New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI PAGE 4

MOTAR KWADAYI

By
Rash Kardam
4

Suna fita ostrich suka nufa, nan suka sha ice cream dinsu, bayan sun danyi hira kafin ya mata sayya sosai a laida, safiya abun nima ya samu don duk lokacin da saurayi zai kashe mata kudi, to saken fiskanta da ban ne, gari suka zaga sai 10:00pm ya ajiyeta a kofar gidansu,hakan ma saida suka danyi hira, kafin ta marairace ta kashe murya tace my mubarak dina, daman akwai wasu yan kudi nakeso kaban zanyi amfani da su, sai da yayi jim kafin ya ciro 10k ya bata, bata waniyi murna sosai ba, sai dan kawai bata da kudi ta bude kofar motar ta fita ko godia babu, tana fita ya girgiza kai safiya kenan ko godia babu kamar ita ta nemo su,(kira gareku mata kisani duk kan kancin kyautar da mijinki zai miki kizama mai yawan godia kina masa adu'ah da fatan alkairi hakan na kara soyayya, bawai sai matar aure ba, harda yan mata kina yawan yima saurayin ki fatan al'kairi, riba biyi ga yin masa adu'ah, gashi kikara saye zuciyarsa ta yanda zaiji sonki sosai, kuma zaiji dadi).

Tana shiga gida, ta ga ummin aysha tafito daga bayi da buta a hannunta, wani kalo mata kafin ta saki shewa hehehe wasu bakin jini ya musu yawa ko mashin shini babu, haka za'a kare acin towo miyar kuka, su da cin mai dadi sai dai suga anayi, "kunu a wani gida", umma ko ta kanta bata bi ba tashiga daki, mamanta ne ta foto tana mata kirari sai ke yar albarka, kin gadoni ga farin jini ga kyau yar halak, sai wani isa take ita a dole tafi kowa kyau da farin jini, suka nufi dakinsu cikin murna.
WAYE MALAM MUHAMMADU, DA IYALANSA?

Malam muhammad Sabo asalin sunan sa kenan, malam haifafen cikin garin kaduna ne unguwar tudun wada layin yan kosai, yataso cikin so da kauna gun iyayensa duk da talakawa ne amma suna iya bakin kokarinsi su kyautata masa.

......Na........

Rash Kardam

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts