🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧
_Rash Kardam_
_Ummieluff_
*_Last page_*
Ni Ahmad Alkali hai fafen ɗan garin Sokoto ne zamane ya kawo ni nan Kaduna. Amina(sunan Ummin Candy) duk randa ki ka ga wannan sakon ku tafi garin Sakoto unguwan G.R.A gidan Malam Alkali. Sananne mutum ne in kinje ki gabatar da kanki da abunda ke cikinki ki gwada masa wannan photo zai gane ku. Ni kam tawa ta kare ki rike min amanar abunda ke cikinki ki kula da ita ki bata tarbiya tamkar ina raye daga mijinki Ahmad Alkali. Sai mun hadu a darusalam.
Hawaye da ya wanke wa Candy fuska na farin cikin sanin danginta bata san lokacin da ta ruga da gudu ta shiga gidan su Munay tana kiran.
“Abba! Abba!! Abba!!!".
Tana haki ta iso gabansa ta mika masa ta kardan yana gama karanta wa ya saki murmushi tare da fadin
“Allahu Akbar! Allah kenan mai yanda yaso wato bai so Amina taga dangin mijinta ba sai yarta kuma bayan ranta. Tabbas ba sanya yanzu zan sanar da iyayen Adeel a sati nanna zamu tafi".
Waya ya kira ya sanar musu da komai.
Cikin murna suka ce a jibi zasu wuce in Allah ya yarda.
Bayan kwana biyu Abban Adeel da kansa ya sama musu motoci biyu daya shiga Ummie da sirkanta tana rike da hannuta dayan kuma Baban Munay da Mamanta da Munay.
Ko da suka isa Sokoto basu sha walaha ba suka samu gidan tabbas babban gida ne suna zuwa suka bukaci ganin Alhaji Alkali suka sanar masa da komai.
Yan uwa suka hadu masu kuka nayi masu murna nayi Alhaji Alkali yana rike da hannu jikarsa. Ya kuma yi na'am da auren yace a garin Sokoto za'a daura nan yace a ci gaba da shirin biki.
*WAYE ALHAJI ALKALI*
A Alkali haifafen dan garin Sokoto ne babban alkali ne. Yana da yara biyar Fatima ita ce babban yarsa tana Auren Soja wanda suke kiranta da *(Mrs Umar Soja)* Sai kuma Saeed da ke aiki a Bebeji suna kiransa da *(Ya Saeed Bebeji).* sai Abdol-raheem da ke aiki a jega suna kiransa da *(Ya raheem jega)*. Tukunna *Ahmad* (Baban Candy). Sai auntansu Lubabatu tana aure a kano.
Sun kasance su kaunar junansu. Rana daya aka nimi Ahmad aka rasa ya fita fatauci sun shiga kunci da damuwa tun suna zuba ido har suka hakura. Wannan shine takaitacen tarihinsu.
Duk wani shiri ya kan kama saura kwana biyu biki.
Adeel sun kawo lefe na gani na fada kowa ya gani sai ya yaba.
Alhaji Alkali walima kawai ya yarda ayi shi.
Ranar jumma'a bayan sallah jumma'a dubban mutane suka shaida aure Muh'd (Adeel) Aliyu Yahaya da Khadija(Candy) Ahmad Alkali. Akan sadaki dubu dari haka taro ya watse.
Da yamma Candy tayi walima wanda ya hallaci mutane da dama kuma akayi nasiha mai tsuma zuciya.
Bayan gama walima iyayenta suka mata nasiha suka bi jirgi zuwa Kaduna don a gun Adeel ya gina gidan da zasu zauna. Gida ne mai kyau sosai gwanin burgewa. Su Candy da Auta suka zauna sai da amgwaye suka zo. Nasiha sosai suka musu kafin suka tafi.
Adeel ya taso a hankali yazo kusa da Candy cikin salon kauna ya ce "Amarya ba kya laifi".
Har kwanyanta taji muryan kuma akwai ida tasan muryan amma ta rasa ganewa ga nauyin da take ji bare ta dago ta gansa.
A hankali ya yaye gyalen tare da tallabo habarta ya ce “Khadija dago kiga mijinki".
Cikin sauri ta dago wata zata gani Malam Muh'd ido ta murtsuke ko idonta ke mata gizo. Ja da baya ta fara tana hawaye.
Adeel ya sauka kasa ya saka gwuiwarsa a kasa ya fara bata hakuri yana fada mata irin kaunar da ke mata tun haduwarsu. Sam yaki kulasa jiki ba kwari ya koma dakinsa.
Sannu a hankali Adeel ya soma koya ma Candy soshi har suka shaku sosai. Wanda har sukan iya zama gu daya suka kwana a gado daya.
Zaune suke kamar yanda zuka saba cikin dabara da salo Adeel ya soma shafata yana sarrafata ganin kujera ya kasa musu ya daga ta sai gado a hankali ya soma zame mata kayan jikinta. Ganin haka muka bar dakin da sauri. Amatsayin mu na surkai....lol..
Washe gari Adeel shi ya gyara ko ina ya hada musu abun karyawa kar kuso kuga ta rairaya da kauna a gun Adeel da Candy.
******
*BAYAN SHEKARA HUDU*
Adeel na hango da Candy tana rike da hannu wata yarinya wanda kamanta sak na Adeel, yarinya mai kyau da ita. Sun sauka a kofar wani gidan da akayi rasuwa Candy ta shiga ciki bayan tayi ta'aziya nan ta hango masu halin irin nata a da, gunsu ta nufa ta soma musu nasiha sosai ta ciro kudi mai yawa ta basu ta fito ta tafi gidan su Munay suka je suka gaida Maman Munay da Babanta nan ma Alheri sosai suka musu daga nan suka shiga gidan Hajiya ta gaida ta ta mata alheri suka tafi. A mota Adeel ya ce“My Candy wai yaushe za'ayi ma Khairat kanwa ne ko Kani?".
Ido Candy ta juya ta ce“oh Abban khairat da wuri haka yaushe aka yaye ta".
Murmushi yayi “gaskiya ina ga zan kara kai mi don ina son ganin yara na da yawa dan haka yau ki shiya duk dare sau shida zanna duty".
Ido ta zaro ta marairaice fiska “wayyo Abban khairat ina zan iya shida fa".
Dariya yayi sosai yace“kaga raguwa kawai". Itama dariyan tayi.
*ALHAMDULILAHI*
Nan muka kawo karshen wannan littafi mai suna *ZAMAN MAKOKI* kuskuren da ke ciki Allah ka yafe mana amin.
*TSOKACI*
Wannan labarin ba wai mun yi shi da ni shadantarwa bane ka dai a'a akwai sakon da mukae son mu isar. Kusani yan uwa yanzu mafi yawanci badan Allah ake zuwa *ZAMAN MAKOKI* ba, sai dan su je cin abinci ko su saka zani mai tsada suna gasa ko gasan kawo abinci mai yawa da kyau. Wanda hakan haramun ne ko mai mutum zai yi yayi domin Allah. Dan Allah masu wannan halin kuji tsoron Allah ku dai na kunga yanda ya faru da Candy a wannan labari ya Allah ka bamu ikon gyarawa amin.
*SADAUKARWA*
Wannan littafin sadaukarwa ne gareka ɗan mu abin kaunar mu ɗa ɗaya tilo ga *Ummieluff* wato mai suna *MUH'D* *_(Adeel)_* Allah ya raya mana kai bisa sunnan Annabi mu. Ya Allah ka albarkace shi da sauran ya ramu amin.
*TUKWUICI*
Wannan Littafin tukwuici ne gare ku:
Sanah I .S Matazu
Maryam Alkali(Mamu)
Khadija Ahmad Alkali(Candy Uwa ta gari)
Kausar Luv
Ummu Abdoul
Autar Hajiya
Munay
Futha
Aneesa Abubakar Rimi
Aisha Mazoji
Saeed Bebeji
Abdoul-wahab(Mr Smile)
Abdoul Raheem Jega
Aneesa (Anush)
Ummu Abrar
Aisha Muh'd(Maman Abdoul shakur)
Mrs Umar Soja
Haneefa Usman
Manshat
Afreen
Zee Maman Khady
Khdeey
Maryam garba
Simbielurv
Bintu zaif
Serdieylurv
Nuceeluff
Memie bee
Queen Memie
Zahrah BB
Mesha Luv
Ummi Aisha
Lubee Mai tafsir
Miss Hafsy
Mrs Saif
Rabee'at Sk mash
Fancy (mrs sadiq)
*GAISUWA TA MUSAMMAN*
Ga dukkan online hausa writers.
*GODIYA GA GROUPS*
MAMAN ADNAN HAUSA NOVELS
RASH KARDAM HAUSA NOVELS 1,2,3
DAN DALIN LUBIEE MAI TAFSIR
FENNAT NOVEL
MAMU NOVELS
DUNIYAR LITTAFI
HAUSA NOVELS
DUNIYAR MAKARANTA
KHALEESAT HAIYDAR NOVELS F/B
ANEE NOVELS
DAN DALIN AUTAR HAJIYA
RAI DANGIN GORO
MRS SHAMSUR NOVELS
DA SAURAN WAYANDA BAMU AMBATO BA AMANA AFUWA. KUNA RAMMU KUMA MUNA KAUNAR KU.
WRITERS WORLD ASS
SIMBIELURV NOVELS
*UMMIELUFF*
*RASH KARDAM*
Ku ka sance dani a sabon littafina mai suna *TAR KON KAUNA* yana nan tafe ba da jimawa ba.
0 comments:
Post a Comment