°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*5*
A hankali ta d'ago dai-dai lokacin Malam ya zauna daga d'ayan kujerun da ke falon, Umma cikin sanyin jiki ta bud'e laidan kayan kwaliya ne dana shafe-shafe a shak'e a ciki sai d'ayan kuma ice cream ne da su chocolate dun ta tara mata. Umma ta ce"Kdeey gaskiya ya kamata ki rage karb'an kayan Samira ko dai ke kike rok'onta?". Nan take idon Kdeey yayi rau-rau alamar zatayi hawaye ciiin sanyin murya ta ce"Umma wallahi ni ban tab'a rok'onta ba kuma in ta ban nakan k'i karb'a ma, amma sai ta nuna fishi sosai ta ce min ba'a mayar da kyauta da kalamai masu jujja zata min wanda dole sai na karb'a". Umma ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce"an gode ki mata godiya amma ki kula kina kiyayewa da k'awayen banza ki kama mutuncinki ki sani mutunci da kimar mace shine *MARTABANTA* ma tsawan kika kare marta banki to ki sani shi zai k'ara saya miki daraja da kima agun masoyanki, sannan a duk inda kika samu kanki banda zama da k'awayen banza kina yawaita addu'a tsari da shaid'an a duk inda kike Allah zai kareki". Tana dasa aya Malam yayi gyaran murya ya ce"Khadija duk kala man da Mahaifiyarki ta fad'a gaskiya ne kusan kulum sai mun nana ta miki nima hakan zan k'ara fad'a miki, sannan ki kasance mai jin tsoron *Allah* a duk inda kike duk abunda zakiyi kiyishi domin *Allah* banda riya, duk abunda zakiyi ki duba ya tsun hannu mu ba dai-dai suke ba wani yafi wani".
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment