New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 16-20

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍧🍹

                    *NA*

_Ummieeluff_😘
            &
_Rash kardam_

Page
16~20

Tun hajiya na koranta harta gaji ta daina,data gama baccin sai tasai sabulun naira d'ari tukun candy ta nufi gida. Wata rana duk cinikin datayi tana kashewa wajen cin candy da awara,awajen kawayenta masu rashin ji kamar ita. Tana shiga ta tarda mamanta xaune tanacin gyad'a mai gishiri,da sauri tanufi inda take har tana tuntu'be "laah mamah aina kika siyo gyad'a"?  Mamah ta 'bata rai kamar bada ita takeba. "ni matsalana dake kwad'ayi khadiya baki isa kiga mutum nacin abuba,shikenan kin rinka tambayansa kenan aina yasamu? Toh satowa nayi" nan take candy ta 'bata rai kamar ta had'iyi kota. "toh mamah danna tambayeki inda kika samu shine xaki rinka min fad'a" nina lura kwanan nan ma ba sona kikeba,kullum sai kinmin fad'a, nan take shagwa'ba ya motsa ta rinka matsan hawaye tana bubbuga kafa.

Mamah tayi murmushi tana kallon candy dake ta faman shagwa'ba wani kaunarta na sake shiga zuciyanta..candy akwai rashin ji ammah kullum addu'anta shine Allah ya shirya mata yarinya. Janyo hannunta tayi" zonan yar mamanta,idan banso ki ba inso waye? Ke kad'ai Allah ya mallakamin danake gani inajin dad'i,fad'an nan danake miki bawai kiyayya bace kwad'ayinki yanada yawa,ke kenan daga kinga abu ahannun mutum saikin roka. Wannan hali naki Allah dai yasa kada ki girma dashi..Allah ya yaye miki irin wannan kwad'ayi". Sannan ta d'auko gyad'ar kulli d'aya ta bata nan take ta hau murna tana cin gyadarta,tana d'an raira waka dad'in gyadar na ratsata. Shiru mamah tayi tana kallonta Allah sarki mutuwa mai raba tsakanin masoya,tasan da mahaifinta nada rai da khadija tagama jin dad'inta sabida shi mutum ne mai zafin nema. Gashi babu yan uwansu akusa balle su taimaka musu,basuda kowa su biyun nan suke rayuwansu. Cikeda son juna.

Tana gama cin gyad'ar ta mike ta fice abinda zuwa gidan su Aneesah abokiyar fad'anta..tana shiga ta'tarda Anush nacin shinkafa da manja habawa da sauri ta nufi inda take ko sallamah babu tasaka hannu har Anush ta tsorata..haka sukayita wawa akan abincin har candy ta cinye tafara zare idanu "akwai wani ne"? Haushi yasa Anush wanka mata mari suka kwashi dambe suna zage'zage.


*TAGWAYEN MARUBUTA*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts