MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
9
Aysha tana da nitsuwa ga hankali, bata da k'awaye daya, bata cika son hayaniya ba, k'awarta d'ayace, "Karima yar makw'abtan su, tana da hankali ga kok'ari itama. Sh'iya yasa k'awance yazo d'aya. Duk ranar girki Amina. "Aysha keyi musu girki.in girki su "Safiya ne sam abinci ba ka'i, sukanyi harda na mugunta, sab'ani su Aysha"da sukeyi mai k'yau ga dad'i.
"Safiya kulum sai taje yaw'onta da dad'dare zata dawo musu da kayan mak'ula'she su ci, sai sun ga dama suke cin abinci gidan.Su Safiya"kulum sai sun'yi g'ori ma su Aysha, mai bak'in jini ta gada a gun uwarta, kar'ana sa musu ido, nan gani nan bari d'um'amen mayya. Sam bai damunsu daman sun saba shiyasa hidimar gabansu suke yi.
CI GABAN LABARI
Safiya zaune take gaban mir'o, tana kwaliya nuna ma sa'a don jiran sau'rayinta za'izo, yau zasu fita, sosai tayi ky'au dogon riga tasaka bak'i da ratsin golden ba karamin ky'au tayiba, ga fiskan ta sha mai har yana ja-ja. ta fesa turare Black Bond sai k'amsh'i take zubawa, ta zauna zaman jira iso'warsa.
Idris mai Car wash, gaye ne na karshe gun ky'au ba laifi, yana da ky'au abu d'aya ya masa cikas shine kud'i.
Tun yamma ya wanke motar Bala da ya kawo masa wanki, yace"ka bari a gunka zan tafi zari'a gobe in'na dawo zan'zo in k'arba. Da murna ya amshi key din don yau zasu fita da Sofy. Aiki yayi ya kirga kud'i yaga 5k ne lallausar mur'mush'i ya saki, don ya san kud'i zai ish'esa in ya had'a dana gd.
Yana barin gun aiki kasuwa ya nufa, ya say'o sabuwar rigansa na 1k, yana dawo'wa gd ya gogeta da sabuwar jeans dina black colour, sai dare yayi wankansa ya fesa turaren sa Professional da Askiya kamsh'in suka had'u sai ka dage ka gane wane irin turare yasa.
Motarsa ya ja sai k'ofar gidan su Sofy. Wayanta ya kira tace "gani fit'owa My luv, Ba ta dad'e ba ta fito. Sai wani ya'uki takeyi, ganin motar daya ke ciki k'arshe ne. Wani lallausan mur'mush'i ta saki tana sh'iga motar ya tayar suka bar unguwan, Malam Muhammad da ke gefe ta kaici ya ish'esa"wai yata ce zata na wan'an halin, tamkar bani na ha'ifeta ba", Ya Allah ka shirya min ita, ka musu Albarka.( kira gareku iya'ye duk halin da kuka ga yaranku, ku na r'oka musu sh'iriya, a gun Allah, sh'iyake sh'iryarwa, Ya Allah ka sh'iryar damu baki d'aya Ameen). Tunda suka fita, basu suka daw'o ba sai 10:00pm parker motar yayi, cikin salon ya'udara ya rik'o han'nuta my Swt Hrt yace "yanzu sai ya'ushe?. Safiya "kai ta rausaya, sai na jika. All rights!!. Zaki jini a waya ok!! Tace, han'nuta yak'ara rik'ewa, ta kashe masa ido. Da ky'ar ya barta, tashiga gida.(Kira gareku Yan'mata duk dad'in ki da sa'urayi karki bari ya fara rik'e han'nuki daga nan zai soma zarcewa, kin bash'i k'ofar da zai samu damar taba jikinki daga nan kuma shai'dan zai ingiza ku ga fadawa halaka, ayi hattara Yan'mata).lai'dan da yayi mata sayayya ta da'uka ta masa bye-bye ta nufi gida. Dakin kwan'su ta nufa kasan'cewar yau Malam na dakin maman ta ne, ganin Aysha na bacci da gan-gan ta take k'afarta don ta tash'i ta bata haush'i, sanin halin Safiya yasa bata kulata ba. Safiya "ta karaci habaicinta ganin Aysha bata amsa mata ba. Ta dau ledar mamanta taje kai mata. Kafin ta fita tace"saura b'era ya min sata. Aysha "ko kalon inda kayan yake batayi ba, ta sake kw'anciyarta.
......Na......
Rash Kardam
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 9
MOTAR KWADAYI PAGE 9
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment