New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE 55-58

[30/7/08:11pm]

🎋SADEEY S ADAM🎋
                 &
🌲RASH KARDAM🌲
            WITH
💖BEEBAH LUV💖

   🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
      MA'YAUDARAH
      🌺🌺🌺🌺🌺🌺

          55~58

Bikin Hameedah da Areef ya kankama dan an Gama shirya komai lkci kawai ake jira...
           Areef kuwa hankalinsa a tashe yake duk da dai yayi biyayya amma har yanxu baya jin ko k'wayar son hameedah a ransa.

        ****************

Teemah harka ta k'ara kankama karuwanci ba Kama hannun yaro,ta k'ara goge Wa a fagen yaudara..
ta zama hajjaju, yanxu gani take tafi k'arfin duk Wanda baya da 'ya'yan banki(kud'i)
     Idan 'yan mutuncinta sun motsa takan ziyarci futha kuma duk lkcin da taje Sai taji kishi kuma tayi sha'awar dama itace futha
             amma idan ta hango zaman guri d'aya kullun Sai taji auren ya gundireta...

     Ji take bazata iya zaman guri d'aya ba saboda ta Saba samari na d'aukar suje guraren shak'atawa kala2,dan hka gidansu ma bata fiya zamansa ba.

       Yau ma kamar kullun ta Gama shirinta tsaf Tana jiran azo a d'auke ta su tafi yawon shashancin
           Ummanta ce taxo ta zauna kusa da ita tace "inaso ki nutsu muyi mgna"
          "Ina jinki"ta fad'a ba tare da ta kalleta ba dan kuwa tasan da wacce taxo.
       "Fatima inaso ki nutsu ki gane cewa ita duniyar nan ba Aljanna bace,ya kamata ki gane kuma ki dawo hayyacinki"
tad'an yatsina fuska tace "umma wai me kuma akace na yi?su fa mutane basa son ganin cigaban mutum sunfi son kullun su ganshi cikin bak'in ciki"
          "cigaban wace Mace ce kamarki xa'ace har yanxu bata da ko tsayayyen mijin Aure?tirr da irin wannan cigaban wlh wannan ci bayane"

"Amma umma..........ki rufamin baki fatima"
      Ta dakatar da ita sannan taci gaba da fad'in "yau kusan wata 3 dayin bikin k'awarki amma ko a jikinki,duk sa'oinki sunyi Aure wasu ma harda 'ya'yansu amma ke na rasa abinda ke damunki,shin Ina kike xuwa kullun dan kinga na zuba miki ido ko?to wlh kiyi a hankali duk wannan tarin samarin ace kin rasa Wanda zaki fidda a ciki?karki Manta idan an ciza......dole a hura..ki bi duniya a hankali dai"

"Umma sanin kanki ne nima inason in ganni a d'akin mijina to ai komai yanada lkcin umma lkcina ne har yanxu Allah bai kawo ba"

"Allah ya kawo mana ke dai kikai watsi da damarki sbda 'ya'yan masu hunnu da shuni sun hure miki ido,ki dai bi a sannu Kar kixo ki rasa mijin Aure kinsan dai hak'orin dariya shi ke cizon yatsa"

Duk da dai ta ji haushin kalaman umman tata amma Sai ta daure tayi dariya tace "Umma karki damu kinsan guga inta dad'e a ruwa tafi d'ebo da yawa,na tabbata akwai Wani tanadi da ubangiji yamin Wanda Sai kunsha mamaki kedai Kisha kurumin ki"
(mudai cewa mukai a hakan😧)

"Allah ya tabbatar da alkhairi"
        "Amin umma hka nake so ki tayani da addu'a"
    "Inayi ai kullun cikin yi muku nake"

Haka suka b'arke da hira har xuwa lkcin tafiyar Teemah sannan tayi Wa umma sallama ta tafi.

             Written by
              🎋S💖B🌲R

[Truncated by whatsapp].

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts