New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MAI SANDA PAGE 2




Rash Kardam: HANNUNKA MAI SANDA.........
Sanah S Matazu

Rash Kardam
(2)

"Gaskiya Maryam ni bana ba zanje gidan Aunty Naja taya aikin sallah ba,saboda na lura babu mai danshi-danshi a gidan".
Cewar yar siririyar cikinsu kenan,doguwar ta kalleta kallon uku ahu ta watsar.
"Gaskiya Murjanatu kina bani mamaki,itafa duniyar nan da kike dubanta ba aljannah bace kinbi ki ?orawa kanki burin tsiya waima mu gidanmu ana layya ne da zaki damemu komai basai da haliba.Ina laifin Aunty Naja ma da babu dangin iya ba na Baba darajar makotaka ana ra?aki shi ne kike kokarin ci mata dunduniya gaskiya ?an Adam butulu ne".
Lukutar ta wurgawa wadda aka kira da Murjanatu harara kamar bazata tanka ba,ta ciza saita furzar.
"Kyaleta Yaya Maryam ai ita duniya tafi bagaruwa jima,muna zaune zakiji zuwan da dawowar.Bandama ke da kika adabi zuciyarki da kwalama menene na wani zuwa taya aikin layya?".
Dai-dai lokacin suka shiga gida, _(still)_har zuwa lokacin mitar halin autar tasu suke yi.Mahaifiyarsu ta amsa musu da kulawa tana dubansu duba irin na tuhuma.
Maryam ta sadda kanta kasa ta wuce ?akinsu,tana jin hayyaniyya kasa-kasa ?akin mahaifiyarsu Murjanatu.Bata gasgataba saida ta hango fitowar mahaifinsu ransa a matukar ?ace yana huci tamkar sa,muryarta ta yi musu bazata cikin numfarfashi.
"Walahi baka isaba shekara uku kenan rabon da kai mana layya,wannan wulakanci har ina?Kullum yaronmu suna kwalama gidan makota kamshi na sirnane mane hanci nida yara muna ?aga kai tamkar wasu jikokin tamak'ula mayya!".�
Ta karashe da sauti mai hargowa.Shiru yayi ya kasa cewa komai,zuciyarsa na tukuki yana ji kamar ya ha?iyeta ya huta ya numfasa yana duban yadda Maryam da Sa'adatu suka wuce ?aki suna ?acin rai bisa alamu sun shaka daga lamarin Auntyn tasu amma Murjanatu da Mubashar da Muntari tsuru suna kallonsa da ido tamkar an jijjiga ?era a buta tsawa ya yi musu.Da gudu sukai ?aki banda Maryam dake kunkuni ya yi kwafa ya kaimata mangari.
Duk abinda suke sai yanzu Mama ta tanka tana murnushi,wanda ya bayyana ainihin nutsuwarta.Ta dubeta ta ce,

� "haba Auntyn yara,keda zaki tsawatar ke akejin ?hakan a bakinki tamkar bai kamata ba itafa duniya kamun kifi ce kuma koba komai da gudu da arziki gara shekara da tsiya".....
Tunkafin ta karasa ta tare ta,

"Aisha duk fa wata fuffuka da kike kallonki nake,babu tarangahomar da bazan iya ?auka ba saukin abu duk dodo ?aya mukewa tsafi".
Ta yunkura zata yi magana,saita kanne kome ta tuna sai ta yi murmushi ta ce,

"na fahimci hakuri ma zugane,banda ke ai gwanin doki shi ne wanda yake kansa".
"Ahaf! Ai kowa ne tsuntsu kukan gidansu yake,a dai juri zuwa rafi".
Har Mama tasa kai ?akinta ta leko cike da ginshira ta ce,

"zakaranka dai rakuminka".
Ka?a kai ta yi ta koma,tana shiga ta riski Maryam tana kuka tasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya tasan Maryam sarai wajan raunin tsiya musamman a ta?o Abbansu.Murmushi ta yi tare da janta jikinta cikin murya a raunaniya ta ce,

"inason tunasar daku komai lokacine,mahaifinku mutum ne mai zuciyar nema nasan da yana dashi da gazai kiyin layya ba banaso ku dubi ?abi'ar Maryam da mahaifiyarta ku zamo abin koyi da ita.Itama bance ku kyamaceta ba kui mata fatan shiriya ku dinga janta a jiki kuna yi mata kasiha,mafi kyautuwar mu'amala shi ne aboki nagari ita kuwa yar uwarku ce".
"Walahi Mamanmu ko yanzu maganar muke muka shigo,amma bata ji duk laifin Auntynsu ne duk shekara sai anyi wannan bala'in a cikin gidan nan ?haba Mama shiyasa walahi koyaya yini da Malami yafi shekara da jahili".
Dokemata baki Mama ta yi tana fa?ar,

"ashe nima wata rana zaki yimin?

Sa'adatu yaushe kika zama mara kunya haka?".
"Kiyi hakuri Mamanmu".
Mikewa ta yi da sauri ta yi waje jin kururuwar Auntynsu,aikuwa tana zuw

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts