🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*31~35*
Candy ganin ran Umma ya b'aci sosai gashi bata son abunda zai b'ata mata rai rusunawa tayi ta ce“Ummana dan Allah kiyi hak'uri bazan sake ba Ummana karkiyi fishi dani kinga bani da kowa sai Allah sai ke kinji Ummana".
Umma duk jikinta yayi sanyi Candy ta gama kashe mata jiki a hankali ta furta “zo nan Khadija kece ai amma in kikabar neman tsokana to zamu zauna lafiya da ke".
Candy ta ce“Umma zan bari in dai zakiyi farin ciki".
Umma ta ce“sosai ma zan so ganin hakan Allah ya miki Albarka". Candy ta amsa da ”amin".
Bayan kwana biyu ana zaman lafiya da Candy talle in ta d'auka ma Umma take ta kan zaga da ikon Allah ya k'are ta dawo gida ko gidansu Autar Hajiya bata zuwa yanzu bata shiga harkan kowa.
BAYAN KWANA BIYU...
Candy kamar abun kirki har Umma tana murna d'iyarta ta nutsu komai cikin girma take yi da nutsuwa.
Yau ta dawo daga talla ta hango Aneesa cikin sauri ta zaga ta bayanta ta ajiye tallan tukun ta shak'o ta, sai da talasa Aneesa tukun ta mak'ureta ta ce“in kika fad'a a gida ko wa Maman ki sai na fasa wannan bakin". Sake ta tayi ta d'au tallanta tayi gaba. Tun daga nesa ta hango motan gawa an wuce da shi zuwa makabarta a gur-guje ta sayar da sabulun ta ce“Umma barin je gidan su Munay bata jin dad'i zan gai data".
Umma tace“to karki dad'e kice ina gai data Allah ya sauwaka". Candy ta amsa da “Amin".
Tana fita tayi gidan su Munay da Sallama ta shiga ta gaida Maman Munay ta ce“Inna Munay na nan kuwa?".
Maman Munay ta ce“ki duba d'akinta tananan ta na baccin rashin zuciya". Da sauri Candy ta shiga tana zuwa ta d'ana wa Munay duka ta ce“ke tashi yau mun samu gun zuwa zamuje cin shefe(shinkafa)". Da sauri Munay ta tashi ta ce“da gaske ki keyi ne?". Candy ta ce“eh wallahi dazu naga an wuce da motar gawa amma ban san wani gida bane kawai sai mu gan-gara kasan layi in munga gidan sai mu shiga".
*```TAGWAYEN MARUBUTA```*
0 comments:
Post a Comment