🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧
_Rash Kardam_
_Ummieluff_
*_page➖141-150._
Wani irin kuka Candy take yi mai tsuma zuciya tana jijjiga Umma. Likitoci ne suka shigo suka rike ta tana fisgewa tana kiran Ummanta. Suka fita da ita waje tana wani irin kuka mai tsuma zuciya ɗauke da tausayi a ciki. Dai-dai lokacin sai ga Baban Munay yazo duba su da Mamanta sun iso suka taras da rasuwan Ummin Candy jikinsu yayi sanyi. Maman Munay har ta fara kuka ita ta rike Candy Baban Munay yasa su a keke Napep suka dawo gida. Shikuma ya samo mota da wasu bayin Allah suka dawo da gawanta gida. Rayuwa kenan dukkan wani rai sai ya ɗan-ɗani mutuwa.
A haka aka shirya Umma nan a kazo za'afita dan mata Sallah akaita gidanta na gasky.
Candy na ganin haka ta kurma kara tana bori tana ture masu riketa da gudu taje ta rike makaranta tana kuka “Umma pls ki tashi kice wasa kike min kin ga zasu tafi da ke. Banda kowa sai Allah sai ke in kin tafi ya zanyi. Wayyo Umma na mai kaunata ki tashi daga yau zan ji duk abunda zaki ce min. Ko gidan makoki ma na bar zuwa ki yarda dani Umma sauko mu tafi ɗaki".
Duk wanda ke gun sai da ya zubar da hawaye don Candy abun a tausaya mata ne bata da kowa yanzu sai Allah. Baban Munay yayi karfin halin janyeta daga makaran tana turjewa aka shiga da ita ɗakin su.
Maman Munay ta ce“Khadija kiyi hakuri kin san abunda kike haramun ne ba kyau. Yin kuka kana kururuwa ga mamaci kina da sanin ki mai yasa kike haka? Ayanzu Umma addu'a ki tafi bukata ba kuka ba. Ki sani duk kaunan da kike mata Allah da ya karɓeta yafi ki sonta ki yi hakuri addu'a zaki mata". Nasiha sosai ta mata mai ratsa zuciya.
A hankali Candy ta bar kukan sai sauke zuciya take tana hawayen.
Bayan an kai Umma makwancinta na gsky. Gida ya cika fam da yan gaisuwa.
Da yamma aka kawo abbincin sadaka kala-kala Candy bata taɓa jin ta tsani cin abincin gidan mutuwa ba sai yau. Tana zaune ta hango fiskokin da bazata manta da su ba. Wato *Ummu Abrar da Futha da Pherty* suka shigo bayan sunyi gaisuwa suka nimi tabarma suka zauna. Basu daɗe da zuwa ba Candy na halkance da su taga sunyi gun kuloli nan suka buɗe suka fara duba abinci har suka zo kan wanda ya musu suka cika plate.
Take zuciyar Candy ya soma suya a rasuwan Mahaifiyarta wasu suka zo cin shinkafan gidam rasuwa. Asai daman haka ake jin idan aka maka rasuwa kaga wasu ba dan Allah suka zo ba? Bata idar da tunani ba taji shewar su da sauri ta ɗago kai wasu ta gani suna tsaye da su *Pherty,* *Futha* da *Ummu Abrar* sunci kwaliya kamar masu zuwa paty, sun daɗe suna hira kafin wayanda suka shigo kafin suma suka je suka ɗau plate suka ɗibi abincin suka nimi gu suka zauna.
Candy ɗaki ta koma ta barke da sabon kuka lalle yau taji ɗacin da ake ji in an maka wannan abun tabbas sai yau take dana sanin zuwanta *GIDAN MAKOKI* da take yi yau taga ilar abun da ciwonsa.
Washe gari bayan sun karya ta na zaune Maman Munay ta liko ta ce“Candy wasu na waje zasu miki ta'aziyya ki same su a zaure".
Jiki ba kwari Candy ta mike ta fito daga gefe ta ga wani ya haɗa kunu da kosai ga ɗan wake a plate duk shi ɗaya ta wuce shi ta fita. Wasu Malamansu na boko ne suka mata gaisuwa tare da nasiha sosai. Kafin suka mata sallama suka tafi ta mike zata shiga gida kenan taji wannan bawan Allah wanda ya ɗibo kunun nan ya ce“Alhamdulilah kai tun da nake zuwa *ZAMAN MAKOKI* Ban taɓa koshi irin na yau ba, aoohh!". Yayi gyatsa yana murmushi.
Sam bai ma lura da Candy ba. Laida sa ya zaro daga aljuhu yafara juye kosan yana cewa “kai amma Allah yasa wata ta kara mutuwa a wannan gidan wani sati don na sake dawowa na sha koko da kosai da kayan tea, da ɗan wake haka nake so gsky *ZAMAN MAKOKI* irin na wannan gidan a kwai daɗi......".
Kasa karasa magar yayi sakamakon ganin Candy tana hawaye a gabansa. Cikin ɓacin rai ta fisge ledar zuciyarta na mata wani irin suya.
Cikin kunar rai ta ce" amma tirrr! Da halinka wannan halin ba mai kyau bane anya kana tuna zaka mutu anya kana tsoron Allah kuwa? Baka tunani kai ma akwai randa zaka mutu a maka haka? Shin iyalanka zasu ji daɗin in sunga hakan?".
Hawaye ta share “kaicona ni Candy kasani da bani da abunyi da ya wuce bin gidan mutuwa don nayi *ZAMAN MAKOKI* don kawai naci abincin mutuwa na koshi. Ni har gidan Christer ina zuwa. Ban taɓa tunani ya zasuji zafin abun, kunci ko ɗacin abun, sai jiya da aka fara min na gani tabbas nayi nadama da dana sani. Sai gashi kai har kana kara min addu'a a gidan asake mutuwa".
Wasu zafafan hawaye ta sake sharewa ta ci gaba da cewa.
"Yau nayi nadama gami da danasani kuma nayi alkawarin canza ɗabi'una. Bawan Allah kaji tsoron Allah ka tuba ka dai na don in baka gyara ba wataran zakayi danasani kamar yanda nake yi yanzu". Bata jira amsan sa ba ta sa kai ta shiga gida.
Bawan Allah nan jikinsa duk yayi sanyi yana mai-maita kalaman ta ya fita a zauren. Tare da yin alkawarin daga yau ya bar wannan halin.
A haka har akayi sadakan bakwai aka watse Candy duk ta dawo shiru-shiru da ita bata son yawan hayaniya sosai ko cikin sa'aninta in ta zauna ita kaɗai sai dai kaji tana azukar ko ta ɗauko al-qur'ani tana karatu. Rayuwa kenan Candy ta dawo kamar ba ita ba ta bar zuwa ko ina. Duk ta rame kulum tana cikin tunani, in ta tuna abunda tayi a gidansu Mr Smile sai ta zubar da hawaye gashi itama an mata. Ta naso ta kirasa ta basa hakuri tarasa yanda zata yi.
*BAYAN KWANA BIYU....*
Candy sai da ta nimi gidansu *Ummu Abrar da Futha da Pherty* taje ta musu nasiha kan zuwa *ZAMAN MAKOKI* wanda sai da suka zubar da hawaye. Suka mata alkawarin sun dai na zuwa. Tun ga ranar suka fara mutunci suna kawo mata ziyara.
Haka rayuwan Candy ya kasance ita kaɗai a gida. Maman Munay tayi-tayi ta koma gidansu taki kasancewar makwabta suke hakan yasa kulum suna tare da Munay.
******
Adeel duk yana cikin damuwa yana zaune a Madina ne amma hankalinsa na 9ja gun Candy Kulum bai da hiran da ya wuce na Candy duk wanda yasan shi to zai san labarin Candy. Hakan yasa Umman sa tana murna tilon ɗanta ɗaya ya samu macen aure hakan yasa tun bata bata ga Candy ba taji tana sonta.
*BAYAN WATA BIYAR...*
Muh'd(Adeel) ne kwance akan gadonsa. Idonsa na kallon P.O.P dakin yana sana'arsa na tunanin Candy. Sam ya kasa tsinana komai bai da aiki sai tunanin Candy, wayar sa ne yayi kara har ya tsinke bai ɗauka ba.
“mtssw ni fa bana son hayaniya shiyasa na ma cire layin da aka sanni na saka sabo".
Wayar ne ta sake kara kamar ba zai ɗauka ba sai ya ɗaga number 9ja ya gani da sunan Ahmad akan wayar. A hankali ya ɗaga wayar.
“Assalamu'alaikum".
“Wa'alaikumusalam Adeel ina ka shiga ne kwana biyu ina ne man wayarka?".
“Hmmm!!". Ya sauke gwaron numfashi.
“Ahmad ban son hayaniya ne tun da na bar 9ja na rasa Candy na rasa farin ciki na shiya banson hayaniya". Muh'd (Adeel) ya faɗa.
“Muh'd(Adeel) haba ya kake abu kaman bana miji ba? Ko da yaushe ka kasance mai amsan kaddara da hakuri. Kuma in har *Rabo ya rantse* to ba makawa sai ka auri Candy. Ko kamanta *Matar Mutum Kabarinsa* wani baya taɓa auren matar wani. Na kai ina ta niman number ka don in sanar maka da Candy ta rabu da Abdoul wahab".
Cikin razana mai ɗauke da farin ciki Adeel ya ce.
“what?!! Mai kake son faɗa min ne? Kana nufin cewar yanzu Candy basa tare da Abdoul?".
Ahmad ya ci gaba da cewa “eh sun daɗe da rabuwa ga mahaifiyarta Allah ya mata rasuwa".
“Innalilahi wa inna ilaihi raji'un". Abunda Adeel yake nana tawa kenan.
“Adeel a yanzu Candy bata da kowa sai Allah kuma yanzu ne ya kamata ka zo ka bayyana kanka in da halima ayi muku aure da ita. Don tana bukatar tai mako gaggawa". Ahmad ya faɗa.
“Allah ya jikanta ya mata rahma. Ahmad satin nan zamu zo ni da Ummie na da Abbah na ayi mai yiwuwa".
“good haka za'ayi sai najika". Cewan Ahmad.
“ok to nagode bye".
Adeel da sauri ya tashi ya nufi falo nan ya samu Ummie da Abbansa ba tare da ɓata lokaci ba yasanarsu komai.
Abba ya nisa ya ce.
“dole mu fara shiri satin nan zamu 9ja in Allah ya yarda ai *YAYA DA DUKOYA BA'A KETARSU* koda ba sonta kake ba abun a tai maka mata ne. Zamu iya kokarin mu ganin an samo fangin iyayenta".
Da farin ciki Adeel ya bar falon ya fara shiri zuwa 9ja gun abar kaunarsa.
A satin su Abba suka gama shirya komai don yau Alhamis jirginsu ya daga zuwa 9ja. Ko da suka sauka a mai duguri garin su Abban Adeel. Nan aka zo aka ɗaukesu bayan sun huta suka ci abinci. Nan Abban Adeel ya sanar ma danginsa akan gobe zasu Kaduna aha ka kowa ya watse.
Washe gari suka bi jirgi sai garin Kaduna. Ko da suka isa gidansu kanin baban Adeel suka sauka. Abban Adeel ya sanar musu komai basu dau lokaci ba suka je gun Baban munay. Abban Adeel suka sanar masa da komai. Yayi farin ciki ya ce.
“Yanzu ni ba zance komai ba in har yarinya ta amince ba matsala ni zan tsaya mata har ayi aure amatsayin mahaifinta".
Godiya sukayi nan Abban Munay ya shiga gida ya kira Candy. Ko da ta zo nasiha ya mata sannan ya ce.
“Khadija wani bawan Allah ne yazo yana sonki sunansa Adeel suna da zama a Madina. Adeel ya dade yana sonki amma ya kasa gaya miki. Har lokacin da yaji kinyi saurayi ya bar kasan sabida ke. Sai daga baya yasamu labarin komai har da rasuwan Ummanki dalilin da yasa yazo kenan". Ya karashe maganan ya na kallon fiskan Candy.
“Khadija ina shawarta ki da kiyi amfani da damanki don wannan masoyi ne na gaskiya kuma kiyi kokari ki bi umar nin Ummanki tace tanaso kiyi aure".
Candy tana kuka tace“Abba na amince tunda na san bazaka taɓa zaba min abunda zai cutar dani ba".
“Allah ya miki albarka".
Ya mike ya sanar musu da ta amince ba matsala. Na suka tsayar da maganan aure nan da sati biyu. Kuma sun dau nayin komai zasuyi sannan suna son ta dawo gidansu Munay gaba daya da zama. Don za'a gyara gidan tunda mallakinta ne.
Godiya Abban munay yayi sukayi sallama suka tafi.
Adeel bai taba zuwa gun Candy ba itama bata damu da tasan kowa ye mijinta ba.
Bayan kwana biyu za'a fara aikin gidan hakan saya tasoma tattaro kayanta zata dawo gidansu Munay. Wata akwati ta dauko a kasan gadonsu duk tayi kura da tsatsa. Da har ta barta, kawai sai taji tana son ta ga miye a cikin a kwatin tayi ta balla kwadon ta kasa. Sai da ta samo tabarya ta rinka dukan akwatin ya balle. Da sauri ta buge wani takarda ta gani da rubutu duk jirwayen ruwa ya bata. Tana kara dago wasu photo ta gani na Ummanta da wanda take tsammanin shine mahai finta. Takardan tasoma warewa ta fara karanta shi kamar haka.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
0 comments:
Post a Comment