°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(AUGUST 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*30*
_Cikin sauri Kdeey ta fita mai Napep ta tsara ya kai ta gida tun a hanya taji kanta na sara tana zuwa gida tayi ma Umma sannu da gida Umma ta amsa ta ce“ya mai jikin Kdeey ta ce“da sauki". 'Daki tashiga ta ajiye hijab d'inta ta canza riga ta kwanta sai ga hawaye Kdeey tana tsanani tausaya ma Samy halin da take ciki. Jiddah ne tashigi da sallamanta ta gai da Umma tukun ta wuce gun Kdeey tana shiga ta ganta tana hawaye da sauri tayi gunta tana tambayanta“lafiya sister mai ya same ki". Kdeey na ganin Jiddah ta k'ara fashewa da kuka nan ta gyara zama ta ce”yau naje gai da Aunty Samy sis Allah ne ya kare ni yau zargina ya zama gaskiya". Malam da ya dawo yazo wucewa yaji alamar kukan Kdeey sai yayi hanyan d'akin yaji suna batun lesbian ba karamin razana yayi ba. Komawa yayi da baya ya kamo hannu Umma suka zo suka tsaya k'ofar dai-dai lokacin da Kdeey ta fara ba ma Jiddah labarin abun da ya faru ba k'aramin razana sukayi ba Malam ya sauke ajiyan zuciya ya shiga d'akin ya ce "akan boko zaki shiga mumunan hali Allah nagodr maka da ka kare min 'yata daga yau karatu ya kare"._
_Malam falo ya koma Umma da duk jikinta yana rawa don ta razana Malam waya yaciro ya kira Yayansa bai dad'e ba ya d'aga wayar nan suka gaisa Malam ya sanar masa abun da yafaru ya ce“Yaya inaga auren nan za'ayi ba sai ta gama makaranta ba don kar muzo muma mu fad'a halaka". Daga d'aya b'angaren ya ce" gsky kam hakan za'ayi". Malam ya ce" inaga ayi auren nan da sati kawai tunda shi daman ya gama karatunsa ita ce a ke jira duk abunda Allah ya hore ayi ba k'arya". Haka suka tsara komai akan sati mai zuwa za'ayi aure Kdeey da yayanta Sani wanda ya ke aikin Soja ne._
_Samy ko sai da mijinta ya dawo bata ko iya tashi daya tambaye ta mai ya sameta ta ce“ta fad'o ne". Nan ya d'auketa sai gun mai d'auri asai kafan ta kauce ne sai ya gyara._
_Umma shirin biki suke yi ita tafi k'arfi a gyara 'Yarta yanzu bata fita ko Aunty Aisha ma ba'a barta a baya ba gurin gyara Kdeey sosai ta sha gyara. Kdeey bata gayyaci kawa ko d'aya ba sai Jiddah ta._
_BAYAN KWANA SHIDA..._
_Yau take jumma'a yau bayan sallah Azahar a masallacin gwallaga duban mutane suka shaida aure Kdeey da Sani. Daga nan aka d'auki amarya sai Kano a can aka shirya musu walima mai lafiya kowa sai fatan zaman lafiya ake ma Amarya da Ango. Ranan Monday 'yan Bauchi suka dawo aka bar amarya a gidanta._
_Tun da suka dawo aka soma shirin bikin Jiddah da Al'ameen su Umma ba zama 'yar aminiya zatayi aure abun dai sai fatan alkairi._
```Rash Kardam```
0 comments:
Post a Comment