance miki".  Tari ta ɗanyi kafin ta dafe gefen kirjinta ta lumshe ido ta buɗe.
“Khadija ina son ki kasance mai hakuri da juriya a rayuwanki. Kar kiyi wasa da ibada duk rintsi-duk-wuya ki rike amana gaskiya da zumunci. Karki manta da tarbiyan da muka baki koda bayan raina ki kasance mai yi min addu'a da mahaifinki da sauran musulmai. Ki kasance mai taimako a duk inda kika ga mai neman hakan matsawan bai saɓa wa addini ba. Dan Allah kar ki kina niman faɗa ki rinka hakuri duk inda kika samu kanki. Aaah! aaah!! Tayi tari ta cije leɓenta sabida zafin da take akirjinta.

Candy ko in banda kuka ba abinda take yi cikin zuciyarta ko sai furta “ina! Umma zaki tashi bazaki mutu ba".

“Khadija ni kam ba tashi zanyi ba tawa ta kare ki kara hakuri a duk inda kika sami kanki. Kasancewar ba wanda zaki zauna a gunsa in kin samu miji kiyi aure. Ko zaki yi karatu sai bayan kinyi aure don gidan mijikin shine mutunciki. Martaban mace shine gidan mijinta..dan Allah khadija ki daina zuwa gidan *ZAMAN MAKOKI*Wanda nasan ya riga yazame miki jika ayanzu". Cikin sauri candy ta suma girgiza mata kai" wallahi ummuh nadaina daga yau" murmusawa ummah tayi sannan ahankali ta furta "Allah miki albarka" Nasiha sosai tayi ma Candy.

Candy in banda kuka ba abinda take yi.

Ummi ta fara wani irin tari tana kakari tana salati idon ta suka soma kafewa a sama.

Candy ganin haka ta kurma kara tana kiran “Ummi! Ummina!! dan Allah kar ki tafi ki barni in kin tafi wa zan zauna dashi. Ko kin manta ke ce gatana,da ke kaɗai nake gani nayi murmushi banda kowa sai Allah sai ke. Ummi karki tafi ki barni ina zan saka kaina? Ina zan zauna? Abba ya tafi kema so kike ki bisa? Zaki bar Candyn ki mai kaunarki. Ummi in nice na dai na rashin ji zan zauna da kowa lafiya zan na duk abunda kike so".

Wani irin kuka Candy take yi mai tsuma zuciya tana jijjiga Umma. Likitoci ne suka shigo suka rike ta tana fisgewa tana kiran Ummanta.

Duk fuskata ya jike da hawayen tausayi na ɗago karaf naga Ummieluff itama kukan take yi abun gwanin ban tausayi. Rayuwa kenan.

         *```TAGWAYEN MARUBUTA```*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts