New Post

Monday, 20 February 2017

HANNUNKA MI SANDA PAGE 6

HANNUNKA MAI SANDA............

Rash A Kardam

Sanah S Matazu

6
Tun bayan da Halima ta dawo gida kannenta sun rainata sam basa girmamata ga zagi da hantaran da suke mata.Kamar kullum yauma zaune take cikin ?aki ta yi jigum tare da zabga tagumi tana tunani zuciyarta k'war cike da alhini da nadaman zuwanta gidansu. Tunanin kuncin da take fuskanta take yi,ko banza in gidantane tana yin abinda taga dama. Gashi in ta ce zata fa?a ma Baffansu shima wani fa?an zai yi mata ajiyar zuciya ta sauke,
"tabbas danasani k'e yace, sai a yanzu nasan na TAFKA BABBAN KUSKURE na matsa wa mijina ya sakeni".
A fili ta furta tare da share ?an guntun hawayen da ya zubo mata a kuncinta.
Bammm!! Karar bu?e kofar, ya dira a kunnuwanta ta ?aga kai Hafiz ne ya nufo ?akin yana huci tamkar zakanya. Tafiya yake tamkar matashin ?auna da ke ji da kansa, kalo ?aya zakayi wa damatsansa kasan yana ji da samarta ka ga karfi tamkar giwa duk damatsansa a mur?e suke yana da faffa?an kirji kuma yana da kyau. Cikin huci ya iso tsakiyar ?akin yana aika mata da mugun kalo. Take taji 'ya'yan hanjin cikinta suna niman agaji. Safa-da-marwa ya farayi a gabanta yana aika mata da harara. Cikin ?acin rai ya nuna ta da yatsa.
"Kee! Halima kar ki kuskura ki kara ta?a min kayana ina ajiye, in kina yi wa wanan mijin naki rashin kunya ni bazaki min na ?auka ba".
Hannusa ya ?aga ya nuna kirjinsa da ?an yatsansa ya ce,
"ina mai jan miki kunne ki kiyaye sabgata in ba haka ba kinsan sauran".
Ya karashe maganar tare da ka?a yatsunsa biyu sukayi kara, kafin ya ka?a kansa ya fita yana fankama.�
"Hmm!".
Ta sauke a jiyar zuciya, kamar anjehota ta shigo.Ta kalli tulin kayan da Halima ta jibga mata a cikin kayanta masu kyau.
"Mtssw lalle ma Aunty Haliman nan ta raina min hankali da sauri ta ?ago ta dubeta cikin fishi ta ce,
"dani kike?".
"Eh! Din dake ake meyasa haka Aunty Halima zaki ?auki tsatstsaman kayanki ki ?ora min akan nawa gaskiya ni ba zan lamunci wannan halinba. In kinsaba rashin ?a'a wa mijinki to bazaki zo gida ki hana mu sake b ki takura mana ba".
Kallon mamaki tabita dashi cikin kunar rai ta mike,ta zabgamata mari tana ?aukewa ta rama karaf akan idon Murjanatu data kawo mata ziyar bazata.
Aikuwa ta yi kukan kura ta afko ?akin,nan da nan fa?a ya sarke tsakaninta da Salima da gudu mahaifiyarta ta shigo ta rabasu dukkansu huci suke Halima na gefe kuka kawai take tare da shadshekar nadama.
Cikin kaushin murya ta dubesu,

"duk ku zauna".

Ba musu suka bi umarninta,tayi musu kallon ?ai-?ai ta sauke idonta kan Halima sukai kallon kuda ta yi saurin ?auke idonta.
"Menene ya ha?aku?".

Cikin kunar zuci Halima ta yi mata bayanin komai.Ta saki ajiyar zuciya cikin hikima ta yi musu nasiha tare da nunawa kowace kuskuranta.Murjanatu ta ce,
"Mama tare muke da Abbanmu yana son ganin Baffa".
Wani sanyin da?ine ya kwaranya a zuciyarta,ji take tamkar ta daskare dan sanyi.
Ta bu?e baki zata yi magana sallamar mahaifinta da mijinta ya katse mata hanzari, da sauri Sahiem ya nufi mahaifinsa yana ?angala dariya ya shafa kansa duk ya fa?a iya kwanaki uku kacal.
Zama suka yi bayan an gaggaisa mahaifinta ya yi gyaran murya yana dubanta.
"Halimatu duk naji abinda ya faru a bakin ?iyarki da maigidanki,baki kyauta ba kin bani mamaki akan layya kika yi sanadin ?alewar igiyar auranki wannan abin kunya ne".
Cikin kuka ta dinga bawa mahaifinta hakuri, nasiha ya yi mata sossai daganan suka yi sallama suna fitowa Hafiz na shigo da wani kossashen rago ganinsu yasa ya yi turus ya ce,
"Baffa badai maidata zaku yi ba, ai rago na siyo kar muma ta gujeman

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts