°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
_(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
*(JULY 2016)*
*NA*
*®Rashida .A. Kardam*
*N. W. A*
Page
*9*
_Kdeey tayi murmushi ta amsa da "amin Umma na", tafito ta tafi Abba duk abinda sukayi yana jinsu kuma ya k'ara gode ma Allah da ya bashi Umma a matsayin mata sannan ya azurtashi da 'Ya ta gari,(gareki Uwa kinga dai abunda ya faru da Umma da 'Yarta ke kina haka ma Yaranki? Har Yaran susan akwai ranar da wani abu na alkairi da kike musu in baki musu ba su shiga damuwa iyaye dan Allah mu dage kusani 'YA'AYA amana ne agun mu wallahi Allah sai ya tambaye mu akansu Allah ya taya mu tarbiya ya shiryar da Yaran mu amin)._
_gidan su Hauwa Jiddah Jibrin wanda suke kiranta da(JJ)ta shiga da sallama ta gaida mamanta nan Jiddah ta fito suka kama hanyan makaranta, suna tafiya Kdeey ta ce" kawata nikam inaso sanarki wani abun da ya damen", Jiddah ta ce"ina jinki Kdeey", Kdeey ta nisa ta ce"nikam al'amarin Aunty Samy yana d'aure min kai kinga ranan rungumana fa tayi ni ina mata zargin kaman tana aikata lesbian (mad'igo)". Sannan ta fad'a mata abunda ya faru jiya Jiddah ta nisa ta ce"a kwai littafin dana k'aranta na alamomin masu mad'igo(lesbian) ka mar haka; Yana da da cikin alamar mad'igo Mace ko k'awan da zata dinga bayyana miki tsaraicinta. Kada ki yarda k'awarki ta yabaki ta fuskar sha'awa. Ki guji k'awar da zata dinga rungume ki da nufin wasa. Ki tsoraci k'awar da zata dinga kunna miki fina-finan 'yan mad'ugo (Lesbian). Kada ki yarda k'awarki ta tama hannunki na tsawon lokaci don idan ta jima tana shafa miki hannu , da sannu zata zai ga mabudin sha'awa shine ta fara shafa miki k'irjinki. Ki nisanci k'awar fa zata dinga yawan shafa gashin kanki. Ki k'auracewa k'awar da za ta dinga yawan kwanciya ajikinki batare da wani dalili ba. Ki kyamaci k'awar da a ko da yaushe zata dinga son ta dinga ganin jikin ki , kamar k'irjin ki da bayan ki zuwa kasan marar ki. Ki rabu da k'awar da za ta dinga yawan yi mi ki kyaututtuka masu tsada ba bisa falili ba"._
*DEDICATED TO*
*_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*
_Rash Kardam💕_
0 comments:
Post a Comment